Ɓangaren yanzu model
Darasi Salloli Mustahabbai
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Kuma an sanya musu wannan sunan ne domin basa rabuwa da sallolin farilla, kuma domin yawanci musulmi yana tabbata akansu.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Babu wani bawa musulmi da zai yiwa Allah sallah raka'a goma sha biyu na nafila ba na farilla ba a cikin kowace rana face Allah Ya gina mishi gida a cikin Aljannah" (Musulmi: 728).
Sunnoni Ratibai su ne:
Kuma an saka mata wannan sunan ne domin adadin raka'o'inta guda ɗaya ne, kuma tana daga cikin mafifitan Sallolin nafila, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ku dinga yin witiri ya ku mutanen Alkur'ani" (Attirmizi: 453, Ibnu Majah: 1170).
Kuma mafificin lokacinshi, shi ne ƙarshen dare, kuma musulmi zai iya sallatan ta a kowana lokaci daga bayan sallar isha har zuwa lokacin fitowan alfijir.
Adadin raka'o'in witiri
Mafi kƙarancin kamala a cikin sallar witiri shi ne ta kasance raka'a uku, sai musulmi ya sallaci raka'a biyu sai yayi sallama, sa'annan sai ya sallaci raka'a ɗaya yayi sallama. kuma anso mishi a cikin raka'ar ƙarshe gabanin ruku'u ko bayanshi da ya ɗaga hannayenshi zuwa kirjinshi sai yayi addu'ar Alƙunutu.
Kuma ita wata sallah ce wacce Allah Ya shar'anta ta idan aka samu fari sai cutarwa ya samu mutane sakamakon ƙarancin ruwan sama, kuma anfiso a sallace ta a sarari da kuma dandali buɗaɗɗu idan har hakan ya samu, kuma ya halatta da a sallace ta a cikin masallaci.
Kuma an shar'anta wa masu sallah da su fito zuwa gare ta suna masu natsuwa masu ƙasƙantar da kai zuwa ga Allah, masu tuba zuwa gare Shi, kuma lalle su kasance sun aiwatar da sababin da zai jawo musu rahamar Allah; Kaman istigfari, da mayar da zalumci zuwa ma'abotanta, da kyautata wa mutane, da makamancinsu.
Siffar sallan roƙon ruwa
Kuma ita ce sallar da aka shar'antawa musulmi yayin da ya himmatu da aikata wani abunda aikata shi yake halal amma kuma bai san da cewa shin akwai alheri a cikinshi ko babu alheri ba.
Yadda ake sallatar ta
Kuma tana daga cikin salloli mustahabbai waɗanda lada mai ɗimbin yawa yazo a cikin bayanin falalarta, kuma mafi ƙarancinta raka'a biyu ne, lokacinta kuma shi ne daga ɗagowan rana bayan fitowanta har zuwa kusa da lokacin zawalinta da kuma shigan lokacin sallar azahar.
Kisfewan wata ko rana wani yanayi ne wanda ya saɓawa al'ada wanda yake faruwa da tafiyan hasken rana ko na wata gaba ɗaya ko wani bangare, kuma ita wata aya ce daga cikin ayoyin Allah wacce take nuna ikonshi da sarautarshi, kuma take faɗakar da mutum take kuma farkar dashi daga rabkananshi domin ya ji tsoron azabar Allah ya kuma tsammaci rahamarShi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Lalle rana da wata ba sa kisfewa domin mutuwar wani daga cikin mutane, sai dai su wasu ayoyi ne daga cikin ayoyin Allah, to idan kuka gansu sai ku tashi kuyi sallah" (Bukhari: 1041).