Ɓangaren yanzu model
Darasi Manzancin Annabi Muhammad (S. A. W)
Buƙatuwan Ƴan Adam zuwa ga Manzanni
Yana daga cikin hikimar Allah Maɗaukakki da Ya aika mai gargadi a cikin kowace Al ummah wanda zai dinga bayyana musu ababen da Allah Ya saukarwa bayinShi na daga Addini da kuma shiriya wanda su ne zasu gyara musu yanayin rayuwansu na duniya da kuma na lahira. Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma babu wata Al-Ummah face mai gargaɗi yazo mata}[Suratu Fadir: 24]
Domin lalle babu tsira kuma babu rabauta a cikin Duniya da lahira sai dai a hannun Manzanni, kuma babu wata hanyar da za a san kyawawan ababe da kuma munanansu a bayyane sai ta wurinsu, kuma ba a samun yardan Allah Maɗaukaki sai ta hannunsu, saboda haka kyawawan ayyuka, da na zantuka, da kuma kyawawan halaye dukkansu shiriyansu ne kuma waɗannan su ne ababen da suka zo da su.
Imani da Muhammad (S. A. W) a matsayin Annabi da kuma Manzo
Zamuyi imani da cewa Muhammadu (S. A. W) bawan Allah ne kuma ManzonShi ne, kuma shi ne shugaban mutanen farko da na ƙarshe, kuma shi ne cikamakin Annabawa babu wani Annabin da zai zo a bayanshi, kuma haƙiƙa ya isar da manzanci, kuma ya cika amana, kuma ya yiwa Al-ummah nasiha, kuma yayi matiƙar ƙoƙari a cikin addinin Allah.
Allah Maɗaukaki Yace: {Muhammadu Manzon Allah ne} [Suratul Fathi: 29].
Kuma ya wajaba a gare mu da mu gaskata shi cikin ababen da ya labarta, kuma muyi mishi biyayya cikan ababen da yayi umarni da su, kuma mu nisanci duk wani abunda ya hana ya kuma tsawatar a gare shi, kuma mu bautatawa Allah a bisa sunnarshi, kuma mu koikoye shi (S. A. W)
Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne cikamakin Annabawa da Manzanni, kuma babu wani annabin da zai zo a bayanshi, kuma manzancinshi shi ne cikamakin dukkanin manzancin da suka gabata, kuma addininshi shi ne cikamakin dukkanin addinai.
Allah Maɗaukaki Yace:{Muhammadu bai kasance mahaifin ɗaya daga cikinku ba, saidai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa} [Ah-Ahzab: 40].
An karɓo daga Abu Huraira Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi (S. A. W) yace: "Lalle misali na da misalin Annabawan da suka rigaye ni tamkar wani mutum ne wanda ya gina gida sai ya kyautata shi ya kuma ƙyawata shi, sai ya bar wani tubali a wata kusurwa ba tare da ya sanya shi ba, sai mutane suka kasance suna kewaye wannan gidan yana burge su kuma suna cewa: ina ma da an sanya wannan tubalin? sai yace: Toh ni ne wannan tubalin kuma ni ne cikamakin Annabawa" [Bukhari: 3535]
Mafificin Manzanni da kuma Annabawa
Annabinmu Muhammadu (S. A. W) shi ne mafificin Annabawa, shi ne mafificin halitta gaba ɗaya, kuma yafi su matsayi a wurin Allah Maɗaukaki, Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ɗaukaka lamarinshi, kuma Ya ɗaga darajanshi, saboda haka shi ne mafificin halitta kuma mafi darajansu a wurin Allah, kuma yafi kowa alfarma a gaban Allah Maɗaukaki, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma Allah Ya sauƙar maka da littafi da hikima, kuma Ya sanar da kai abunda baka kasance ka sani ba, kuma falalar Allah ta kasance mai girma ne akanka} [Annisa'i: 113], kuma Allah Maɗaukaki Yace yana mai Yiwa Annabinshi magana: {Kuma mun ɗaukaka maka ambatonka} [Inshirah: 4]
Saboda haka shi ne shugaban dukkanin ƴan Adam, kuma shi ne farkon wanda kabari zai tsage mishi, kuma shi ne farkon wanda zaiyi ceto, kuma shi ne farkon wanda za a ceta, kuma tutar godiya a hannunshi take ranar Alkiyama, kuma shi ne farkon wanda zai ƙetare Siraɗi, kuma shi ne farkon wanda zai ƙonƙosa ƙofar Aljannah, kuma shi ne farkon wanda zai shige ta.
Allah Maɗaukaki Ya aiko Muhammadu domin ya zamto rahama ga talikai, saboda haka manzancinshi gamamme ne ga dukkanin mutane da Aljanu, kuma an aiko shi ne zuwa ga dukkanin mutane. Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma bamu aiko ka ba face ka kasance rahama ga dukkanin talikai}. [Anbiya: 107].
Kuma Allah Maɗaukaki Yana cewa: "Kuma bamu aiko ka ba face ga dukkanin mutane} [Saba'i: 28]. Kuma Allah Yace: {Kace ya ku mutane, lalle ni manzon Allah ne zuwa gare ku baki ɗaya} [A'arafi: 158].
Sai Allah Maɗaukaki ya aiko shi domin ya zamto rahama ga talikai domin ya fitar dasu daga duhun shirka da kafurci da kuma jahilci, zuwa hasken Ilimi da imani da kuma tauhidi, domin su samu gafarar Allah da yardanShi su kuma tsira daga ukubarShi da kuma fushinShi.
Wajabcin Imani da shi da kuma bin sunnoninshi
Manzancin Annabi Muhammadu ya goge dukkanin manzancin da suka gabata, saboda haka Allah ba zai karɓi addini daga wurin wani ba sai da bin annabi Muhammadu (S. A. W), kuma babu wanda zai isa zuwa ga ni'imar Aljannah sai ta hanyarshi, domin shi Annabi (S. A. W) shi ne mafificin Manzanni, kuma Al-ummarshi ita ce mafificiyar Al-ummah, kuma shari'arshi ita ce mafi cikan shari'a.
Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma duk wanda ya riƙi wani addinin da ba musulunci ba to ba za a karɓa daga gare shi ba, kuma a ranar lahira zai kasance daga cikin masu asara} [Ali Imran: 85].
Daga Abu Huraira daga Annabi (S. A. W), lalle yace: "Na rantse da wanda ran Muhammadu yake hannunshi, babu wani wanda zaiji labari na a cikin wannan Al-ummar bayahude ne ko banasare, sa'annan ya mutu ba tare da yayi imani da abunda aka aiko ni da shi ba, face ya kasance daga cikin mutanen wuta" [Muslim: 153]
Daga cikin mu'ujizozin Annabi (S. A. W) waɗanda suke nuna gaskiyan Manzancinshi
Allah Mai girma da ɗaukaka Ya taimakawa Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da manya-manyan mu'ujizozi, da kuma ayoyi daban-daban, waɗanda a cikinsu akwai ababen da suke nuna gaskiyan Manzancinshi da Annabcinshi, daga cikin waɗannan mu'ujizozin akwai:
Mafi girman ayar da aka baiwa Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne Alkur'ani mai girma wanda yake magana da zukata da kuma hankali, kuma shi aya ce wacce zata wanzu har zuwa ranar Alkiyama, canji ko musanya bazai taba samunshi ba, saboda shi ya gagara a cikin laffuzanshi da usulubinshi, kuma yana da mu'ujiza a cikin shari'o'inshi da hukunce-hukuncenshi, kaman yadda yake da mu'ujizozin a cikin labaranshi
Allah Maɗaukaki Yace: "Kace da ace mutane da kuma Aljanu zasu taru akan su kawo irin wannan Alkur'anin ba zasu kawo irinshi ba, koda ace sashinsu yana taimakawa shashi} [Al-Isra: 88].
Allah Maɗaukaki Yace {Alkiyama ta kusanto kuma wata ta tsage * Idan suka ga wata aya sai su kau da kai suce wannan sihiri ne mai wanzuwa} [Alkamar: 1,2] kuma wannan tsagewan watar ya faru ne a cikin rayuwanshi (S. A. W) kuma Ƙuraishawa sun ganshi da ma waninshi.
Domin waɗanda suke tare da shi su samu su ci kuma su rage daga gare shi, daga cikin wannan akwai hadisin da aka rawaito daga Samrata Ɗan Jundubi, yace: "Wata rana mun kasance a wurin Annabi (S. A. W) sai aka kawo wani akushi da abinci a cikin shi", yace: sai Annabi yaci sauran jama'a ma suka ci, mutanen basu gushe ba suna ta cin shi har zuwa kusa da lokacin Azahar, waɗannan jama'an zasu ci, sai su tashi, sai wasu su zo su zauna su maye gurbinsu su ma su ci" [Musnad Ahmad: 20135]
Sai kuma ya faru kamar yadda ya ba da labarin, kuma ababen da ya ba da labari da yawa sun faru, kuma har yanzu bamu gushe ba muna ganin ababen da ya ba da labarinsu suna faruwa.
Daga Anas Allah Ya kara mishi yarda, lalle Umar Ɗan Khaɗɗabi Allah Ya kara mishi yarda ya fara basu labarin mutanen Badar, sai yace: lalle Manzon Allah (S. A. W) ya kasance yana nuna mana kaburburan mutanen Badar jiya, sai ya kasance yana cewa: " wannan shi ne kabarin wane gobe, in Allah Ya yarda", yace: sai Umar yace: na rantse da wanda ya aiko shi da gaskiya basu kauce iyakokin da Manzon Allah (S. A. W) ya nuna ba" [Muslim: 2873]
Haƙƙoƙan Annabi (S. A. W) akan Al-ummanshi suna da yawa, daga cikinsu akwai masu zuwa:
1. Imani da Annabtanshi (S. A. W)
Imanin da Annabtanshi da Manzancinshi da kuma yarda da cewa Manzancinshi ya goge dukkanin manzancin da suka gabata.
2.Gaskantashi (S. A. W)
Gaskanta shi cikin abunda ya bayar da labari, da mishi biyayya cikin abunda yayi umarni da shi, da nisantar ababen da yayi hani daga gare su ya kuma tsawatar, kuma ba za a bautatawa Allah ba sai da abunda ya shar'anta. Allah Maɗaukaki Yace: Kuma dukkanin abunda Manzo yazo muku da shi ku riƙe shi kuma abunda ya haneku daga gare shi ku hanu} [Alhashri: 7].
3. Karɓan Abunda Yazo Dashi (S. A. W)
Ya wajaba a gare mu da mu karɓi abunda Annabi (S. A. W) yazo da shi, kuma mu miƙa wuya ga sunnoninshi, kuma mu girmama shiriyanshi matiƙar girmamawa, kamar yadda Allah Maɗaukaki Yace: {Na rantse da ubangijinka ba zasuyi imani har sai sun sanya ka mai hukunci a cikin abunda ya wakana a tsakaninsu, sa'annan ba zasu samu su wata damuwa daga hukuncin da ka yanke ba, kuma su miƙa wuya miƙawa} [Annisa'i: 65].
4. Gujewa Saɓawa Umarninshi:
Ya kamata mu gujewa saɓawa umarninshi (S. A. W) domin saɓawa umarninshi sababi ne na fitina da ɓata da kuma azaba mai raɗaɗi, Allah Maɗaukaki Yace: "Waɗanda suke saɓawa umarninshi su kula domin fitina zata iya samunsu ko kuma azaba mai raɗaɗi}[Alnoor: 63].
5. Gabatar Da Soyayyarshi (S. A. W) A Bisa Soyayyar Kowa
Wajibi ne mu gabatar da soyayyar Annabi (S. A. W) a bisa son kai, da mahaifi da yara, da ma dukkanin halittu. An karɓo hadisi daga Anas yace: Annabi (S. A. W) yace: "Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai na kasance nafi soyuwa a gare shi fiye da ɗanshi, da mahaifinshi, da ma dukkanin mutane" [Bukhari: 15], kuma Umar Ɗan Khaɗɗabi Allah Ya kara mishi yarda yace: Ya Manzon Allah wallahi kai kafi soyuwa a gare ni fiye da kowana abu sai dai kaina, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Har yanzu ya kai Umar, na rantse da wanda rai na yake hannunshi, har sai na kasance nafi soyuwa a gare ka fiye da kanka" sai Umar yace: Toh lalle a yanzu nafi sonka fiye da kai na wallahi, sai yace: Toh yanzu ne imaninka ya cika Umar.
6. Yin Imani Da Cewa Lalle Shi (S. A. W) Ya Isar Da Saƙo
Wajibi ne muyi imani da cewa lalle Manzon Allah ya isar da cikakken saƙon manzanci, kuma ya cika amana, kuma ya yiwa Al-ummah nasiha, domin babu wani alheri face ya nunawa Al-ummah kuma ya kwaɗaitar da su zuwa gare shi, kuma babu wani sharri face ya hana Al-ummah daga gare shi kuma ya tsawatar mata. Allah Maɗaukaki Yace: {A yau ne Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni'imata a gare ku, kuma na yarda da musulunci a matsayin addini a gare ku} [Alma'idah: 3].
Kuma sahabban Annabi sun shaida cewa ya isar da saƙon manzanci a cikin wani mafi girman taro a ranar da yayi musu huɗuba a hajjin bankwana, an rawaito a cikin hadisin Jabir cewa lalle Annabi (S. A. W) yace: "Idan aka tambayeku dangane da ni me zakau faɗa? " sai suka ce: Zamu shaida cewa lalle kai ka isar, kuma ka cika, kuma kayi nasiha, sai ya ɗaga manuniyarsa zuwa sama yace: Ya Allah Ka shaida, ya Allah Ka shaida, har sau uku.[Muslim: 1218]