Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Wankan Gawa Da Saka Mishi Likkafani

Musulunci ya karrama mutum bayan mutuwanshi kaman yadda ya karrama shi yayin da yake raye, A cikin wannan darasin zaka koya wasu ababen da suke da alaƙa da wanke gawa da suturta shi.

  • Sanin ababen da akeso a aikata su bayan rasuwan musulmi.
  • Sanin siffar wankan gawa
  • Sanin wasu daga cikin hukunce-hukuncen sakawa gawa likkafani.

Abunda akeso a aikata yayin da musulmi ya mutu

Idan mutuwa ta tabbata kuma rai ya rabu da gangan jiki, anaso a aikata ababe da yawa, daga cikinsu

1. Rufe idon mamaci cikin tausayawa da karramawa

A yayin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shiga kan Abu Salamah kuma haƙiƙa idanunshi suna buɗe sai ya rufe mishi ya kuma ce: "Idan kuka shiga kan mamatanku to ku rufe musu idanuwansu" (Ibnu Majah: 1455).

2. Haƙuri da mallakan rai

Da rashin ɗaga murya da kuka da kuma ife-ife, da baiwa mutanen mamacin da makusantanshi haƙuri, kuma lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya umarci ɗaya daga cikin ƴaƴanshi yayin da ɗanta ya rasu da tayi haƙuri ta nemi lada a wurin Allah (Bukhari: 1284, Muslim: 923).

3. Roƙa mishi rahama da gafara, mutanenshi kuma a roƙa musu haƙuri da miƙa wuya ga hukuncin Allah

Kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aikata tare da Abu Salamah -Kuma shi yana daga cikin manyan sahabbai - yayin da ya mutu, sai yace: "lalle shi rai idan aka zare shi to idanuwa suna binshi" sa'annan sai yace: Ya Allah Ka gafartawa Abu Salamah Ka kuma ɗaga darajarshi a cikin mutane managarta, kuma Ka maye gurbin shi cikin abunda ya bari, kuma Ka gafarta mana da shi ya Ubangijin talikai, kuma Ka yalwata mishi kabarinshi, Ka kuma haskaka mishi a cikinshi" (Muslim: 920).

4. Gaggauta shirya mamaci da wanke shi da yi mishi sallah da binne shi.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ku gaggauta gawa zuwa makoncinta, idan ta kasance ta gari ce, to kuna gabatar da ita zuwa ga alheri ne, idan kuma koma bayan hakane, to sharri ne kuke ɗauke dashi akan kafaɗunku" (Bukhari: 1315, Muslim: 944).

5. Taimakawa mutanen mamaci

Da taimakonsu wajen gudanar da wasu uzurinsu, kuma lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi umarni da a dafawa mutanen ɗan baffanshi Ja'afar Binu Abi Ɗalib Abinci yayin da aka kashe Ja'afar Allah Ya kara mishi yarda, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ku dafawa mutanen Ja'afar abinci domin lalle abunda zai shagaltar dasu yazo musu" (Abu Dawood: 3132, Attirmizi: 998, kuma Ibnu Majah ya inganta shi 1610).

Wanke mamaci

Wajibi ne a wanke mamaci gabanin a saka mishi likkafani a kuma binne shi, kuma wani daga cikin mutanenshi ko makusantanshi ne zai wanke shi ko kuma waninsu daga cikin musulmai, domin lalle an wanke Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bayan ya rasu kuma shi ne tsarkakakke mai tsarkakewa.

Yadda ake wanke mamaci

A yayin wanke gawa za a jiƙa dukkanin jikinshi da ruwa, kuma za a kawar da najasa idan har akwai ta, tare da kula da suturta Al'auranshi yayin wankan. Kuma anaso a kula da ababe masu zuwa:

1. A suturta Al'auranshi wato abunda ke tsakanin cibiyarshi da gwiwanshi, bayan tuɓe mishi kayanshi.

2. Mai wanke gawa zai sanya safar hannu a hannayenshi, yayin da yake wanke Al'auran mamacin.

3. Zai fara ne da kawar da najasa da ƙazanta daga gawar idan har akwai su.

4. Sa'annan sai ya wanke gaɓoɓin alwala a bisa tsarin da aka saba.

5. Sa'annan sai ya wanke kai da sauran gangan jiki, kuma an so ya wanke shi da ganyen magarya ko sabulu, daga nan kuma sai ya kwara mishi ruwa.

6. Anso da ya fara wanke gefenshi na dama sa'annan na hagu.

7. Kuma anso a maimaita wankewa har sau uku ko fiye da haka idan akwai buƙatar hakan.

Kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gayawa matan da suka kasance suna wanke ƴarshi Zainab Allah Ya kara mata yarda: "Ku wanke ta sau uku ko sau biyar ko fiye da haka idan kunga akwai buƙatan hakan" (Bukhari: 1253, Muslim: 939).

8. Za a iya saka wani ƙelle ko Auduga ko wani abu makamancinsu

A dubura, da gaba, da kunnuwa biyu, da hanci da baki; domin kada wata najasa ko jini ya fito daga gare su.

9. Anaso a fesawa mamaci turare

Yayin wanke shi da bayan wanke shi, domin lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi umarni ga matan da suka kasance suna wanke ƴarshi Zainab da su sanya Kafur a cikin ruwan wanke ta na ƙarshe (Kafur wani nau'i ne na turare)(Bukhari: 1253, Muslim: 939).

Waye zai wanke mamaci?

١
Idan har mamaci ya bar wasaiyyan wanda zai wanke shi sai a zantar da wasiyyarshi.
٢
Maza da Mata waɗanda suke ƙasa da shekaru bakwai, ya halatta Maza ko Mata su wanke su, amma abunda yafi shi ne Maza su wanke yara maza Mata kuma su wanke yara mata.
٣
Idan kuma mamacin ya kasance yafi shekaru bakwai, to idan na miji ne maza ne zasu wanke shi idan kuma ta mace ce mata ne zasu wanke ta.
٤
Ya halatta ga mutum ya wanke matarsa kuma ya halatta ga mace da ta wanke mijinta, Kuma lalle Aliyu Bin Abi Ɗalib shi ya wanke Faɗimah Allah Ya kara musu yarda.

Kuma Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: «Da ace na fiskanta lamari na kaman abunda na juyawa baya da babu wanda zai wanke Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi face matanshi» (Abu Dawood: 3141, Ibnu Majah: 1464).

Sanyawa Mamaci likkafani

Sanyawa mamaci likkafanin da zai suturta shi yana daga cikin haƙƙokanshi waɗanda suke wajbi akan mutanenshi da kuma musulmai, kuma hakan farilla ce wanda wani yakan ɗaukewa wani, domin faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "Ku sanya daga cikin tufafinku farare saboda fari na daga cikin mafificin kayanku, kuma ku sanya mamatanku ma a ciki" (Abu Dawood: 3878).

Kuma ana ɗaukan kuɗaɗen da za ayi sungullan suturta mamaci ne daga abubda ya bari idan ya kasance mai dukiya ne, idan kuma ya kasance bai bar wani abu na daga dukiya ba, to sungullan tufatar dashi ya wajaba akan waɗanda kulawa da shi ya zamto wajibi a gare su yayin da yake raye, kaman babanshi, da kakanshi, da ɗanshi, da jikanshi, idan kuma ya kasance dukkansu basu da hali, to nauyin ya koma kan mawadata daga cikin musulmai.

Abunda yake wajibi na likkafani ga mamaci shi ne abunda zai suturta mishi jikinshi na daga tsarkakakken tufafi, mamacin ya kasance na miji ne ko ta mace.

Kuma anaso yayin sanyawa mamaci tufafi

١
A saka na miji a cikin tufafi guda uku farare kaman yadda aka yiwa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, mace kuma anso a saka ta a cikin tufafi guda biyar domin ƙara suturta ta.
٢
Anso launin likafanin ya zamto fari idan hakan ya samu, kuma lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "ku sanya daga cikin kayakinku farare, domin suna daga cikin mafifitan kayanku kuma ku sanya mamatanku ma a cikinsu" (Abu Dawood: 4061, Attirmizi: 994 Kuma Ibnu Majah ya inganta shi: 3566).
٣
Anso a sanyawa tufafin likafanin turare mai kyau na halal.
٤
Ya kamata a mai da hankali wajen sanya wa mamaci likafani ta yadda zai rufe dukkanin kanshi da ƙafanshi, kuma lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Idan ɗayanku zai sanya wa ɗan uwanshi likafani to ya kyautata shi" (Muslim: 943).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa