Ɓangaren yanzu model
Darasi Gamammun Hukunce-hukuncen da suke yawaita yayin tafiya
Ya kamata gabanin bacci: A kashe wutan da ake yawan kunnawa yayin tafiyan hunturu; musamman a cikin tantuna da makamantansu.
Asalin farauta halal ne, amma kuma bai kamata shagaltuwa da farauta ya kasance sababin alaƙantuwar zuciya da shi ba da kuma sakaci da ayyukan addini da na iyali, kuma kada ya kasance sababin almubazzaranci da wargi da kuma alfahari, ya zo a cikin hadisi cewa: (Duk wanda ya zauna a daji zuciyarshi zata ƙeƙeshe, duk wanda yake farauta kuma zai shagala) (Abu Dawood: 2859).
Asali shi ne halatta farautan dukkanin dabbobi da cinsu sai dai waɗanda dalilin shari'a ya hanasu, misali duk wani dabba mai fiƙa na daga dabbobi masu farauta kaman kuraye da dila, da duk wani mai dogon baki daga cikin tsuntsaye kaman Mikiya, da kuma dabbobi masu guba kaman Macizai da wasunsu.
Farautan dabbobin kan tudu da na cikin ruwa duka ya halalta a cikin kowana lokacin shekara; Ba a bambance tsakanin ranar jumma'a ko watan ramadan a cikin haka ko kuma watanni masu alfarma da wanin haka, amma kuma an hana farauta a cikin haramin Makkah ko na Madinah, haka kuma an haramta farautan dabobin da suka kasance mallakan wasu ne, kuma an haramtawa wanda yake sanye da ihrami farautan dabbobin kan tudu.
An sharɗanta cewa mai farautan ya kasance musulmi ne, kuma yayi bismillah, kuma yayi farautan da taimakon karnuka ko tsuntsaye horarru akan farauta, idan tsuntsu ya fire don kanshi ko kuma harsashi ya tafi ba tare da saninshi ba; to cin naman farautan baya halatta sai dai idan ya riske shi gabanin mutuwarshi sai yayi bismillah ya yanka shi.
Kaman yadda aka sharɗanta mutuwan dabbar farauta ya kasance sakamakon raunin da ya mata ne, ba wai ya shaƙeta ko ya natsar da ita a ruwa, ko ya dake ta, ko ya jefo da ita daga tudu ba. Kuma idan ya riski abun farauta yana cikin cikakken rayuwa to zai mishi yanka irin ta shari'a.
An haramta kashe abun farauta domin wasa da wargi kaman wanda zai farauci wata dabba ba don ya ci ta ba, haka ma idan ya kasance akwai tsoratar da mutane da makamin farautan, kaman yadda ya haramta da ya ɗaure tsuntsu domin horar da shi akan farauta.
Haramun ne nuna mutane da tsinin tokobi koda ace da wasa ne; ya zo a cikin hadisi cewa: (Kada ɗayanku yayi nuni zuwa ga ɗan uwanshi da tokobi. Domin ɗayanku bai san cewa ko Shaiɗan zai ƙwace shi daga hannunshi sai ya jefa shi a cikin ramin wuta ba) (Bukhari: 7072, Muslim: 2617), a cikin wani hadisi kuma: (Duk wanda yayi nuni zuwa ɗan uwanshi da wani ƙarfe mala'iku za su dinga tsine mishi har sai ya sauƙe shi, koda ya kasance ɗan uwanshi ne uwa ɗaya uba ɗaya). (Muslim: 2616).
Ya kamata mai farauta ya san tsare-tsaren farauta da kuma matakan aminci, domin ya kare kanshi da waninshi. Kuma akwai hukunce-hukunce na musamman dangane da yadda ake tsarkakewa (Yankan shari'a ga dabbobi), da yadda ake mu'amala da karnukan farauta, da yanayin mutuwan abun farautan, da wanin haka, sai ya koma wajen masana akan hakan.
Asalin ababen ci halal ne sai dai waɗanda sharia ta hana cin su.
Daga cikin ababen da suke haramun na daga ababen ci da ababen sha
Tsirrai da ababen marmarin da suke cikin daji ko a kasuwanni za su shiga cikin ababe halastattu, amma kuma ya wajaba akan musulmi ya kiyaye cin ababen da za su cutar da shi, ko kuma abin da bai san amincinshi ba.