Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Haƙiƙanin Rayuwa Da Kuma Mutuwa

Allah Mai girma da ɗaukaka Ya halicce mu Ya kuma samar damu a cikin wannan duniyar domin ya gwada mu Ya kuma jarraba mu, Kuma lamarim mutum baya ƙarewa da mutuwa, saidai matakin jarabawan ne yake ƙarewa, domin matakin lahira na farko ya fara, a wurinda mutane zasu samu sakamakon ayyukansu. A cikin wannan darasin zaka san wani abu daga cikin haƙiƙanin rayuwa da kuma mutuwa.

  • Sanin haƙiƙanin rayuwa da mutuwa. 
  • Sanin hukunce-hukunce da kuma ladduban da suke da alaƙa da mamaci

Haƙiƙanin rayuwa da mutuwa

Mutuwa ba ita ce ƙarshen lamari ba sai dai wani sabon mataki ne ga mutum, kuma ita ce farkon cikakkiyar rayuwa a lahira, kuma kaman yadda musulunci ya kwaɗaitar akan kula da haƙƙoka tun daga haihuwa haƙiƙa ya tabbatar da hukunce-hukuncen da za su kare haƙƙokan mamaci kuma zasu kula da yanayin mutanenshi da makusantanshi.

Allah Mai girma da ɗaukaka Ya halicce mu Ya kuma samar damu a cikin wannan duniyar domin Ya gwada mu Ya kuma jarraba mu, kaman yadda Allah Maɗaukaki Yace: (Wanda Ya halicci rayuwa da mutuwa domin Ya gwada ku waye daga cikinku zai fi kyautata aiki) (Al-Mulku: 2), duk wanda yayi imani ya kuma ji tsoron Allah zai shiga Aljannah, kuma duk wanda ya zaɓi ɓata da karkacewa zai shiga wuta.

Kuma rayuwar mutum a cikin wannan duniyar duk yadda tayi tsawo sai ta ƙare ta kuma gushe, kuma wanzuwa da tabbata na har abada a lahira yake, Kaman yadda Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma lalle lahira ita ce asalin rayuwa da ace sun kasance sun sani) (Al-Ankabutu: 64).

Kuma haƙiƙa Allah Ya gayawa Mafificin halittanshi - Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa lalle zai mutu tamkar yadda mutane suke mutuwa, sa'annan kuma dukkanin mutane zasu taru a wurin Allah domin Yayi hukunci a tsakaninau, (Lalle zaka mutu kuma lalle su ma matattu ne) (30) Sa'annan kuma lalle ku a ranar Alkiyama a wurin ubangijinku zakuyi ta husuma) (Azzumar: 30, 31).

Kuma haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kwatanta mana yanayinshi - da kuma yanayin kowana mutum - game da duniya da gajartanta idan aka kwatanta ta da lahira da yanayin matafiyi wanda ya zauna ya ɗan huta a ƙarƙashin inuwar wata bishiya sa'annan sai ya tafi ya barta. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (Me ruwa na da duniya, Misali na a wannan duniyar shi ne kaman misalin matafiyin da ya zauna yana hutawa a inuwar wata bishiya sa'annan ya tafi ya barta". (Attirmizi: 2377, Ibnu Majah: 4109).

Kamar yadda Allah Ya labarta mana wasiyyar Annabi Yakubu alaihis salam ga ƴaƴanshi a yayin da yace: (Lalle Allah Ya zaɓa muku Addini, saboda haka kada ku kuskura ku mutu face kuna musulmai) (Albakara: 132).

Kuma idan mutum ya kasance bai san yaushe ne ajalinshi wanda Allah Ya ƙaddara mishi zaiyi ba, kuma baisan a ina hakan zai kasance ba, kuma babu wani wanda ya isa ya canza mishi, to duk mai hankali ya wajaba a gare shi da ya cika lokutanshi da ayyukan alheri da nagarta da kuma Addini, domin lalle shi kaman yadda Allah Ta'ala Yace ne: (Kuma kowace Al-Ummah tanada ajali, Kuma idan ajalinsu yazo to ba za a jinkirta musu na wani lokaci ba kuma ba za a gabatar da su ba) (Al-A'arafi: 34).

Kuma duk wanda ya mutu da fitan ranshi daga gangan jikinshi to haƙiƙa Alƙiyamarshi ta tsaya kuma ya fara sabuwar tafiyarshi a gidan lahira, wacce tana daga cikin sanin gaibun da hankali ba zai taɓa iya sanin yadda take a fayyace ba.

Kuma kaman yadda shari'a ta kula da hukunce-hukuncen mutum tun daga haihuwarshi, da ƙuruciyarshi, da tasowanshi, da samartakanshi, da tsufanshi, to haƙiƙa an shar'anta mana hukunce-hukunce da kuma ladduban da zasu kiyaye haƙƙokan mamaci, su kuma kula da mutanenshi da makusantanshi, saboda haka dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya kammala mana wannan Addinin, Ya kuma cika mana ni'imarShi, kuma Ya shiryar damu zuwa wannan addini mai girman gaske.

Hukunce-hukunce da kuma ladduban da suke da alaƙa da mamaci

1. Yayin da yazo dab da mutuwa

Duk wanda ya ziyarci mara lafiya ya kamata ya roƙa mishi waraka da lafiya ya kuma gaya mishi cewa wannan rashin lafiyan kankare zunubi ne da kuma yafe kura-kurai kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: "Babu damuwa wannan tsarkaka daga zunubi ne da yardan Allah" (Bukhari: 3616).

Kuma ya wajaba a gare shi yayin magana da ya zaɓi laffuza da kalmomin da zasu kwantarwa mara lafiyan hankali domin ya samu ƙarfin gwiwan jurewa cutar ya kuma tsammaci waraka, ya kuma yi amfani da lokutan da suka dace da roƙon Alkah, ya kuma tunatar da mamacin Allah da ranar ƙarshe cikin hikima da wa'azi mai kyau, kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya buga mafi kyawun misali a bisa hakan, An karɓo daga Anas Allah Ya kara mishi yarda yace: Wani yaro bayahude ya kasance yana yiwa Annabi hidima, sai yayi rashin lafiya, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yaje duba shi, sai ya zauna a dab da kanshi sai yace dashi: «Ka musulunta» sai yayi dubi zuwa ga babanshi wanda ya kasance yana tare da shi, sai babanshin yace mishi: Kayiwa Baban Ƙasim biyayya- Wato Annabi- sai ya musulunta, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fito yana cewa: «Na godewa Allah Wanda Ya kuɓutar da shi daga wuta» (Bukhari: 1356).

2. Laƙƙanawa wanda ya kusa mutuwa Kalmar shahada

Idan alamum mutuwa suka bayyana akan mara lafiya, anaso a dinga laƙƙƙana mishi kalmar shahada kuma ana kwaɗaitar dashi akan faɗinta (La ilaha illal lahu) domin ita ce mabuɗin Aljannah, cikin hikima ta kuma hanyar da ta dace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ku laƙƙanawa mamatanku kalmar La ilaha illal lahu" (Muslim: 916).

Kuma ita ce mafi girman abunda mutum zai faɗa a cikin rayuwarshi da kuma yayin mutuwarshi, kuma duk wanda ya dace ta zamto ita ce kalmarshi ta ƙarshe to haƙiƙa ya samu darajah mai girman gaske, kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ƙarshen maganarsa ta kasance la ilaha illal lahu ya shiga Aljannah" (Abu Dawood: 3116).

3. Fiskantar da wanda ya kusa mutuwa zuwa ga Alkiblah

Anaso a fiskantar da wanda ya kusa mutuwa zuwa ga Alkiblah saboda faɗin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Masallacin Harami Alkiblarku ce kuna raye da kuma kuna mace" (Abu Dawood: 2875), sai a kwantar da shi a gefenshi na dama a kuma fiskantar da shi zuwa ga Alkiblah kamar yadda aka kwantar da mutum a cikin kabari.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa