Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Sallah da Azumi a cikin tafiya

Sallah da Azumi a cikin tafiya suna da hukunce-hukunce na musammam. A cikin wannan darasin zaka san da yawa daga cikin waɗannan hukunce-hukuncen.

Sanin hukunce hukuncen da suke da alaka da sallah da kuma azumi yayin tafiya

Ƙiran Sallah a cikin tafiya

Idan lokacin sallah yayi a wurin shaƙatawar da babu masallaci a kusa da shi, to an shar'anta ɗaga murya da ƙiran sallah ga kowace sallah.

Daga Abdullahi Ɗan Abdurrahman Ɗan Abi Sa'asa'atata cewa lalle Abu Saeed Al-khuduri Allah Ya kara mishi yarda yace da shi: Lalle na ga cewa kana son daji da tumakai, to idan ka kasance a cikin dajinka ko tumakanka idan ka kira sallah to ka ɗaga muryarka da ƙiran sallar; domin lalle: «babu wanda zai ji sautin mai ƙiran sallah mutum ne ko aljani ko wani abu face ya mishi shaida a ranar alkiyama». Abu Saeed yace: na ji hakan ne daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.(Bukhari: 609).

Daga nan ne za a san falalar ƙiran sallah, da kuma cewa lalle bai kamata ga matafiya da suji kunyar yinta ba, ko su guje ta, kuma ya zo a cikin wani hadisin cewa: "Mai ƙiran sallah za a gafarta mishi iya wurin da sautinshi ya kai, kuma duk wani abu ɗanye da bushashshe suna nema mishi gafara" (Ibnu Majah: 724).

Fuskantar Alkiblah

Ya wajaba ga wanda yake cikin tafiya da yayi matiƙar ƙoƙari wajen sanin ɓangaren Alkiblah, kuma abun nufi da alkiblah shi ne yankin Ka'abah idan kuma ya kasance baya ganinta to zai taƙaita da fiskantar ɓangarenta, kuma baya wajaba a gare shi da ya fiskanci ainihin ka'abah, domin hakan zai ba da wahala, kuma bai zo daga wani sahabi ba.

Idan yayi ƙoƙari yayi sallah bayan ya nemi alkiblah to sallarshi ta inganta, koda bayan kammala sallar ya fahimci cewa ba ta ɓangaren alkiblah yayi sallar ba, kuma ba zai sake sallar ba, idan kuma yana tsakiyan sallar ne ya fahimci hakan, to nan take sai ya juya zuwa alkiblan. amma kuma idan baiyi ƙokƙari wajen neman alkiblah ba sai ya gane cewa ba ta alkiblah yayi sallah ba, to zai sake sallar.

Kuma za a iya amfani da na'urorin zamani wajen sanin ɓangaren alkiblah, ko da ingantattun nuni daga rana ko waninta, ko da faɗin wani yardajje daga cikin mutanen garin da makamantansu, ko kuma da wasu bayyanannun alamomin da suke nuna alkiblah.

Falalan sallah a sahara

Kiyaye sallah a cikin tafiya yana daga cikin mafi girman ayyuka, kuma hakan dalili ne a bisa gaskiyan imanin mutum.

Ya zo a cikin hadisi cewa: "Sallah ɗaya a cikin jama'a tana daidai da salloli ashirin da biyar, idan kuma ya sallace ta a cikin sahara sai ya cika ruku'unta da sujjadanta sai ta kai matsayin salloli hamsin" (Abu Dawood: 560).

Kuma hakan zai iya kasancewa ne domin hakan wata alama ce ta kyakkyawar alaƙa da Allah Ta'ala, da kuma tsoronShi; har a yayin da mutum ya kasance nesa da mutane da kuma kallonsu, saboda haka ne yazo a cikin hadisi cewa: "Ubangijinku Yana mamakin mai kiwon dabbobi a ƙoluluwan dutse, ya ƙira sallah kuma yayi sallah, sai Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: "kuyi dubi zuwa wannan bawan Nawa, yana ƙiran sallah kuma yana tsayar da sallah, yana mai tsoro Na, haƙiƙa na gafarta mishi kuma Na shigar da shi Aljannah" (Abu Dawood 1203).

Sallah zuwa ga wuta

Mutane suna kunna wuta a tafiye-tafiyensu musamman a wurare masu sanyi, kuma ba mamaki ma wutar tana kasancewa ne a ɓangaren alkiblah, amma abunda yafi shi ne kada suyi sallah ta ɓnagaren da wutar take, musamman ma liman, domin kaucewa kama da Majusawa waɗanda suka kasance suna bauta wa wuta, da kuma cewa lalle zata ja hankalin mai sallah amma idan suka buƙace ta domin ɗumama wuri ko kuma canza mata wuri zai ba da wahala, to babu laifi.

Haɗa sallah da kuma taƙaita su a yayin tafiya

Abun nufi da hada tsakanin salloli biyu shi ne: Ka sallaci sallan azahar sai ka haɗa ta tare da ta la'asar, ko ka sallaci magariba sai ka haɗa ta tare da isha'i. sai ka sallaci salloli biyun a lokacin ɗaya daga cikinsu (Ko da ya kasance haɗawan gabatarwa ne ko na jinkirtawa). Kuma hakan zai faru ne yayin da aka samu uzurin da ya halatta hakan.

Kuma abunda ake nufi da taƙaita sallah shi ne ka sallaci dukkanin salloli masu raka'a huɗu raka'a bibbiyu, ma'ana sallan azahar, da na la'asar, da na isha'i, amma kuma sallar magariba da na asubahi ba a taƙaita su.

Daga cikin uzurin da suke ba da damar haɗa sallah da taƙaita su akwai tafiya: Abunda ake nufi da tafiya kuma shi ne fita daga gari zuwa wani wuri mai nisa wanda hakan ya kai a ƙira shi da tafiya, wasu daga cikin malamai sun ƙimanta nisanshi da ma'aunin zamani kaman kimanin kilomita 80. saboda haka idan mutum ya fita tafiyar shaƙatawa a kusa da garinsu ba zai taƙaita sallah ba, amma kuma idan yayi nisan da za a iya cewa yayi tafiya sai ya taƙaita ta, koda ace yawon shaƙatawar ya fita.

Taƙaita sallah (Ƙasaru) Sunnah ce ga matafiyi, amma kuma haɗa tsakanin salloli idan har ya kasance akan hanyar tafiya to zai iya haɗawa, haɗawan gabatarwa ko na jinkirtawa gwargwadon abunda ya dace da tafiyarshi, amma kuma idan a zaune yake a wuri guda, to abunda yafi shi ne ya sallaci kowace sallah akan lokacinta, musamman ma idan zai iya sallah da jama'an masallaci.

Ya wajaba akan matafiya da kada suyi wasa wajen gudanar da salloli akan lokacinsu sakamakon shagaltuwa da ababen tafiya, Allah Maɗaukaki Yace bayan Ya ambaci yanayin yaƙi :{Idan har kuka natsu to ku tsayar da sallah, domin lalle ita sallah ta kasance akan muminai farilla ce mai lokaci} [Annisa'i: 103).

Yayin haɗa sallah a cikin tafiya, ƙiran sallah guda ɗaya ya isa sai a tayarwa kowace sallah iƙamah, amma kuma azkar din sallah za ayi su ne a bayan sallah ta biyun.

Za a iya samun saɓani a cikin tafiya dangane da uzurin da zai iya ba da damar haɗa salloli da kuma taƙaita su, amma kuma asali shi ne lalle limami ko kuma jagoran tafiya (Kaman Uba alal misali) shi ne da alhaƙin wannan, sai yayi ƙoƙari idan ya kasance yana da sani, kuma ya shawarci wanda yake da sani, kuma idan bai gamsu da halaccin haɗawan ba to ba zai haɗa ba kuma ba zai taƙaita ba, kuma ya wajaba akan sauran jama'a da kada suyi jayayya da shi, domin haɗin kai ma ibadah ce mai zaman kanta.

Tafiye-tafiye da Azumi

Ba a nufan azumi a cikin tafiya don shi, amma kuma wanda ya sabawa kanshi azumin wasu kwanaki - kaman ranar litinin da alhamis alal misali- sai waɗannan kwanakin suka dace da ranakun tafiyarshi to ba laifi zai iya yin azuminshi.

Daga Anas Allah Ya kara mishi yarda yace: "Mun kasance a cikin tafiya tare da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga cikinmu akwai masu azumi kuma akwai waɗanda suka ajiye azumi, waɗanda sukayi azumi basu aibanta waɗanda basuyi ba, kuma waɗanda ba suyi ba basu aibanta waɗanda sukayi ba" (Bukhari: 1947, Muslim: 1118).

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa