Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ma'anan Hajji da falalanshi

Hajji shi ne bautawa Allah Mai girma da ɗaukaka da nufan Makkah Almukarramah a cikin wani ƙayyadadden lokaci domin gudanar da wasu ayyukan bauta, kuma shi ne rukuni na biyar daga cikin rukunnan musulunci. A cikin wannan darasin zaka san ma'anan hajji da falalanshi.

  • Sanin Ma'anan Hajji
  • Sanin sharruɗan wajabcin Hajji
  • Sanin falalan Hajji

Ma'anan Hajji

Hajji shi ne nufan ɗakin Allah mai alfarma a wani ƙayyadadden lokaci domin gudanar da wasu ibadu, kuma su ɗin wasu ayyuka ne da zantuka waɗanda suka zo daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kaman ihrami da ɗawafi a kewayen ɗakin Allah sau bakwai da sa'ayi a tsakanin Safa da Marwa, da tsayuwa akan dutsen Arafah, da jifan Jamarat a Mina, da wanin haka. Kuma a cikinshi akwai alfanu masu yawa ga bayi na daga bayyana tauhidi ga Allah, da gafara mai girman wanda Alhazai suke samu, da kuma sanin juna a tsakanin Musulmai, da sanin hukuncen-hukuncen addini, da wanin haka

Hukuncin Hajji

Hajji shi ne rukuni na biyar daga cikin rukunnan musulunci, kuma ya wajaba akan kowana musulmi da musulma sau ɗaya a rayuwa ga wanda ya samu ikon tafarki zuwa gare shi. Allah Ta'ala Yace: (Kuma Allah Yana da aikin hajji akan mutane ga wanda ya samu ikon tafarki zuwa gare shi, kuma wanda ya kafurce, to lalle Allah Mawadaci ne ga barin talikai) (Ali Imran: 97).

Daga Abu Hurairah Allah Ya kara mishi yarda yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi mana huɗuba sai yace: «Ya ku mutane lalle Allah Ya farlanta muku hajji toh kuyi aikin hajji» sai wani mutum yace: Shin a kowana shekara ne ya Manzon Allah? sai Annabi yayi shuru, har sai da mutumin ya maimata wannan tambayar sau uku, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Da nace Eh, da ya wajaba da kuma bazaku iya ba» (Muslim: 1337).

Kuma ya wajaba akan kowana musulmi da yayi gaggawa zuwa sauƙe faralin hajji a duk lokacin da ya samu dama.

Lokacin Hajji

Hajji yana da lokuta na zamani da na wuri

Lokutan zamani

Hajji yanada wasu watanni na musamman, wanda baya halatta ga mutum da yayi haraman aikin hajji ba a cikinsu ba; kuma su ne: Shawwal, da Zul Ƙa'adah, da Zul Hijjah, Ayyukan hajji suna taruwa ne a tsakanin ranar bakwai zuwa ranar sha uku ga watan Zul Hijjah, kuma wannan wata shi ne watan goma sha biyu a jerin kalandar musulunci.

Lokutan wurare

Su ne wasu wuraren da baya halatta ga mai aikin hajji ko mai aikin umrah waɗanda suke zuwa daga wajensu da su wuce zuwa Makkah ba tare da ihrami ba. Saboda haka, Miƙatin mutanen Madinah shi ne Zul Hulaifah, Miƙatin mutanen Sham kuma shi ne Aljahfah, Miƙatin mutanen Najadu kuma shi ne Karnul Manazil, Miƙatin mutanen Yaman kuma shi ne Yalamlam, Miƙatin mutanen Iraqi kuma shi ne Zatu Irqi. Waɗannan Miƙatan nasu ne da kuma waɗanda suka biyo ta wurinsu waɗanda ba sa daga cikinsu, daga cikin waɗanda suke nufin Hajji ko Umrah, kuma waɗannan wuraren ana saninsu ne ta hanyan waɗanda suke da gogewa akan taswirorin zamani.

Sharruɗan Wajabcin Hajji

١
Musulunci
٢
Hankali
٣
Balaga
٤
Ƴanci
٦
Samun muharrami a tare da mace wanda zai raka ta

Sharaɗin farko: Musulunci

Hajji ya wajaba ne akan musulmi kuma baya wajaba akan kafuri, baya ma inganta daga gare shi; domin lalle musulunci shi ne sharaɗin ingancin ibadah.

Sharaɗi Na Biyu: Hankali

Hajji ba ya wajaba akan mahaukaci kuma baya inganta daga gare shi, domin hankali Sharaɗi ne na wajabci da kuma inganci, domin yazo a hadisi daga Aliyu Allah Ya kara mishi yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "An ɗaga alƙalami akan mutane guda uku, akan mai bacci har sai ya farka, akan yaro ƙarami har sai ya balaga, kuma akan mahaukaci har sai yayi hankali» Abu Dawood: 4403).

Sharaɗi Na Uku: Balaga

Hajji baya wajaba akan yaro ƙarami domin hadisin da yazo daga Aliyu Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "An ɗaga alƙalami akan mutane guda uku, akan mai bacci har sai ya farka, akan yaro ƙarami har sai ya balaga, kuma akan mahaukaci har sai yayi hankali» Abu Dawood: 4403).

Amma kuma da yaro ƙarami zaiyi aikin hajji da hajjinshi ya inganta, amma kuma wannan ba zai isar masa hajjin musulunci wanda ya wajaba akanshi ba. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace "Idan yaro ƙarami yayi aikin hajji toh wannan nashi ne har sai ya balaga, idan kuma ya balaga to wani aikin hajjin ya wajaba akanshi" (Mustadrakul Hakim: 1769).

Sharaɗi Na Huɗu: Ƴanci

Bawan da aka mallake shi hajji baya wajaba akanshi, kuma an bashi uzuri domin shagaltuwanshi da ayyukan mai gidanshi, amma da bawa zaiyi hajji da izinin mai gidanshi da hajjinshi ya inganta, amma kuma bazai isar mishi hajjin musulunci wanda yake wajibi akanshi ba. Hadisi yazo daga Ibnu Abbas Allah Ya kara musu yarda yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wani bawan da yayi aikin hajji sai daga baya aka ƴanta shi to wani aikin hajjin ya wajaba a gare shi" (Assunanan Alkubra na Baihaƙi: 8613).

Sharaɗi Na Biyar: Iko

Hajji yana wajaba ne akan wanda yake da iko, kuma shi ne mai lafiyan jiki, wanda zai iya tafiya, kuma yana da guzuri da abun hawa waɗanda zasu iya kai shi zuwa gudanar da aikin hajjin, daga cikin ikon aikin hajji ga mace kuma akwai samun muharrami wanda zai mata rakiya a cikin tafiyan hajji; domin baya halatta a gare ta da ta tafi zuwa aikin hajji ko zuwa wani wuri na daban ba tare da muharrami ba.

Allah Ta'ala Yace: (Kuma Allah Yana da aikin hajji akan mutane ga wanda ya samu ikon tafarki zuwa gare shi) (Ali Imran: 79).

Amma kuma wanda ya kasance yana da ikon dukiya amma bai da ikon gangan jiki sakamakon rashin lafiyan da ba a tsamanin warkewanshi, ko kuma saboda tsufanshi, to ya wajaba akanshi da ya samu wanda zaiyi aikin hajji a madadinshi. Daga Fadlu Ɗan Abbas lalle wani mutum ya tambayi Annabi (S. A. W) yace: Ya Manzon Allah lalle baba na musulunci ya riske shi alhali yana dottijo bazai iya zama akan abar hawarshi ba, shin zan iya yin hajji a madadinshi? sai yace: Shin baka gani ba da ace akwai bashi akanshi sai ka biya mishi, shin kanaga hakan yayi? yace: Eh, sai Annabi yace: "To kaje kayi hajji a madadin mahaifinka" (Musnad Ahmad: 1812).

Yanayin samun ikon Musulmi dangane da hajji:

١
Ya kasance yana da ikon hajji da kanshi, ma'ana ya kasance yana da damar isa zuwa Masallacin Harami da kanshi ba tare da wata wahalar da ba a saba da ita ba, kuma yanada kuɗin da zai mishi wannan hidimar, to anan lalle sauƙe faralin hajji ya wajaba akanshi.
٢
Ya samu ikon hajji da waninshi ba da kanshi ba, kuma shi ne wanda ba zai iya aikin hajji da kanshi ba saboda rashin lafiya ko tsufa, amma kuma ya samu wanda zai iya hajji a madadinshi, kuma zai iya bashi kuɗaɗen da zaiyi mishi wannan aikin hajjin, to anan ya wajaba a gare shi da ya biya aje ayi mishi.
٣
Wanda ba zai iya aikin hajji da kanshi ba, kuma ba zai iya da waninshi ba, to wannan aikin hajji ba ya wajaba a gare shi domin ba shi da iko. Misali kaman wanda bai da kuɗaɗen da sukafi ƙarfin buƙatunshi da buƙatun iyalanshi, balle ma yaje yayi aikin hajji, to irin wannan ba wajibi bane akanshi ya tara kuɗi domin ya samu ikon aikin hajji, sai dai a duk lokacin da ya samu dama ne hajji zai wajaba akanshi.

Sharaɗi Na Shida: Samun muharrami tare da mace a cikin tafiyan

An sharɗantawa wajabcin hajji ga mace da ya kasance a tattare da ita akwai muharrami. Saboda haka, hajji baya wajaba akan mace sai dai idan ya kasance mai mata rakiya a cikin wannan tafiyar muharramin ta ne, muharramanta kuma su ne: Mijinta ko wanda babu aure a tsakaninshi da ita har abada kaman Babanta, da kakanta, da ɗanta, da jikanta, da ƴan uwanta da ƴaƴansu, da baffanta da kuma kawunta.

Idan kuma mace tayi aikin hajji ba tare da muharrami ba ta wata hanyar da zata aminta a bisa kanta, to aikin hajjinta ya inganta kuma ya isar mata, amma kuma tayi laifi da aikata hakan.

Falalan Hajji

Falala masu girma da kuma alherai masu yawa sunzo akan aikin hajji, daga cikinsu:

1- Lalle yana daga cikin mafifitan ayyuka

Yayin da aka tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wana aiki ne yafi falala? yace: "Imani da Allah da ManzonShi" akace sai wanne? sai yace: "Jihadi a tafarkin Allah" akace sai wanne? sai yace: "Karɓaɓɓen hajji" (Bukhari: 1519, Muslim: 83).

2- Babban lokacin gafara ne

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda yayi aikin hajji ba tare da yayi wargi ko fasiƙanci ba, zai dawo ne kaman yadda mahaifiyarshi ta haife shi" (Bukhari: 1521, Muslim: 1350), Abun nufi shi ne zai dawo ba tare da zunubbai ba tamkar yadda ake haifan jariri.

3- Babbar dama ce na ƴantawa daga wuta

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Babu wani yinin da Allah Yafi ƴanta bayi a cikin shi kaman ranar Arafah" (Muslim: 1348).

4- Lalle sakamakonshi shi ne Aljannah

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Karɓaɓɓen hajji bashi da sakamako face Aljannah" (Bukhari: 1773, Muslim: 1349). kuma waɗannan falalan da wasunsu zasu kasance ne ga wanda ya gaskata anniyarshi ya kuma inganta ta, ya tsaftace baɗininshi, kuma ya bi koyarwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa