Ɓangaren yanzu model
Darasi Wasu ababen masu ƙara imani yayin tafiya
Abin da ake nufi da tafiye-tafiye anan shi ne tafiyar da mutum zaiyi domin yawon buɗe ido a wuraren dabi'a da makamantansu.
Kalmar tafiya tazo sau ɗaya a cikin Alkur'ani mai girma, a cikin faɗin Allah: {Saboda sãbon Ƙuraishawa * Sãbonsu na tafiyar hunturu da bazara} (Kuraish: 1-2), Tafiyar hunturu: ita ce tafiyar Ƙuraishawa na kasuwanci a cikin hunturu, kuma sun kasance suna fiskantar Yaman a cikinta, tafiyan bazara kuma sun kasance suna fiskantar Sham a cikinta.
Rayuwan musulmi a koda yaushe yana haɗe ne da Allah da kuma shari'arShi, kuma tafiye-tafiye da balaguro a cike suke da hukunce-hukuncen shari'a waɗanda Allah Ya shar'anta mana su; saboda manya-manyan amfanin da suke cikinsu na duniya da lahira, kuma hakan zai samu ne idan mutum ya kyautata aiki da su.
Mumini zai iya sanya tafiyarshi ta zamto ibadah, ta yadda zaije wuraren da ake gudanar da ibadah a cikinsu, kamar Hajji da Umrah, ko neman ilimi..., kuma zai iya kyautata niyyarshi wajen sadar da zumuncinshi, ko ya farantawa mutanenshi, ko ya yalwata musu da kuma kanshi da abunda yake na halal wanda za ayi amfani da shi wajen biyayya ga Allah ko za a gujewa saɓon Allah da shi.
{Kace lalle sallata, da ibadu na, da rayuwa ta, da mutuwa ta na Allah ne Ubangijin talikai}[Al-An'am: 162]
Duniya a cike take da ayoyin Allah waɗanda suke nuni zuwa ga girmanShi, da rahamarShi da kuma hikimarShi, Allah Ta'ala Yace: (Lalle a cikin halittan sammai da ƙasa, da sassaɓawan dare da yini akwai ayoyi ga masu kaifin hankali) (Ali-Imran: 190). saboda haka Allah Yayi umarni sau da yawa da ayi dubi da idon basira zuwa ga waɗannan ababen, ba wai kawai kallon jin daɗi da sabo ba, Allah Ta'ala Yace:{Shin ba suyi dubi bane cikin mulkin sammai da ƙasa da abunda Allah Ya halitta na daga komai} (Al-A'araf: 185).
Kamar yadda a cikin kaɗaita akwai damar yiwa kai hisabi da kuma duba guzurin da mutum ya gabatarwa gobenshi, musamman idan ya keɓanta da kanshi kuma babu wani wanda yake kallonshi face Allah Maɗaukaki.
Duk wanda ya isa gidan da yayi tafiya zuwa gare ta, koda ya kasance akan tudu ne ko wanin haka, an shar'anta mishi yin addu'ar da tazo a wannan lamarin.
An karɓo daga Khaulatu Ƴar Hakim Allah Ya kara mata yarda tace: Naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: (Duk wanda ya sauƙa a wani masauƙi sai yace: Ina neman tsari da cikakkun kalmomin Allah daga dukkanin abin da ya halitta, babu wani abin da zai cutar da shi har sai ya bar wannan wurin) (Muslim: 2708).