Ɓangaren yanzu model
Darasi Tafiye-tafiye da tsarki
A yayin tafiya ababe da yawa daga cikin ababen da mutum yake samu suna canzawa, hakama yadda yake samun ababe a kusa da shi. Daga Abu Huraira Allah Ya kara mishi yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (Tafiya wani yanki ne na azaba, zai hana ɗayanku abincinshi da abin shanshi da kuma baccinshi, saboda haka idan mutum ya gama buƙatanshi to ya koma zuwa ga iyalanshi), Bukhari: 1804,3001,5429), (Muslim: 1927). Saboda haka, ya kamata ga wanda yayi tafiya da ya san ababe da dama waɗanda suke da alaƙa da Tsarki da waninshi, daga cikin haka:
An haramta biyan buƙata a wurin da mutane suke zirga-zirga hakama zuba ƙazanta a wurin, na daga inuwa ko bishiya, ko wani wurin da aka gyare shi domin zama da makamancin haka.
Kuma malamai sun bayyana cewa idan mutum ya so biyan buƙatanshi a sahara ko wani wuri makamancinshi, An so ya samu wuri mai laushi; domin kada fitsari ya lalata wurin kuma domin kada fitsarin ya feshe shi, saboda haka ya nisanci bushashshiyar kasa, hakama hanyan da iska take busowa.
2. Suturtuwa yayin biyan buƙatar
Kuma a cikin hadisin Abdullahi Ɗan Ja'afar yana ambatan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Kuma mafi soyuwan abin da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake suturta da shi domin biyan buƙatanshi shi ne wuri mai tudu ko tarin ganyen dabino" (Muslim: 342). Kuma ya zo a cikin wani hadisi "Ya kasance idan ya buƙaci biyan buƙata baya ɗaga tufafinshi har sai yayi kusa da ƙasa" (Abu Dawood: 14), domin abin da ke cikin haka na suturtuwa.
Taimama wani nau'i ne na tsarkaka domin gudanar da sallah yayin rashin samun ruwa, ko rashin ikon amfani da shi, kuma siffarta shi ne kaman haka: Mutum zai daki Ƙasa da hannayenshi biyu sai ya shafi fuskarshi da su, sa'annan sai ya shafi bayan tafin hannunshi na dama da hagunshi, ya kuma shafi bayan tafin hannunshi na hagu da damanshi.
Shafa akan Huffi: Shi ne mutum ya kasance yana sanye da huffi (sawu ciki na fata wanda yake rufe diga-digai) ko safa ko wani abu makamancinsu na daga ababen da suke rufe dukkanin diga-digai a bisa cikakken tsarki na daga babban kari da ƙaramin kari, to idan yayi alwala ya shafa kanshi, to baya wajaba akanshi da ya cire huffinshi domin ya wanke ƙafafunshi sai dai zai shafa kansu ne daga samansu.