Ibadah:
Ibadah ita ce: Sakakkiyar biyayya tare da soyayya da girmamawa da ƙasƙantar da kai, kuma haƙƙin Allah ne akan bayinshi, Ya keɓanta da ita shi kaɗai koma bayan waninShi, kuma ibadah ta ƙunshi dukkanin abunda Allah Yakeso Ya kuma yarda dashi na daga zantuka da ayyuka waɗanda Yayi umarni da su kuma Ya kwaɗaitar da mutane zuwa garesu, sawa'an ta kasance daga cikin ayyukan da suke zahiri ne kaman sallah da zakkah da hajji, ko daga cikin ayyukan da suke ɓoye irinsu ambaton Allah da zuciya, da tsoron Allah, da dogara a gare Shi, da neman agajinShi, da wanin haka.