Ɓangaren yanzu model
Darasi Ƙa'idojin alaƙa tsakanin jinsi biyu (Na miji da ta mace)
Shari’ar Musulunci ta kula da tsara al’amuran mutane a fagage daban-daban, ciki har da ɓangaren mu’amala tsakanin maza da mata. Allah Ta’ala ya halicci maza da mata da sha’awar juna, kuma sakamakon wannan sha’awar abu ne kyakkyawa kuma halal ne ta hanyar aure. Kuma duk wani abin da ba haka ba, ƙofa ce zuwa ga sharri da fitina, ɗaya daga cikin fitintinu masu tsanani. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ban bari a bayana wata fitinar da ta fi mata illa ga maza ba. (Al-Bukhari 5096, da Muslim 2741).
Lalle mafi hatsarin sakamakon dangantaka tsakanin namiji da mace shi ne zina. Kuma shari’ar Musulunci bata taƙaita kawai da haramta wannan zunubi ba, sai dai, tana kuma gargaɗi da ko kusantarsa kada ayi kuma a nisanci duk wani abu da zai iya kaiwa zuwa gare shi. Allah maɗaukaki yana cewa: {Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfasha ce, kuma tafarkinta ya munana.} [Isra'i: 32]. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “Ido suna yin zina da kallo, kunne da saurare, harshe da magana, hannu da kamawa, ƙafa da tafiya, zuciya da sha’awa, al’aura kuma sai ta tabbatar da haka ko kuma ta ƙarya ta shi”. (Bukhari 6243, Muslim 2657, kuma lafazin nasa ne).
Saboda damuwa da kiyaye duk wata karkata ko kuskure da kan iya haifar da mummunan sakamako, shari'ar Musulunci ta tsara wasu tsare-tsare na mu'amalar maza da mata a cikin yanayi na larura, kamar saye, sayarwa, da sauran mu'amalolin da suka halatta, ko kuma a wani yanayi na larura, kamar macen da take neman magani daga wurin likita namiji a lokacin da mace likita ba ta samu ba. Waɗannan ƙa'idojin sun haɗa da:
Runtsa Idanu
Nisanta shafa ko musafaha
Nisantan dukkanin keɓanta
Akwai wasu ƙa'idojin da ya wajaba mace musulma ta kiyaye su yayin da buƙatuwa ta kaita yin mu'amala da maza
Wajibi ne mace musulma ta yi riƙo da ka'idojin suturar Musulunci, na farko domin biyayya ga umarnin Allah Maɗaukakin Sarki, na biyu kuma ta tilasta wa maza su girmama ta, kada su cutar da ita; ta aiki, zance, ko kallo. Allah Ta’ala ya ce: {Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga ganinsu, kuma su kiyaye farjojinsu, kuma kada su bayyanar da ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su yi lulluɓi a kan ƙirjinsu} [Nur: 31]. Kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: {Ya kai Annabi ka ce wa matanka da ƴaƴanka mata da matan muminai su rufe kansu da tufafinsu. Wancan ne mafi cancantar a gane su, kuma kada a zãlunce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin kai.} [Ahzab: 59].