Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Haƙiƙanin Ibadah

Ibadah tanada matsayi mai girma a cikin addinin musulunci. Wannan darasin zai tattauna ma'anarta, da haƙiƙaninta, da rukunnanta, da hikimar da take cikin kasancewarta nau'i daban-daban.

  • Sanin Ma'anar Ibadah Da Haƙiƙaninta. 
  • Sanin Rukunnanta Da Nau'o'inta. 
  • Sanin wani abu daga cikin hikimar kasancewarta nau'i daban-daban. 

Ma'anar Ibadah

Ibadah gamammiyarr suna ce ga dukkanin ababen da Allah Ta'ala Yake so kuma Ya yarda da su na daga zantuka da ayyuka; na bayyane da na ɓoye. Saboda haka, dukkanin ababen da Allah Yakeso na daga ayyuka da zantuka sunanshi Ibadah.

Haƙiƙanin Ibadah

Ibadah ita ce: Sakakkiyar biyayya tare da soyayya da girmamawa da ƙasƙantar da kai, kuma haƙƙin Allah ne akan bayinshi, Ya keɓanta da ita shi kaɗai koma bayan waninShi, kuma ibadah ta ƙunshi dukkanin abunda Allah Yakeso Ya kuma yarda dashi na daga zantuka da ayyuka waɗanda Yayi umarni da su kuma Ya kwaɗaitar da mutane zuwa gare su, sawa'an ta kasance daga cikin ayyukan da suke zahiri ne kaman sallah da zakkah da hajji, ko daga cikin ayyukan da suke ɓoye irinsu ambaton Allah da zuciya, da tsoron Allah, da dogara a gare Shi, da neman agajinShi, da wanin haka.

Daga cikin rahamar Allah akan bayinShi ne ya sanya ibadah ta zamto nau'i daban-daban, daga cikinsu:

١
Ibadun zuciya: Kamar son Allah, da jin tsoronShi, da dogara a gare shi, kuma su ne mafifitan ibadu waɗanda suka fi darajah.
٢
Ibadun gangan jiki: Daga cikinsu akwai waɗanda suka keɓanta da harce, kamar ambaton Allah, da karatun Alkur'ani, da kyakkyawan zance. Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suka keɓanta da wanin harce, kaman alwala, da azumi, da sallah, da kawar da abunda zai cutar daga hanya.
٣
Ibadun Kuɗi: Kaman sadaka, da zakkah, da ciyarwa a hanyoyin alheri.
٤
Daga cikinsu kuma akwai waɗanda suka haɗa waɗannan nau'ukan gaba ɗaya, kaman hajji da umrah.

Hikimar Dake Cikin Kasancewar Ibada Nau'i Daban-daban

Daga cikin hikimar Allah Ta'ala ne Ya sanya ibadah ta kasance nau'i iri-iri daban-daban, domin mutum ya samu nashaɗi a cikin zuciyarshi ya kuma samu damar gudanar da ibadu ba tare da gajiya ko ƙosawa ba, kuma domin mutum ya fiskanci ibadar da ranshi tafi son aikata ta.

Kamar yadda ibadu suka bambanta hakama mutane suka bambanta wajen ababen da suke so da kuma ikon da suke da shi, daga cikinsu akwai wanda zai samu nashaɗi akan wata ibadah fiye da waninta. zakaga wani yana son kyautatawa mutane, wani kuma yafi son yin azumin nafila, wani kuma zuciyar shi tafi son karatun Alkur'ani da haddanshi.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ya kasance daga cikin mutanen sallah za a ƙira shi ta ƙofan sallah (Zuwa shiga Aljannah), Kuma wanda ya kasance daga cikin mutanen jihadi za a ƙira shi ta ƙofar jihadi, wanda kuma ya kasance daga cikin mutanen sadaka, za a ƙira shi ta ƙofar sadaka, kuma duk wanda ya kasance daga cikin mutanen azumi, za a ƙira shi ta ƙofar Arrayyan". Sai Abubakar As-siddik yace: Ya Manzon Allah yanzu babu wanda za a kira shi ta waɗannan ƙofofin gaba ɗaya? sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Akwai kuma ina fatan zaka kasance daga cikinsu» [Bukari: 1897, Muslim: 1027].

Ibadah ta shafi dukkanin ɓangarorin rayuwa

Ibadah ta shafi dukkanin tasarrufin mumini idan har yayi niyan neman kusanci zuwa ga Allah da hakan. A musulunci ibdah bata taƙaita kawai akan ayyukan ibadan da suke sanannu ba, kamar sallah da azumi da makamancinsu, sai dai dukkanin ayyuka masu amfani tare da kyakkyawar niyya da kuma ingantaccen manufa sukan zama ibadan da za a sakawa mutum akansu, da ace musulmi zai ci abinci, ko ya sha ruwa, ko kuma yayi bacci da niyyar samun ƙarfin bauta wa Allah Ta'ala; da za a bashi lada a bisa hakan.

Musulmi yana gudanar da dukkanin rayuwar shi ne saboda Allah, domin idan yaci abinci da niyyar samun ƙarfin biyayya ga Allah, sai cin abincin shi da wannan manufar ya zamto ibadah, kuma zaiyi aure domin ya kame daga barin haram, sai aurenshi ya zamto ibadah, kuma da irin wannan manufar ne kasuwancin shi, da aikinshi da neman kuɗinshi dukkaninsu zasu kasance ibadah, hakama neman ilimi da neman takardan shaida, da bincikenshi, da ƙirƙire-ƙirƙirenshi zasu zamto ibadah, hakama kulawan da mace zata yiwa mijinta da kuma gidanta ibadah ne, hakanan dukkanin ɓangarorin rayuwa da ayyukanta, da lammuranta masu amfani muddin dukkaninsu an gudanar dasu da kyakkyawar niyya da kuma manufa mai kyau.

Ibadah Ita Ce Hikimar Halittan Mutum:

Allah Madaukaki Yace: {Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini * Bã Ni nufin (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni * Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi} [Azzariyat: 56- 58].

Allah Maɗaukaki Ya bada labarin cewa lalle hikimar halittan aljani da mutane ita ce su bautatawa Allah, kuma Allah Maɗaukaki Mawadaci ne daga ibadarsu, sai dai su ne suke buƙatuwa zuwa bauta miShi, domin buƙatun da suke dashi a wurin Allah Maɗaukakin Sarki.

Kuma idan mutum yayi sakaci da wannan manufar ya kuma nitse cikin ababen jin daɗin duniya ba tare da tuna hikimar ubangiji na halittanshi ba; sai ya koma tamkar sauran halittun da basu da wata darajah a cikin wannan duniyar, saboda dabbobi ma suna ci kuma suna wasa, saidai su ba za a musu hisabi a lahira ba, koma bayan mutum, lalle Allah Ta'ala Yace: {Kuma waɗanda suka kafurta suna ci kuma suna jin daɗi tamkar yadda dabbobi suke ci, amma kuma wuta ita ce makomansu} [Muhammad: 2]. domin sunyi kamanceceniya da dabbobi wajen ayyukansu da kuma manufofinsu, saidai su babu shakka zasu samu sakamakonsu a bisa hakan domin lalle su suna da hankali suna fahimta kuma suna riskan abubuwa saɓanin dabbobin da basu da hankali.

Rukunnan Ibada

Ibadar da Allah Yayi umarni da ita tana da rukunnai guda uku masu mahimmanci, kowana ɗaya yana cika ɗan uwanshi

Rukunnan Ibadah

١
Soyayya don Allah Ta'ala
٢
Ƙasƙantar da kai a gare Shi da kuma tsoronShi
٣
TsammaninShi da kuma kyautata miShi zato

Ibadar da Allah Ya farlantawa bayinShi, dole ne a cikinta ya kasance akwai cikakken ƙasƙantar da kai ga Allah da kuma rusuna a gabanShi, tare da cikakkiyar soyayya, ya kuma ya kasance Shi ake nufi da ita tare da kwaɗayi da kuma tsammani a gare Shi.

A bisa wannan, duk wata soyayyar da babu tsoro da ƙanƙan da kai a cikinta - kaman son abinci da dukiya- ba ibadah bace, hakama tsoro ba tare da soyayya ba- kaman tsoron dabba mai farauta, da azzalumin shugaba- wannan ma ba ibadah bane, amma idan tsoro da soyayya da kuma tsammani suka haɗu a cikin aiki anan ne ya zamto ibadah, kuma ibadah bata kasancewa sai ga Allah Shi kaɗai.

Saboda haka, idan musulmi yayi sallah ko yayi azumi sa'annan ya kasance abunda ya saka shi wannan shi ne son Allah da tsammanin ladanShi, da kuma tsoron azabar Shi, to ya kasance a cikin ibadah, amma kuma idan yayi sallah domin kada ace: Baya sallah, ko yayi azumi da manufan kiyaye lafiyarshi; to wannan baya daga cikin ibadah

Allah Maɗaukakin Sarki Yace Yana Mai jinjina ga AnnabawanShi: (Lalle su sun kasance masu tsere ne wajen aikata alheri kuma suna roƙonMu suna masu tsammani kuma masu tsoro, kuma sun kasance a gare Mu masu ƙasƙantar da kai ne) (Al-Anbiya: 90).

Nau'ukan Ibadah:

١
Ibadah Tsantsa
٢
Abunda yake zamtowa ibadah da niyyah

1- Ibadah tsantsa:

Kuma su ne abunda Allah da ManzonShi sukayi umarni da a gudanar da su cikin wani yanayi na musamman, kuma ba zasu iya kasancewa wani abu ba face ibadah, kaman: Sallah da azumi da hajji da addu'a, da ɗawafi, da makamantan su, kuma waɗannan ibadun ba ya halatta a gudanar dasu ga wanin Allah, ko kuma a nemi ladan akansu a wurin wanin Allah.

2- Ababen da suke kasancewa ibada da niyyah:

Daga cikinsu akwai kyawawan halaye waɗanda Allah Yayi umarni dasu ko Ya kwaɗaitar da mutane zuwa gare su, misalin biyayya ga iyaye, da kyautatawa mutane, da taimakon wanda aka zalumta, da waninsu na daga kyawawan ɗabi'u da al'adun da Allah Yayi umarni da su, kuma musulmi zai zamto mai laifi idan ya bar aikata su. kuma a cikin irin waɗannan ibadu ba dole bane bin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi daki-daki, abunda yake wajibi a cikinsu kawai shi ne barin saɓa mishi da kuma kiyaye faɗawa cikin abinda Allah Ya haramta.

Kuma waɗannan ayyukan idan mai aikatasu ya kyautata niyyarsa, kuma yayi niyar isa zuwa biyayyar Allah dasu zai samu lada, amma kuma idan ya aikata su ba tare da neman yardan Allah ba to ba zai samu lada ba amma kuma ba za a rubuta mishi zunubi ba. Daga cikin waɗannan ibadun akwai al'amuran rayuwar mu na yau da kullum, kaman bacci, da aiki, da kasuwanci, da motsa jiki, da makamancinsu. Saboda haka, duk wani aiki mai amfani wanda aka nufi neman yardan Allah da shi mai shi zai samu lada (Lalle Mu Bama lalata sakamakon wanda ya kyautata aiki) (Alkahfi: 30).

An sharɗanta sharruɗa guda biyu domin ingancin ibadah da kuma karɓanta:

١
Tsarkake ibadah ga Allah Shi kaɗai ba tare da abokin tarayya ba.
٢
Ta kasance ta dace da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma kamar yadda yayi.

Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma duk wanda yake burin saduwa da rahamar ubangijin shi, to ya aikata aiki na gari kuma kada ya yiwa Ubangijinshi tarayya da kowa cikin ibadarshi) (Alkahfi: 110).

Sai faɗin Allah Ta'ala: (Kuma kada yayiwa ubangijinshi tarayya da kowa cikin ibadarshi) yayi nuni zuwa ga tsarkake ibadah ga Allah Shi kaɗai ba tare da waninShi ba, kuma faɗinShi: (Aiki na gari) sai yayi nuni zuwa ga bin Sunnah; domin aiki na gari shi ne ingantacce, kuma aiki ba zai kasance ingantacce ba har sai ya dace da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Saboda haka, duk wanda yake burin saduwa da Allah da gidan lahira, toh ya bautawa Allah a bisa waɗannan sharruɗa guda biyun waɗanda aka ambace su a cikin wannan ayar.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa