Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangarorin koyon karatun

Dandalin Taa ya ƙunshi silsilar koyon karatu daban-daban, kuma kowana shashi ya ƙunshi zaɓaɓɓun darrusa daga wurare daban-daban domin hakan ya taimaka wajen gina masaniyar shari'a ga ɗalibi dai dai da buƙatarshi

Ababen da ya wajaba kowana musulmi ya sani

Shari’ar Musulunci ta zo da hukunce-hukuncen da ya wajaba dukkan musulmi su koye su kuma su aiwatar da su. Wadannan hukunce-hukunce kuma masu sauki ne sosai , kasancewar tushen shari’ar Musulunci ya ginu ne a kan kawo fa’ida da kuma nisantar da cutarwa. Bayan haka kuma wadannan hukunce-hukunce sun zamto na daban ne domin daga wurin Allah suke, da kuma kasancewar wanda ya bayyana wa mutane shi ne mafi ilimi, fasaha, kuma wanda yafi kowa iya nasiha ga al’ummarsa wato Annabi Muhammad (S. A. W). Wannan silsilar ta kunshi zababbun darussa da suke samarwa musulmai muhimman hukunce-hukuncen Musulunci wadanda wajibi ne su sansu su kuma yi aiki da su.

39 درس
+35

Sabon Musulmi

Dazaran mutum ya shiga cikin Musulunci, to lalle ya fara wata sabuwar tafiyar wacce ta banbanta da tafiyarshi na baya a cikin wannan duniyar, kuma babu shakka zai bukaci ilimi da fahimta masu yawa a cikin wannan sabuwar tafiya tashi domin ya inganta Akidarshi ya kuma kare ta da su. Kuma ya aiwatar da ababen da Allah Ya farlanta mishi wadanda suke wajibi, domin ya samu daukaka a cikin matakan musulunci da na imani kadan-kadan. kuma hakika a cikin wannan silsilar mun tara mishi dukkanin ababen da zasu kaishi ga cinma wannan manufar da yardan Allah.

38 درس
+34

Mu'amalolin Kuɗaɗe

Musulunci addini ne wanda ya kunshi dukkan bangarorin rayuwa. Addini ne na ibada kuma addinin mu'amala. Muminai suna bukatar shiriya don fahimtar hukunce-hukuncen shari’ar Musulunci a dukkan wadannan bangarorin, ta yadda ayyukansu za su kasance cikin yardar Allah. Alkur'ani mai girma ya kunshi cikakkun bayanai game da mu'amala da kwangiloli, kuma Annabi (S. A. W) ya bayyana wa al'ummarsa hukunce-hukuncen da suke bukata dangane da ciniki da sauran hada-hadar kudi. Za mu yi bayanin wasu daga cikin waɗannan hukunce-hukuncen a wannan bangaren.

درسان

Iyali Musulma

Musulunci ya baiwa iyali lura da cikakkiyar kulawa, kasancewar Shari'a ta ginu ne a kan shiryar da mutane zuwa ga maslahar rayuwa da kuma ta lahira, kuma babu yadda Al'umma zata shiryu sai ta hanyar shiryuwan iyalan da suke fitowa daga cikinta. Saboda haka Sharia ta zo da hukunce-hukunce da tsare-tsare, da kyawawan halaye, da tsari madaidaici wanda yake gina iyali ya kuma kiyaye shi, kuma ta fayyace aikin kowane mutum a cikin iyali, da kuma hakkokinsa.

11 درس
+7

Mace Musulma

Shari’ar Musulunci ta zo ne don girmama mata, kuma akwai misalai da yawa a kan haka a cikin littafin Allah Maɗaukakin Sarki da tarihin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Wani ɓangare na girmamawar Musulunci ga mata shi ne, ya shar’anta musu hukunce-hukuncen da suka yi la’akari da siffofinsu da yanayinsu, da kiyaye haƙƙoƙinsu, da kare su daga fasiƙanci da buri na mugaye da masu zukata marasa lafiya.

6 دروس
+2