Ɓangaren yanzu model
Darasi Sharruɗan Sallah Da Hukunce-hukuncenta
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Sharruɗan Sallah
Tsarkaka daga kari da kuma najasa. Daga Abdullahi Bin Umar Allah Ya kara musu yarda yace: lalle ni naji Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: «Ba a karɓan sallah ba tare da alwala ba» (Muslim: 224).
An sharɗanta rufe al'aura da tufafin da baya nuna sassan jiki domin gajartanshi ko kasancewar shi shara-shara.
Daga cibiya zuwa gwiwa
Dukkanin mace al'aura ne face fuskarta da tafin hannunta. Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda tace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Ba a karɓan sallar mai haila [Ma'ana balagaggiya] sai ta suturta jikinta» (Abu Dawood: 641, Attirmizi:377)
Allah Ta'ala Yace: (Kuma ta duk inda ka fito to ka juya fuskarka zuwa ɓangaren Masallacin Harami (Albakara: 149).
Alkiblar musulmai ita ce Ka'abah mai darajah wacce baban Annabawa ya gina ta Ibrahim alaihis salam, kuma dukkanin Annabawa alihimus salamu sukayi hajji zuwa gare ta, kuma lalle mu mun san cewa ita duwatsu ne ba sa amfanarwa kuma ba sa cutarwa, sai dai Allah Maɗaukaki ne Ya umarce mu da mu fiskance ta yayin sallah, domin dukkanin musulmai su fiskanci ɓangare guda, sai wannan fiskantar ma ta zamto ibadah.
Yadda ake fiskantar Alkiblah
Wajabcin fiskantar alkiblah ya faɗi akanshi yayin kasawa, kamar yadda dukkanin ababen da suke wajibi suke sauƙa daga kan mutum yayin da ya gagara aikata su. Allah Ta'ala Yace: kuji tsoron Allah gwargwadon ikonku) (Attagabun: 16).
Kuma shi sharaɗi ne na ingancin sallah, kuma sallah bata inganta gabanin shigan lokacinta, kuma an haramta jinkirta ta akan lokacinta, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: (Lalle sallah ta kasance farillah ce mai lokaci akan muminai) (Annisa'i: 103).
Abunda yafi shi ne gudanar da sallah a farkon lokacinta. Daga ummu firwata Allah Ya kara mata yarda tace: An tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wana aiki ne yafi? sai yace: "Sallah a farkon lokacinta» (Abu Dawood: 426).
Wajibi ne a tsayar da sallah a cikin lokacinta, kuma an haramta jinkirta ta sai dai a cikin yanayin da akayi rangwamen haɗa tsakanin salloli guda biyu.
Ya wajaba akanshi da ya gaggauta biyanta a yayin da ya tuna ta. Daga Anas Bin Malik Allah Ya kara mishi yarda yace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Duk wanda ya manta wata sallah ko yayi bacci akanta, to kaffararta shi ne ya sallace ta a lokacin da ya tuna ta» (Muslim: 684).
Wajabcin Sallah
Kuma ana hukunta cewa mutum ya balaga ne yayin da ɗaya daga cikin waɗannan alamomin suka bayyana a gare shi:
Salloli farillai biyar da lokutansu
Raka'a biyu ce, kuma lokacinta yana farawa ne daga ketowan alfijir na biyu kuma shi ne farawan bayyanan haske a sararin sama daga ɓangaren gabas, kuma lokacinta yana karewa ne da fitowan rana.
Raka'a huɗu ne, kuma lokacinta yana farawa ne daga lokacin zawalin rana -karkacewan rana daga tsakiyar sama zuwa ɓangaren yamma bayan- kuma lokacinta yana ƙarewa ne yayin da inuwar kowana abu ya zamto tamkarshi a tsawo.
Ita ma raka'a hudu ce, kuma lokacinta yana farawa ne daga fitan lokacin sallar azahar yayin da inuwan kowana abu ya zamto tamkarshi a tsawo, kuma yana ƙarewa ne da faɗuwan rana, ya kamata musulmi ya gaggauta sallar kafin hasken rana ya dishe kuma launinta ya canza.
Kuma ita raka'a uku ce, lokacinta yana farawa ne daga fadɗuwan rana da fakewan shatinta a sama, yana kuma ƙarewa da fakewan shafaƙi ja wanda yake bayyana bayan faɗuwar rana.
Kuma ita raka'a huɗu ce, lokacinta yana farawa ne daga fakewan shafaƙi ja, kuma yana ƙarewa da shiga tsakiyan dare, kuma yayin uzuri akan iya sallatan ta har zuwa lokacin ketowan alfijir.