Ɓangaren yanzu model
Darasi Shirka
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ma'anar Shirka
Misalai akan shirka
Haɗarin Dake Cikin Shirka
Shirka tana ɓata ayyuka kuma tana lalata ta kamar yadda Allah Ta'ala Yace: (Da ace sunyi Shirka, da duk abunda suka kasance suna aikata ya rushe a garesu) (Al-An'am: 88).
Shirka tana tabbatar da ma'abocinta a cikin wutan jahannama, Allah Madaukaki Yace: (Lalle duk wanda Yayi shirka ga Allah, to haƙiƙa Allah Ya haramta mishi Aljannah kuma makomarshi ita ce wuta) (Al-Ma'idah: 72).
Nau'ukan shirka
Shi ne bawa ya fiskantar da wani nau'i na ibadah zuwa ga wanin Allah Ta'ala, duk wani zance ko wani aiki na daga ibadah daga cikin ababen da Allah Madaukaki Yakeso, idan aka gudanar da su ga wanin Allah to hakan Shirka ne da kafurci. Misalin Babban shirka Shi ne mutum ya roƙi wanin Allah, ko yayi addu'a zuwa gare shi da neman waraka daga wata cuta, ko ya yalwata mishi arzikinshi, hakama idan mutum ya dogara akan wanin Allah, ko yayi sallah ga wanin Allah, ko yayi yanka ga wanin Allah.
Saboda haka fiskantar da waɗannan ayyukan da wasunsu zuwa ga wanin Allah shirka ne da kuma kafurci, domin waraka, da arziki sun keɓanta ne ga ubangiji, kuma dogaro da sallah da kuma yanka suna daga cikin tauhidin uluhiyyah.
2- Ƙaramin Shirka
Misalai akan ƙaramin shirka
Shin ana la'akarin tambayan mutane da neman biyan buƙata daga gare su shirka?
Roƙo ko neman biyan buƙata daga abunda baya motsi ko Mamaci shirka ne wanda ya saɓawa hankali da musulunci da kuma imani; Saboda mamaci da abunda ba ya motsi ba za su iya jin wannan buƙatar ko biyanshi ba, kuma domin lalle shi addu'a akaran kanshi ma ibadah ne kuma gudanar da shi ga wanin Allah shirka ne, kuma hakan ya kasance daga shirkan da larabawa suka kasance suna aikatawa yayin da aka aiko Annabi.