Mutuwa Da Jana'izah
Mutuwa ba shi ne ƙarshen lamari ba sai dai wani sabon mataki ne ga mutum, kuma ita ce farkon cikakkiyar rayuwa a lahira, kuma kaman yadda musulunci ya kwaɗaitar akan kula da haƙƙoka tun daga haihuwa haƙiƙa ya tabbatar da hukunce-hukuncen da za su kare haƙƙokan mamaci kuma zasu kula da yanayin mutanenshi da makusantanshi.