Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Imani Da Kasancewan Allah Abun Bauta (Uluhiyyah)

Allah Mai girma da ɗaukaka shi ne abun bautawa na gaskiya, kuma duk wani abun bauta koma bayanshi shirme ne. A cikin wannan darasin zaka san ma'anar tauhidin Uluhiyyah da kuma mahimmancin shi.

  • Sanin ma'anar tauhidin Uluhiyyah. 
  • Sanin Mahimmancin tauhidin Uluhiyyah 

Ma'anar tauhidin Uluhiyyah:

Haƙiƙanin gaskata cewa lalle Allah Ta'ala shi kaɗai ne ya cancanci dukkanin nau'ukan ibadah na bayyane da na ɓoye, saboda hakane zamu kaɗaita Allah da dukkanin nau'ukan Ibadah, kaman Addu'a da tsoro da tawakkali da neman agaji da sallah da zakkah da azumi, domin babu wani wanda ya cancanci bauta face Allah Ta'ala, kaman yadda Allah Maɗaukaki Yace: {Abun bautarku abun bauta ɗaya ne, saboda haka duk wanda yake burin saduwa da ubangijinshi sai ya aikata aiki na gari kuma kada yayi tarayya da bautar ubangijinshi da kowa} [Alkahfi: 110].

Sai Allah Ta'ala Ya bada labarin cewa lalle abun bauta guda ɗaya ne, saboda haka baya halatta a riƙi wani abun bauta koma bayan shi kuma ba za a bauta wa wanin shi ba.

{Lalle abun bautarku Shi ne Allah wanda babu wani abun bauta wa da gaskiya sai shi, kuma iliminShi ya yalwaci dukkanin komai} [Ɗaha: 98].

Mahimmancin tauhidin Uluhiyyah:

Mahimmancin tauhidin Uluhiyyah yana bayyana a ɓangarori da dama, daga cikinsu:

1. Shi ne manufar halittar Aljani da mutane

Allah bai halicci Aljan da mutum ba face don su bautata miShi shi kaɗai bashi da abokin tarayya Allah Ta'ala Yace: {Kuma ban halicci Aljani da mutum ba face don su bautata miNi} [Azzariyat: 56].

2. Shi ne manufan aiko da Manzanni da kuma sauƙar da litattafai

Manufan hakan shi ne ƙiran mutane zuwa bautar Allah Shi kaɗai, da kuma kafurcewa duk wani abunda ake bautawa koma bayan Allah, kaman yadda Allah Ta'ala Yace: {Kuma haƙiƙa mun tura Manzo a cikin kowace Al-ummah da cewa ku bauta wa Allah kuma ku nisanci Ɗagutu (Duk wani abun bauta koma bayan Allah} [Alnahl: 36].

3. Shi ne farkon abunda yake wajibi akan mutum

Kamar yadda yazo a wasiyyar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ga Mu'azu Allah Ya kara mishi yarda yayin da ya aike shi zuwa Yaman, yace da shi: "Lalle zaka riski wasu mutane na daga Ahlul kitabi (Yahudu da Nasara). To ya kasance farkon abunda zaka ƙira su zuwa gare shi shi ne bauta wa Allah Mai girma da ɗaukaka" (Bukhari: 1458, Muslim 19].

4. Lalle tauhidin Uluhiyyah shi ne haƙiƙanin ma'anar "La ila illal lahu" (Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah)

Domin kalmar Ilahu ma'anarta shi ne abun bauta, kuma ma'anan "La ila illal lahu": babu abun bautawa a bisa cancanta sai Allah; sai mu bauta mishi shi kaɗai kuma kada mu gudanar da wani nau'i na ibadah ga waninShi.

5. lalle imani da cewa Allah Shi kaɗai ne abun bauta shi ne asalin sakamakon imani da cewa lalle Allah shi kaɗai ne Mahalicci, Mamallaki kuma mai sarrafawa.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa