Ɓangaren yanzu model
Darasi Falalan Alkur'ani Mai Girma:
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Alkur'ani mai girma yanada manya-manyan falala kuma masu yawan gaske, daga cikinsu akwai masu zuwa:
Daga Usman Bin Affan Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi (S.A.W) yace: «Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur'ani ya kuma koyar da shi» [Bukhari: 5027].
Daga Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi (S. A. W) yace: «Lalle Allah Yana da iyali daga cikin mutane» sai sukace: ya Manzon Allah, su waye waɗannan? sai yace: Ma'abota Alkur'ani su ne iyalan Allah kuma makusantan Shi». [Ibnu Majah: 215]».
Daga Abdullahi Bin Mas'ud Allah Ya kara mishi yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Duk wanda ya karanta harafi ɗaya daga littafin Allah yanada kyakkyawan aiki ɗaya, kuma kowace kyakkyawa za a ninkata sau goma, bance Alif. Lam. Mim shi ne harafi ɗaya ba fah, saidai Alif harafi ne, lamun harafi ne, mimun ma wani harafi ne» Tirmizi ne ya rawaito [2910].
4. Sauƙan Mala'iku da natsuwa da rahama a wuraren da ake tilawar Alkur'ani ko ake darasunshi.
5. Ceton Alkur'ani ga ma'abotanshi
Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: Manzon Allah (S. A. W) yace: «Gwani a cikin Alkur'ani yana tare da mala'iku masu girma a wurin Allah, wanda kuma yake karanta Alkur'ani kuma yana in'ina a cikinshi kuma yana bashi wahala, toh yana da lada biyu» [Muslim: 798].
7. Alkur'ani yana ɗaga darajar ma'abocinshi:
Daga Abdullahi Bin Amru Binul Ãs Allah Ya kara musu yarda yace: Manzon Allah (S. A. W) yace: «Za a gayawa ma'abocin Alkur'ani: Ka karanta ka hau, kuma ka karanta shi tamkar yadda kake karantawa a cikin duniya, domin masauƙinka shi ne wurin ƙashen ayar da ka karanta» [Abu Dawood: 1464].