Ɓangaren yanzu model
Darasi Sallah A Bisa Mamaci Da Kuma Binne Shi
Sallan jana'iza tana wajaba ne akan dukkanin musulmai waɗanda suke nan ba wai akan kowana ɗaya daga cikinsu ba, domin ita farali ne na kifaya ta yadda idan wasunsu suka sallace shi to sallar ta faɗi akan waɗanda basu samu sun sallace shi ba, kuma lalle Manzon Allah ya yiwa wanda ya sallaci gawa albishir da lada mai girman gaske, yace: "Duk wanda ya halarci sallar gawa har aka mata sallah ya kasance yana da lada kimanin Ƙiraɗi, kuma wanda ya halarce ta har aka binneta yana da lada kimanin Ƙiraɗi biyu». sai akace menene Ƙiraɗi kuma? sai yace:? Misalin manya-manyan duwatsu guda biyu» (Bukhari: 1325, Muslim: 945).
Falalan halartan Jana'iza
1. Anaso a gudanar da sallar jana'iza a cikin jama'a kuma liman zai gabata akan mamu tamkar yadda ake yin sallar jama'a.
2. Za a sanya gawar a tsakanin masu sallah da Alkiblah, kuma liman zai tsaya a daidai kanshi, Mace kuma a tsakiyanta, kaman yadda yazo daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi (Abu Dawood: 3194).
-
Kabbara ta farko
Kabbara ta biyu
Kabbara ta uku
Kabbara ta huɗu
Ya halalta ayi sallar jana'iza a cikin masallaci ko a wani wuri na musamman wanda aka tanada domin hakan a wajen masallaci kuma akan iya yi ma a cikin Maƙabarta, domin hakan duka sunzo daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sunnah ita ce gaggawa wajen kintsa mamaci, da sallatanshi, da tafiya da shi zuwa Maƙabarta, da kuma binne shi. Daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Kuyi gaggawa da gawa zuwa makoncinta, idan ta kasance ta gari ce to kuna gabatar da ita zuwa ga alheri ne, idan kuma ta kasance koma bayan haka ne to sharri ne kuke ɗauke da shi akan kafaɗunku». (Bukhari: 1315, Muslim: 944).
Ababen da ya kamata a lura dasu yayin binne mamaci
Anaso waɗanda suka halarci binne mamaci da su roƙawa mamacin tabbata da gafara bayan an binne shi, domin haƙiƙa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan aka kammala binne mamaci sai ya tsaya akanshi yana mai cewa: "Ku naimawa ɗan uwanku gafara kuma ku roƙa mishi tabbata, domin yanzu haka ana tambayanshi" (Abu Dawood: 3221).