Ɓangaren yanzu model
Darasi Imani Da Ƙaddara
Ma'anar Imani Da Ƙaddara
Shi ne gaskata cewa lalle duk wani alheri da kuma sharri yana faruwa ne da hukuncin Allah da kuma ƙaddararshi, kuma Allah shi ne mai aikata abunda yakeso, babu wani abunda zai iya faruwa sai da nufinShi, Kuma babu wani abunda zai iya fita daga cikin sonShi, kuma babu wani abu a cikin duniya wanda ya isa ya fita daga cikin ƙaddararShi, kuma babu abun da zai faru sai da gudanarwar Shi, kuma duk da haka lalle Shi Ya umarci bayi kuma ya hanasu, kuma ya sanya su masu zaɓi ne a cikin ayyukansu, ba waɗanda aka tursasa su akan ayyuka ba, sai dai suna faruwa ne daidai da sonsu da kuma manufansu, kuma Allah Shi ne Mahaliccinsu da Mahaliccin ƙaddarorinsu, Yana shiryar da wanda Yake so da rahamarShi, kuma Yana ɓatar da wanda Yake so da hikimarShi, ba a tambayanshi akan abunda ya aikata amma kuma Shi Mai tambayar kowa ne akan aikin shi.
Ma'anar Ƙaddara
Ƙaddara: Shi ne yadda Allah Ta'ala Yake ƙaddara faruwan abubuwa tun fil azal, Da saninShi cewa lalle zasu faru a cikin wasu sanannun lokuta da keɓantattun siffofi, da rubuta hakan da Yayi, da son da Yayi su faru, da kuma halittansu da yayi, da faruwansu kamar yadda ya ƙaddara su.
Imani da ƙaddara wajibi ne kuma ɗaya ne daga cikin rukunnan imani, kamar yadda yazo a cikin amsar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayin da mala'ika Jibrilu ya tambaye shi dangane da imani, sai yace: "Shi ne kayi imani da Allah, da mala'ikunshi, da litattafanshi, da Manzanninshi, da ranar ƙarshe, kuma kayi imani da ƙaddara alherin shi da sharrinshi" (Muslim: 8).
Menene Imani Da Ƙaddara Ya Ƙunsa?
Imani da ƙaddara ya ƙunshi ababe huɗu:
1- Ilimi (Sani)
Imani da cewa lalle Allah Masanin dukkan komai ne, a jumlace da kuma a fayyace, kuma lalle Shi Allah Ta'ala Yasan dukkanin halittunShi gabanin Ya halicce su kuma Ya san arzikinsu, da ajalinsu, da zantukansu, da ayyukansu, da dukkanin motsinsu da natsuwarsu, da sirrukansu, da ababen da sukayi a bayyane, da waye ne ɗan Aljannah daga cikinsu, da kuma waye ne ɗan wuta daga cikinsu. Allah Maɗaukakin Sarki Yace: (Shi ne Allah Wanda babu wani abun bautawa da cancanta sai Shi, Masanin abunda ke ɓoye da wanda ke bayyane)(Alhashir: 22).
2- Rubutu
Imani da cewa lalle Allah Ta'ala Ya rubuta dukkanin ababen da ya sani a cikin lauhul mahfuz. Kuma dalilin wannan shi ne faɗin Allah Ta'ala: (Babu wani abunda zai faru na daga wani abu a cikin ƙasa ko a cikin sama, ko a cikin kawunanku face yana cikin littafi gabanin aukuwanshi). (Alhadid: 23). Da kuma faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Lalle Allah Ya rubuta ƙaddarorin halittu gabanin halittan sammai da ƙassai da shekaru dubu hamsin" (Muslim: 2653).
4- Mashi'a (So)
Imani da Mashi'ar Allah abar zantarwa wacce babu wani abunda zai iya mayar da ita, da kuma ƙaddararShi wacce babu wani abunda ya gagare ta. Saboda haka, dukkanin ababe sun faru ne cikin mashi'ar Allah da ƙaddararShi, duk abunda Allah Yaso zai kasance, kuma duk abunda da Allah bai so ba ba zai kasance ba. Allah Maɗaukaki Yace: Kuma babu wani abunda zaku so face abunda Allah Ya so) (Attakwir: 29).
4- Halitta
Imani da cewa lalle Allah Maɗaukaki Shi ne wanda Ya samar da ababe gaba ɗaya, Kuma Shi kaɗai ne Mahalicci, kuma dukkanin abunda ba shi ba halitta ne, kuma lalle Shi Mai iko ne a bisa dukkan komai. Allah Ta'ala Yace:(Kuma Shi Ya halicci dukkan komai Ya kuma ƙaddara shi ƙaddarawa) (Alfurkan: 2).
Mutum Yanada Zaɓi Da Ƙudura Da Kuma Iradah:
Imani da ƙaddara baya kore cewa lalle mutum yanada Mashi'a cikin ayyukanshi da yake zaɓa, da kuma iko akansu; domin shari'a da kuma ababen da suke faruwa sun tabbatar mishi da hakan.
Amma a shar'a, to haƙiƙa Allah Ta'ala Yace dangane da mashi'a: (Wancan shi ne ranar gaskiya, kuma duk wanda yakeso sai ya riƙi makoma zuwa ubangijin shi) (Annaba'i: 39). Kuma Allah T'ala Yace (Allah Baya kallafawa rai saidai abunda zata iya, abunda ta aikata na alheri nata ne kuma abunda ta aikata na sharri yana kanta) (Albakara: 286) Kuma ma'anar iyawa anan shi ne iko.
Amma kuma dubi da abunda ke faruwa, babu shakka kowana mutum yasan da cewa yanada mashi'a da ƙudura wadanda dasu yake gudanar da lammuranshi, kuma dasu yake barin aikata wani aiki, da su kuma yake bambance tsakanin ababen da suke faruwa da son shi kaman tafiya da kuma ababen da ba da son shi suke faruwa ba kaman tuntuɓe da faɗuwan ba zata, saidai abunda bawa yakeso da kuma ƙudurarsa dukkaninsu suna ƙarƙashin ƙaddarar Allah da mashi'arShi ne kaman yadda Allah Yace: (Ga wanda yaga damar miƙewa a cikinku * Kuma babu abunda za kuso face Abunda ubangijin talikai Yaso) (Attakwir: 28-29). A cikin wannan Ayar sai Allah Ya tabbatarwa mutum da mashi'a sa'annan kuma Ya bayyana cewa lalle mashi'ar mutum tana ƙarƙashin mashi'ar Allah Ta'ala ne, kuma saboda dukkanin duniya mulkin Allah ne, to babu wani abunda ya isa ya faru a cikinta ba tare da ilimin Allah da kuma saninShi ba.
Ƙudurar mutum da zaɓinshi su ne suke da alaƙa da kallafawa, da umarni da kuma hani, sai a sakawa mutumin kirki domin shi ya zaɓi hanyar shiriya a kuma hukunta wanda ya munana domin shi ya zaɓi hanyar ɓata. Saboda Allah Ta'ala bai kallafa mana abunda ba zamu iya ba, kuma bazai saurari wanda ya bar bautarshi da hujjar ƙaddara ba.
Sa'annan kuma mutum gabanin ya aikata aikin zunubi ai bai san menene ilimin Allah da ƙaddararShi ba, kuma lalle Allah Ya bashi iko da kuma zaɓi Ya kuma bayyana mishi hanyoyin alheri da na sharri, saboda haka idan har ya aikata zunubi, to shi ya zaɓi aikata hakan, ya kuma fifita shi a bisa biyayya ga Allah, saboda hakane zai ɗauki hukuncin laifinshi.
Amfanin Imani Da Ƙaddara:
Imani da hukuncin Allah da kuma ƙaddararShi suna da amfani da yawa a cikin rayuwar musulmi, daga cikinsu:
1- Ingantaccen imani da ƙaddara yana taimakawa wajen aikata ayyuka na gari da kuma riƙo da sabbuba, kuma yana taimakawa wajen hana gangancin barin aikata ayyuka
Saboda haka lalle an umarci muminai da rike sababi tare da dogaro akan Allah Ta'ala, da kuma imani da cewa lalle ba sabbuba bane suke bayar da sakamako sai da izinin Allah, domin lalle Allah Shi ne Mahaliccin sabbuban, kuma Shi Ya halicci sakamako. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ka kwaɗaitu a bisa ababen da zasu amfane ka, ka nemi taimakon Allah, kuma kada ka karaya, kuma idan wani abu ya same ka, kada kace lalle da na aikata kaza da ya zamto kaza da kaza, saidai kace: Allah ne Ya ƙaddara kuma Yanda Yakeso haka Yayi, domin da na... yana buɗe ƙofar shaiɗan" (Muslim: 2664). Kuma a lokacin da wasu mutane sukayi zaton cewa babu buƙatar aiki domin lalle an riga an ƙaddara ayyuka, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare ya bayyana kuskuren hakan yana mai cewa: (Kuyi aiki domin kowa an sauƙaƙe mishi abunda aka halicce shi domin shi) sa'annan sai ya karanta faɗin Allah: (Kuma duk wanda ya bayar, yayi taƙawa, ya kuma gaskata lahira (Allaili: 6) har zuwa faɗin Allah:(To zamu sauƙaƙe mishi hanya zuwa ga wahala) (Alaili: 10). [Bukhari: 4949, Muslim: 2647].
2- Mutum Yasan Kimar Kanshi
Saboda haka kada yayi girman kai da taƙama, domin lalle shi mai rauni ne dangane da sanin abunda aka ƙaddara mishi, da kuma abunda zai faru anan gaba, daga nan ne mutum zai tabbatar da rauninshi da kuma buƙatuwarshi zuwa ubangijin shi Mai girma da ɗaukaka a koda yaushe. Domin mutum idan alheri ya same shi, sai yayi girman kai ya kuma ruɗu, idan kuma sharri da musiba suka same shi, sai ya shiga tashin hankali ya kuma yi baƙin ciki, kuma mutum ba zai kuɓuta daga girman kai da jiji da kai yayin da alheri ya same shi ba, da kuma baƙin ciki da damuwa yayin da sharri ya same shi ba sai da imani da ƙaddara, da kuma sanin cewa duk wani abunda ya faru toh dama akwai shi a cikin ƙaddara, kuma Allah Ya san da cewa hakan zai faru.
3- Lalle Zai Samu Nasara Akan Cutar Hasada
Domin lalle cikakken mumini ba zai yiwa mutane hasada akan abunda Allah Ya basu na daga falalarShi ba; saboda Allah ne Ya azurta su Ya kuma ƙaddara musu hakan, kuma shi yasan cewa a yayin da yake yiwa waninshi hasada to lalle yana ƙalubalantan hukuncin Allah ne da kuma ƙaddararShi.
4- Imani da ƙaddara yana gadarwa zuciya jarumta wajen fiskantar wahalhalun rayuwa
Kuma yana ƙarfafa azama a cikin rayuwa, domin mutum zai samu tabbacin cewa lalle arziki da ajali dukkansu an ƙaddara su ne, kuma babu abunda zai samu mutum sai abunda aka rubuta mishi.
5- Imani da ƙaddara yana tabbatarwa mumini haƙiƙanin imani a zucciyar shi
A koda yaushe zai kasance mai neman agajin Allah, kuma zai dogara akanShi tare da riƙo da sabbuba, kuma a koda yaushe zai kasance mabuƙaci zuwa ga Allah, yana mai neman taimakonShi a bisa tabbata akan daidai.
6- Imani da ƙaddara yana gadar da natsuwa a cikin zuciya
Sai mumini ya gane cewa lalle duk wani abunda ya same shi bai zamto don ya kuskure shi, kuma duk wani abunda ya kuskure shi bai zamto don ya same shi ba.