Ɓangaren yanzu model
Darasi Ta'aziya da Iddah ga mamaci
Ta'aziya
Anaso a yiwa mutanen gidan mamaci ta'aziya kuma a gaishar da makusantanshi, da kuma ƙarfafa su akan abunda ya same su da duk wani zance mai kyau wanda a cikinshi akwai Addu'a ga mamacin da tabbatar da danginshi da kuma basu haƙuri, da tunatar dasu cewa su nemi lada a wurin Allah, kuma haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gayawa ƴarshi Zainab yayin da yake mata ta'aziyan rasuwan ɗanta: «Lalle abunda Allah Ya bayar naShi ne abunda ya karɓa ma naShi ne, kuma kowana abu yana da lokaci sananne a wurinshi, saboda haka kiyi haƙuri ki kuma nemi lada daga gurin Allah» (Bukhari: 1284, Muslim: 923).
Za a iya yiwa makusantan mamaci ta'aziyah kafin binne shi da kuma bayan binne shi, a kowana waje, sawa'an ya kasance a cikin masallaci ne ko a cikin Maƙabarta ko a gida, ko a wurin aiki, ko wanin haka.
Bai kamata ayi shishshigi wajen gabatar da ta'aziya ba ta yadda za a kafa rumfuna, ko gudanar da walima, da kuma tara jama'a domin ita, domin babu shakka wannan baya daga cikin sunnar Amnabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbanshi masu darajah, sa'annan kuma ba wani abu ne na murna da farin ciki ba bare ayi mishi irin waɗannan ababen.
Bakin ciki akan mamaci da yi mishi Iddah
Kuka rahama ce wacce aka saba da ita, kuma wata hanya ce na nuna damuwa da rashin da akayi, kuma haƙiƙa idanun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun zubar da hawaye yayin rasuwar ɗanshi Ibrahim (Bukhari 1303, Muslim 2315).
Musulunci ya sanya wa nuna baƙin ciki a bisa mamaci ka'idoji masu yawa:
Tsawon Lokacin iddar wanda mijinta ya rasu
Shi ne watanni huɗu da kwanaki goma, ko kuma zuwa ta haihu idan ta kasance mai juna biyu ce.
Menene ya wajaba akan mace yayin iddan rasuwan mijinta?
Ziyaran Maƙabarta: Ziyaran Maƙabarta ya kasu zuwa kashi uku:
1. Ziyaran da ake so (Mustahabbi)
Ita ce Ziyarar Maƙabarta domin tunawa da mutuwa da kabari da kuma gidan lahira, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Na kasance na hanaku ziyaran Maƙabarta to ku ziyarce ta" a cikin wata riwaya kuma "Domin lalle ita zata tunatar daku da lahira" (Muslim: 977, Attirmizi: 1054). Abun nufi anan shi ne ziyaran kabarin da suke garin maziyarcin, ba wai sai anyi tafiiya ko kuma sai an niƙi gari ba, wanda kuma ba ayin hakan saidai zuwa masallatai guda uku.
2. Ziyarar da ta halalta
Ita ce ziyarah domin wata manufar da take halal ba don tuna mutuwa ba, kuma a cikin ziyarar babu wani abu dake haram, kaman mutum ya ziyarci kabarin wani ɗan uwanshi ko abokinshi, amma kuma a niyyarshi babu tunawa da gidan lahira.
3. Ziyarar da ta haramta
Ita ce ziyarar da a cikin ta akwai wasu ababe na saɓon Allah; Kaman zama akan kabari, da tafiya akanshi, da duke-duke, da kururuwa, da ɗaga murya da kuka, ko kuma akwai wasu bidi'o'i a cikinta, kaman neman kusanci zuwa ma'abocin kabarin, ko neman albarkah da kabarin ko shafanshi, ko wasu ayyukan shirka; kaman neman biyan buƙata a wajen ma'abocin kabarin.
Saboda haka ziyaran musulmi zuwa Maƙabarta ya kamata ta kasance tana da manufofi daban-daban.
Ya kamata a yayin ziyaran kabari a lura da rashin zama ko tafiya akan kabari domin girmama mamacin da kuma karrama shi, saboda hakane Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana uƙubar hakan, sai yace: "Da ɗayanku zai zauna akan garwashin wuta sai ta ƙona tufafinshi ta isa har zuwa fatarshi, yafi mishi alheri da ya zauna akan kabari" (Muslim: 971).
Addu'a a Maƙabarta
Daga cikin Addu'o'in da suka zo yayin ziyaran Maƙabarta faɗin: «Amincin Allah ya tabbata a gare ku mutanen gidan muminai, kuma mu ma da yardan Allah zamu riske ku» (Muslim: 249). ko «Amincin Allah ya tabbata akan ma'abota wannan gidajen na daga muminai da musulmai, kuma Allah Ya gafartawa waɗanda suka gabata daga cikinmu da kuma waɗanda suka saura, kuma mu ma da yardan Allah zamu riske ku» (Muslim: 974). ko (Amincin Allah ya tabbata a gare ku mutanen wannan gidan na daga muminai da musulmai, kuma mu ma da yardan Allah zamu riske ku, ina roƙa mana lafiya tare da ku gaba ɗaya» (Muslim: 975).