Darasi na gaba
Ladduban tsarki da na biyan buƙata
Musulunci bai bar wani abunda musulmi zai aikata ba face ya sanya mishi ladduba da kuma ƙa'idoji, daga cikin waɗannan abubuwan kuma akwai biyan buƙata. A cikin wannan darasin zaka san ladduban biyan buƙata da na tsarki, da nau'ukan kari, da kuma yadda za ka tsarkaka daga ko wanne daga cikinsu.