Ɓangaren yanzu model
Darasi Zakkah: Haƙiƙaninta Da Manufofinta
Zakkah ita ce rukuni na uku daga cikin rukunnan musulunci, kuma ita wajibi ne na dukiya wanda Allah Ya farlanta wa masu kuɗi domin su baiwa talakawa da mabuƙata da wasunsu na daga waɗanda suka cancanci wani kashi na musamman daga dukiyarsu domin magance matsalolinsu.
1. Lalle an halicci rai da son dukiya, wanda hakan ya saka mutum yake kwaɗaituwa wajen ganin ya kiyaye ta kuma yayi riƙo da ita, sai Allah Ya shar'anta fitar da Zakkah domin tsarkake rai daga cutar rowa da kwaɗayi, da kuma magance son duniya da riƙo da ƙawarta, Allah Ta'ala Yace: (Ka ɗauka daga cikin dukiyarsu sadaka ce, zaka tsarkake su kuma zaka tsaftace su da shi)(Attaubah: 103).
2. Fitar da zakkah yana ƙarfafa igiyar soyayya da tausayawa; saboda Allah Ya halicci ran mutum akan son wanda ya kyautata mata, da hakane mutane zasu rayu tare cikin soyayya da haɗin kai, tamkar tabbataccen gini wani shashi yana ƙarfafa wani shashin, kuma sai cutar sata, da fashi da yaudara su ragu a cikin Al-ummah.
3. Da fitar da zakkah ne za a tabbatar da ma'anar bauta wa Allah da ƙasƙantar da kai zuwa gare Shi, da kuma cikakken miƙa wuya ga Allah ubangijin talikai, domin a yayin da mawadaci ya bayar da zakkan dukiyarshi zai kasance ya aiwatar da shari'ar Allah ya kuma zantar da umarninShi, kuma a cikin fitar da zakkah akwai godewa ni'imar Allah Mai girma da ɗaukaka, kuma Allah zai saka mishi a bisa wannan godiyar, Allah Ta'ala Yace: (Lalle idan kuka gode zan ƙara muku) (Ibrahim: 7).
4. Za a samu haɗin kai sosai da kuma fahimtar juna cikin bayar da zakkah, kuma za a samu wani nau'i na daidaito tsakanin mutanen dake rayuwa a wuri guda, domin da bayar da ita zuwa waɗanda suka cancance ta ne dukiya ba zata zamto a koda yaushe tana daskare a hannun mawadata ba. Allah Ta'ala Yace: (Domin kada dukiyar ta zamto tana jujjuyawa a tsakanin mawadata daga cikinku) (Alhashr: 7).
Musulunci ya ƙayyada kalan mutanen da za a baiwa zakkah. kuma ya halatta ga mutum da ya baiwa kala ɗaya daga cikinsu ko kuma fiye da haka, ko ya baiwa ma'aikata da hukumomin ayyukan alheri waɗanda suke ɗaukan nauyin raba ta ga waɗanda suka cancance ta na daga cikin musulmai, amma kuma abunda yafi shi ne a rabata a cikin garin da wanda ya fitar da zakkan yake rayuwa.