Ɓangaren yanzu model
Darasi Babban kari da kuma wanka
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ababen da suke wajabta wanka
1- Fitar Maniyyi
2- Jima'i
3- Fitan jinin haila da jinin biki
An sauƙaƙewa mai haila da mai biki kwanakin da jini yake fita, sai sallah da azumi su faɗi a kansu, kuma zasu biya azumi bayan sun tsarkaka, amma ba za su biya sallah ba.
Saduwa da mai haila da mai biki
Idan yayi niyar tsarkaka sai ya wanke dukkanin jikinshi da ruwa toh hakan yayi.
Mafi cikan wanka shi ne mutum yayi wanka tamkar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi wanka, idan yaso yin wankan janaba to lalle zai wanke tafukan hannunshi biyu, sa'annan ya wanke farjinshi da dauɗar dake wajen na daga janaba, sa'annan sai yayi cikakken alwala, sai ya wanke kanshi da ruwa sau uku, sa'annan ya wanke sauran jikinshi.
Idan musulmi yayi wankan janaba to babu shakka wannan ya isar mishi ga alwala, ba dole sai ya sake yin alwala tare da wankan ba, amma kuma abunda yafi shi ne yayi wankan da ya ƙunshi alwala kamar yadda yake a sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.