Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Sunnar Annabi (S. A. W)

Addinin musulunci ya kafu ne a bisa tushe manya guda biyu; Su ne Alkur'ani mai girma da kuma Sunnar Annabi tsarkakakka, a cikin wannan darasin zaka san haƙiƙanin sunnar Annabi da matsayinta a cikin musulunci.

  • Sanin falalan sunnar Annabi
  • Sanin matsayin sunnah a musulunci 
  • Jin girman sunnah a cikin shari'a. 

Sunnar Annabi

Sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wahayi ne daga Allah wanda Ya sauƙarwa Annabi Muhammadu (S. A. W), kuma ita da littafin Allah mai girma su ne tushen addinin musulunci da kuma asalinshi, kuma suna lizimtar junansu ne tamkar yadda shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah yake lizimtar shaidawa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, kuma duk wanda baiyi imani da sunnah ba to baiyi imani da Alkur'ani ba.

Ma'anar Sunnah

Sunnar Annabi ita ce: Duk wani abunda aka jingina shi ga Annabi (S. A. W) na daga zance ko aiki ko wani abunda ya tabbatar, ko wasaftashi ta hanyan halitta ko halaye.

Matsayin Sunnar Annabi:

Sunnar Annabi tana da babban matsayi a cikin Musulunci, kuma ababe masu zuwa zasu bayyana darajarta da matsayinta:

1. Lalle Sunnar Annabi ita ce tushen shari'a na biyu

Sunnah ita ce tushen shari'a na biyu bayan Alkur'ani mai girma, an karɓo daga Miƙdam Bin Ma'adi kurbil Kandi, yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: «Ku saurara kuji, lalle an bani littafi da kuma kwatankwacinshi tare da shi, da sannu za a samu wani mutumin da yake koshe a kishingiɗe akan kujerarsa yana cewa: Na umarce ku da ku riƙi Alkur'ani, duk abin da kuka samu a cikinshi na halal to ku halasta shi, kuma duk abin da kuka samu a cikinshi na haram toh ku haramta shi» [Musnad Ahmad: 17174].

2. Lalle Sunnar Annabi wahayi ne daga Allah Maɗaukaki

Sunnar Annabi (S. A. W) wahayi ne daga Allah Maɗaukaki zuwa ga ManzonShi (S. A. W), Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma baya magana a bisa son zuciyarshi, saidai a bisa wahayin da aka sauƙar mishi, mai tsananin karfi ne ya sanar da shi} [Annajmi: 3-5].

3. Lalle Sunnah Bayanin Alkur'ani ne

A cikin sunnar Annabi akwai bayanin Alkur'ani, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma Mun sauƙar maka da ambato domin ka bayyanawa mutane abin da aka sauƙar zuwa gare su domin su kasance masu tuntuntuni}[Alnahal: 44].

Kuma haƙiƙa ayoyin Alkur'ani mai girma sunzo a cikin da yawa daga lammura da dunƙulallun hukunci, sai manzon Allah (S. A. W) ya bayyana su da ayyukanshi, ko da zantar da su a aikace, misalin faɗin Allah Maɗaukaki: {Kuma ku tsayar da sallah, ku kuma bayar da zakkah, kuma ku yiwa Allah da manzo biyayya domin ku samu rahama} [Alnur: 56]. umarnin tsayar da sallah da kuma bayar da zakkah sun zo ne a dunƙule, kuma bayanin hakan da fayyace shi ya zo ne a cikin Sunnah, ta inda aka bayyana lokutan Salloli biyar, da yadda ake yinsu da kuma sauran hukunce-hukuncen su, kamar yadda aka bayyana hukunce-hukuncen zakkah.

Allah Maɗaukaki Ya kiyaye sunnar Annabi

Sunnar Annabi tana daga cikin ambaton da Allah Ya ɗauki nauyin kare shi, Allah Maɗaukaki Yace: Lalle Mu ne Muka sauƙar da ambato kuma lalle Mu ne Masu kare shi} [Alhijir: 9]. saboda haka Ambato kalma ce wacce ta ƙunshi dukkanin abin da Allah Ya sauƙarwa AnnabinShi (S. A. W) na daga Alkur'ani ko Sunnah.

Kuma daga cikin alamun wannan kariyar cewa lalle Allah Mai girma da ɗaukaka ya tanadawa Sunnar Annabi wasu manyan malamai waɗanda sukayi na mijin ƙoƙari domin tara Sunnah da rubuta ta, kuma suka sanya ka'idojin da zasu inganta riwayarta, kuma suka cire ababen da suka shige ta na daga karya da rabkanwa da kuma kuskure, kuma sun kula da hakan matiƙar kula, kuma suka ba ta cikakken kariya, kuma suka tabbatar da ingancin yanayin masu kawo ta da kuma masu rawaito ta.

Saboda haka Allah Ya ɗauki nauyin kare Sunnah ta hanyar waɗannan malaman da masu rawaitowan waɗanda Allah Ya horar da su domin bada kariya ga sunnar AnnabinShi (S. A. W)

Kasancewar Sunnar Annabi Hujja ce

Sunnar Annabi ita ce tushe na biyu na shari'a bayan Alkur'ani mai girma, kuma addinin Allah ba zai taɓa cika ba sai da komawa zuwa ga littafin Allah da kuma Sunnar Annabi kafaɗa da kafaɗa.

Saboda haka Sunnah babban tushe ne wajen samo hukunce-hukuncen shari'a, kuma wajibi ne amfani da ababen da su kazo a cikinta wajen mas'alolin Aƙida da kuma na shari'a.

Kuma Sunnah zata iya zuwa da bayanin hukunce-hukuncen Alkur'ani mai girma, kuma zata iya zuwa tana mai cin gashin kanta da wani hukuncin shari'a, saboda haka sunnah tamkar Alkur'ani take wajen halalta halal, da kuma haramta haram.

Kuma haƙiƙa dalilan Alkur'ani mai girma da kuma na hadisan Annabi sun tabbatar da cewa lalle sunnah hujjah ce, kuma sun tabbatar da matsayinta a cikin shari'ar musulunci, saboda haka ne akwai ayoyi da dama da hadisai da yawa waɗanda suke umarni da riƙe sunnah, da kafa hujja da ita, da kuma wajabcin yiwa Annabi (S. A. W) biyayya, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma duk abunda manzo yazo muku da shi ku riƙe shi, kuma abunda ya haneku daga gare shi ku hanu} [Alhashri: 7].

Daga Miƙdam Bin Ma'adil Yakribil Kandi, lalle Manzon Allah (S. A. W) yace: An kusa a samu wani mutumin da yake ƙoshe a kishingiɗe akan kujerarsa, yana bada labarin wani hadisi daga hadisai na, sai yace: Abin da ke tsakaninmu da ku shi ne littafin Allah Mai girma da ɗaukaka, duk wani abunda muka samu a cikinshi na halal zamu halasta shi, kuma duk wani abunda muka samu a cikinshi na haram zamu haramta shi, to ku saurara kuji, lalle abunda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya haramta tamkar abunda Allah Ya haramta ne» [Ibn Majah: 12].

Bin Sunnah

Allah Ya wajabta bayinShi biyayya ga Annabi (S. A. W) da kuma bin sunnarshi, cikin zantukansa da ayyukansa da kuma yanayinsa. Allah Yace:{Kace idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah Ya so ku, Ya kuma gafarta muku zunubanku, Kuma Allah Mai yawan gafara ne Mai yawan jin ƙai} [Ãli Imran: 31]. Kuma Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma ku bi shi domin ku shiryu}[Al-A'araf: 158].

Kuma an karɓo daga Irbadi Ɗan Sariyata Allah Ya kara mishi yarda, lalle Manzon Allah (S. A. W) yace: «kuma na umarce ku da riƙe sunnata, da sunnar khalifofi shiryayyu masu shiryarwa, kuyi riƙo a gare ta, kuma ku kamata da fiƙoƙinku, kuma na hore ku daga fararrun abubuwa, domin duk wani fararren abu bidi'a ne, kuma kowace bidi'a ɓata ce» [Abu Dawood: 4607].

Saboda haka biyayya ita ce riƙe abunda manzon Allah (S. A. W) ya faɗa ko ya aikata, kuma da tafiya a bisa tafarkin Annabi (S. A. W) da kuma hanyarshi wajen bin umarnin Allah da kuma nisantar ababen da ya hana, da aiwatar da addini tare da aiki da shi.

Biyayya wajibi ne a cikin ababen da suke wajibi kuma mustahabbi ne a cikin ababen da suke mustahabbi.

Falalar bin Sunnah

Bin Sunnah yana da falala da kuma sakamako masu yawa, daga cikinsu:

A cikin bin sunnah da lizimtarta akwai tsira daga bin kungiyoyin da Annabi yayiwa mabiyarta alkawarin wuta, daga Abdullahi Da Amru Allah Ya kara musu yarda yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: «Hakika abunda ya zowa bani Isra'ila zai zowa Al'umma ta, ku riki takalmi da takalmi, koda ace a cikinsu akwai wanda ya zowa uwarsa a bayyane, da za a samu wanda zai aikata hakan a cikin Al-umma ta, kuma lalle bani Isra'ila sun rabu har zuwa kungiyoyi saba'in da biyu, kuma Al-ummata zata rabu har zuwa kungiyoyi saba'in da uku, dukkaninsu suna cikin wuta saidai guda daya», sai sukace: waccece wannan ya manzon Allah? sai yace: Wadanda suka kasance akan abunda nake kai ni da sahabbai na»[Tirmizi: 2641].

A cikin lizimtar sunnah akwai samun aminci da shiriya daga ɓata, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma ku bi shi domin ku kasance shiryayyu} Al-A'araf: 158]. Kuma an karɓo daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: «Lalle ni na bar wasu ababe guda biyu a cikinku ba zaku taɓa ɓata bayansu ba: Littafin Allah da sunna ta» [Mustadrakul Hakim: 391].

Sharaɗin karɓan kyawawan ayyuka sai sun dace da Sunnah, dole ne ayyukan da bawa zai aikata su zamto sun dace da Sunnar Annabi (S. A. W), daga Aisha Allah Ya kara mata yarda lalle Manzon Allah (S. A. W) yace: «Duk wanda ya aikata wani aikin da babu umarnimu a cikinshi to an mayar mishi» [Muslim: 1718].

A cikin bin sunnah akwai kusantar Annabi (S. A. W), a cikin barin Sunnah kuma akwai nisantar Annabi (S. A. W). An karɓo daga Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yarda yace: Mutane guda uku sunzo gidajen matan Annabi (S. A. W), suna tambaya dangane da ibadar Annabi (S. A. W), a yayin da aka basu labari sai suka raina ayyukan da sukeyi, sai sukace: to ya muke da Manzon Allah (S. A. W)? wanda haƙiƙa an gafarta mishi abunda ya gabatar da kuma abunda ya jinkirta! sai ɗaya daga cikinsu yace: Amma ni zan fara yin sallar dare na har abada, ɗayan kuma yace: Ni kuma zan dinga yin azumi kuma bazan ci abinci da rana ba har abada, sai na ƙarshen kuma yace: Ni kuma zan nisanci mata ba zanyi aure ba har abada, sai Manzon Allah (S. A. W) yazo sai yace: Ku ne waɗanda sukace kaza da kaza, amma ni wallahi na fiku tsoron Allah kuma na fi ku taƙawa, saidai ni ina sallah kuma ina bacci, ina azumi kuma ina cin abinci da rana, ina kuma auran mata, saboda haka duk wanda ya bijirewa sunnah ta baya tare da ni» [Bukhari: 5063]

A cikin lizimtar sunnah akwai tsira daga fitintunu da kuma Azaba mai raɗaɗi, Allah Maɗaukaki Yace:{Waɗanda suke saɓawa umarninshi su kiyaye domin fitina zata iya samunsu ko kuma azaba mai raɗaɗi} [Alnur: 63].

Cikin bin sunnah da kuma lizimtarta akwai samun rabauta da rayuwa mai daɗi a cikin Duniya da Lahira, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma duk wanda yayiwa Allah da manzonShi biyayya, kuma ya ji tsoron Allah yayi taƙawa, to, waɗannan su ne masu rabauta} [Alnur: 52].

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa