Hukunce-hukuncen Tafiya
Musulunci addinin rayuwa ne, saboda haka ne yake da alaƙa da dukkanin yanayin rayuwar mutum, a yayin da yake zaune da lokacin da yayi tafiya, da natsuwarshi, da motsinshi, da gaskiyarshi da wasanshi, kuma tafiye-tafiye wani ɓangare ne na wannan rayuwar, kuma lalle ba zai rabu da wasu hukunce-hukunce waɗanda Allah Ta'ala Yake so daga gare mu da mu sansu mu kuma aikata su, ko kuma wasu ababen da Allah Yake son mu nisance su kuma mu barsu ba. A cikin wannan darasin da yardan Allah zamu duba wasu daga cikin hukunce-hukuncen tafiya.