Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Imani Da Ranar Ƙarshe

Ranar ƙarshe ita ce ranar da Allah Maɗaukaki zai tada mutane daga cikin kaburbura, sa'annan yayi musu hisabi ya saka musu a bisa ayyukansu, kuma imani da shi rukuni ne daga cikin rukunnan imani. A cikin wannan darasin zaka san ababe masu yawa waɗanda suke da alaƙa da wannan rana.

  • Sanin abunda ake nufi da ranar ƙarshe da kuma hikiman samar da ita. 
  • Sanin wasu daga cikin Alamomin tashin alƙiyama
  • Sanin wasu ababen da suke da alaƙa da imani da rarar ƙarshe. 

Ma'anan Imani Da Ranar Ƙarshe

Shi ne gaskata cewa lalle Allah Maɗaukaki zai ta da mutane daga cikin kaburbura, sa'annan yayi musu hisabi ya kuma saka musu a bisa ayyukansu domin mutanen Aljannah su samu wucewa zuwa masauƙinsu, mutanen wuta ma su shiga masauƙinsu. Kuma imani da ranar ƙarshe ɗaya ne daga cikin rukunnan imani guda shida, saboda haka imani baya inganta sai da shi. Allah Maɗaukaki Yace: {Amma sai dai kyakkyawan aiki shi ne wanda yayi imani da Allah, da ranar ƙarshe} (Albakara: 177).

Menene Ranar Ƙarshe?

wata rana da zata zo bayanta. kuma an ambaci wannan rana da sunaye masu yawa a cikin Alkur'ani da Sunnah, ana ƙiranta ranar alƙiyama (Ranar tsayuwa) domin manya-manyan ayyukan da za a tsayar a cikinta, kuma domin mutane zasu tsaya ga ubangijin talikai. Kuma ana ƙiranta da Assa'ah (Lokaci), kuma ana ƙiranta, ranar tantancewa, kuma ana ƙiranta ranar addini; da wasun haka na daga sunayenta.

Me Yasa Alkur'ani Ya Ƙafafa Imani Da Ranar Ƙarshe?

Alkur'ani mai girma ya ƙarfafa imani da ranar ƙarshe, kuma ya ja hankali zuwa gare shi cikin kowana yanayi, kuma ya tabbatar da kasantuwar shi da usulubin larabci daban-daban, kuma ya haɗa imani da shi da imani da Allah Mai girma da ɗaukaka a wurare daban-daban; domin bayanin Mahimmancin shi, kuma domin kada mutane su rafkana daga gare shi, kuma domin su shiryawa ababen da suke cikinshi da imani da kuma kyawawan ayyuka.

Imani da ranar karshe sakamako ne wanda yake lizimtar imani da Allah da kuma adalcinshi, bayanin haka kuma shi ne kaman haka:

Allah baya tabbatar da zalumci kuma baya barin azzalumi ba tare da uƙuba ba, kuma baya barin wanda aka zalumta ba tare da adalci ba, kuma baya barin mai kyautatawa ba tare da lada da sakamako ba, kuma yana baiwa duk wani mai haƙƙi haƙƙinshi, kuma lalle a rayuwar duniya muna ganin wanda zai rayu a bisa zalumci ya mutu a bisa zalumci ba tare da wata uƙuba ba, kuma muna ganin wanda zai rayu a cikin zalumci ya mutu a cikin zalumci ba tare da an karɓa mishi hakkinshi ba, to menene ma'anar cewa lalle Allah bai yarda da zalumci ba? Ma'anar wannan shi ne dole ne akwai wata rayuwa ta daban banda wannan rayuwa da muke cikintan, dole ne akwai wata haɗuwa anan gaba wanda za a sakawa wanda ya kyautata, kuma ayiwa wanda ya munana uƙuba, kuma duk wani mai haƙƙi ya karɓi haƙƙinshi.

Alamomin Tashin Alƙiyama

Yana daga cikin imani da ranar ƙarshe imani da alamomin tashin alƙiyama, kuma su ne wasu ababen da zasu faru gabanin ranar alkiyama, waɗanda suke nuna kusancin zuwanta. kuma alamomin tashin alkiyama sun kasu zuwa kashi biyu:

1- Ƙananan Alamomi

Su ne ababen da zasu faru gabanin ranar alkiyama da lokaci mai tsawo kuma a lokuta mabambanta, daga cikinsu akwai za kaga mutane marasa takalma tsiraru, da makiyaya dabbobi suna tsawaita gine-gine kamar yadda yazo a hadisin Jibrilu alaihis salam: «Sai yace ka bani labari a bisa ranar alkiyama. sai yace: wanda aka tambaya baifi wanda yayi tambayar sani ba, sai yace: Toh ka bani labarin alamominta, sai yace: shi ne yadda kuyanga zata haifi ubangijiyarta, kuma za kaga wasu mutane marasa takalma tsiraru talakawa masu kiwon dabbobi suna tsawaitawa cikin gine-gine» (Muslim: 8).

2- Manya-Manyan Alamomin Tashin Alkiyama

Su ne manya-manyan al'amuran da zasu bayyana a dab da lokacin tashin alkiyama, kuma su ne wasu alamomi guda goma, kamar yadda yazo a cikin hadisi, an karɓo daga Huzaifah Binu Usaid yace: «Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana a gare mu alhali muna tunatar da juna, sai yace: Akan meye kuke tunatar da juna? sai sukace: akan ranar alkiyama. Sai yace: lalle alkiyama ba za ta taɓa tashi ba har sai kunga wasu alamomi guda goma: sai ya ambaci hayaƙi, da Dujjal, da Dabba, da fitowan rana daga mafaɗanta, da zuwan Annabi Isa Ɗan Maryama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Ya'ajuju da Ma'ajuju, da kisfewan rana har sau uku: ɗaya ta gabas ɗaya ta yamma ɗaya kuma a yankin larbawa, daga karshe kuma wuta ta fito daga Yaman ta kora mutane zuwa wurin tashin alkiyamar» (Muslim: 2901).

Menene Imani Da Ranar Ƙarshe Ya Ƙunsa?

Imanin musulmi da ranar ƙarshe ya ƙunshi ababe da yawa, daga cikinsu:

1- Imani da tayar da mutane da kuma tara su:

Kuma shi ne raya matattu daga kaburburansu, da mayar musu da rayukan su zuwa jikkunansu, sai mutane su tashi ga Allah ubangijin talikai, sa'annan sai a tashe su a tara su a wuri guda, suna tsirara babu takalma kuma babu shayi (Kaciya) tamkar yadda aka haife su a karon farko. Kuma imani da tashin mutane daga kaburburansu abu ne wanda Alkur'ani da Sunnah sunyi nuni zuwa gare su, hakama hankali da ingantacciyar fiɗira, zamuyi imani mu kuma sakankance da cewa lalle Allah zai ta da waɗanda suke kwance a cikin kabari, kuma za a mayar da rayuka zuwa ga jikkuna, kuma mutane zasu tashi ga ubangijin talikai.

Allah Maɗaukaki Yace: (Sa'annan lalle ku bayan haka masu mutuwa ne * Sa'annan kuma lalle ku a ranar alkiyama za a tashe ku) (Almuminun: 15- 16). Kuma haƙiƙa dukkanin litattafan sama sun haɗu akan cewa za a tashi mutane bayan mutuwa, kuma wannan hikima ce ta ubangiji; domin ya kamata ace ya sanyawa waɗannan khalifofin na shi a doron ƙasa makoma wanda zai saka musu akan dukkanin ababen da ya kallafa musu a bisa harsunan Manzanninshi, Allah Maɗaukaki Yace: (Shin kuna zaton cewa mun halicce ku domin wargi ne, kuma cewa lalle ku ba zaku dawo zuwa gare mu ba) (Almuminun: 115).

2- Imani Da Hisabi Da Kuma Mizani:

Sai Allah Ya yiwa mutane hisabi a bisa ayyukansu da suka kasance sun aikata su a cikin rayuwar duniya, duk wanda ya kasance daga cikin ma'abota tauhidi kuma mai biyayya ga Allah da Manzonshi, to hisabinshi zai kasance cikin sauƙi, kuma wanda ya kasance daga cikin mutane masu shirka da saɓon Allah, to hisabinshi zaiyi tsauri.

Kuma za a auna ayyuka a cikin wani babban mizani, sai a sanya kyawawan ayyuka a gefen mizanin munanan ayyuka a ɗayan gefen, duk wanda kyawawan ayyukanshi suka rinjayi munanan ayyukanshi to zai kasance daga cikin mutanen Aljannah, kuma duk wanda munanan ayyukanshi suka rinjayi kyawawan ayyukanshi to zai kasance daga cikin mutanen wuta, kuma ubangijinka ba zai zalumci kowa ba. Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma zamu kafa ma'aunin adalci ga ranar alkiyama saboda haka babu wata rai da za a zalumce ta, koda ace tsagun ƙwayan zarra ne sai mun zo da shi kuma mune mukafi kowa iya hisabi) (Al-Anbiya: 47).

3.Aljannah Da Wuta:

Aljannah ita ce gidan tabbatacciyar ni'ima wacce Allah Ya tanadawa Muminai masu tsoron Allah, masu yiwa Allah da Manzonshi biyayya, a cikinta akwai dukkanin nau'in tabbatattun ni'imomi na daga ababen da rayuka suke sha'awa kuma idanuwa suke samun natsuwa dasu, na daga dukkanin nau'in ƴaƴan itace. Allah Maɗaukaki Yace yana mai kwaɗaitar da bayinshi da suyi gaggawa zuwa aikata alheri domin su shiga aljannar da faɗinta tamkar faɗin sama da ƙasa:(Kuyi gaggawa zuwa ga rahama daga ubangijinku da kuma Aljannah wacce faɗinta shi ne sammai da ƙasa, an kuma tanada ta ne ga masu taƙawa) (Ali Imran: 133).

Wuta kuma ita ce gidan tabbatacciyar azaba wacce Allah Ya tanadawa Kafurai waɗanda suka kafurcewa Allah kuma suka saɓawa Manzanninshi, a cikinta akwai nau'i kala-kala na azaba da raɗaɗi da kuma wulaƙanci wanda mutum bai isa ya tuna ba. Allah Maɗaukaki Yace, Yana Mai tsorata bayinshi daga wutar da ya tanadawa Kafurai: (Kuji tsoron wutar da makamashinta shi ne mutane da duwatsu, an tanade ta ne domin Kafurai) (Albakara: 24).

Ya Allah Lalle mu muna roƙonKa Aljannah da abunda zai kusantar zuwa gare ta na daga zance da aiki, kuma muna neman tsarinKa daga wuta da duk wani abunda zai kusantar zuwa gare ta na daga zance da aiki.

4- Azaban Kabari Da Ni'imarshi:

Zamuyi imani da cewa lalle mutuwa gaskiya ce, Allah Maɗaukaki Yace: (Kace Mala'ikan mutuwa wanda aka wakilta shi akanku shi ne mai ɗaukan rayukanku, sa'annan kuma zuwa ubangijinku ne makomarku take) (Assajadah: 11). Kuma wannan lamari ne wanda ake gani babu shakka a cikinshi, kuma muyi imani da cewa duk wani wanda ya mutu ko aka kashe shi, ko wana sababi ne ya zamto dalilin mutuwarshi, to dama lokacinshi ne yayi ba a rage mishi komai daga cikin ajalinshi ba, Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma idan ajalinsu yazo, to ba za a jinkirta shi na wani lokaci ba kuma ba za a gabatar da su ba) (Al-A'araf: 34). Kuma duk wanda ya mutu to lalle Ƙiyamarshi ta tsaya kuma ya wuce zuwa gidan lahira.

Ayoyi masu girma da dama da kuma hadisai masu darajah da yawa sunzo suna tabbatar da azaban kabari ga kafurai da masu aikata zunubi, suna kuma bayyana ni'imar dake cikin kabari ga muminai da mutanen kirki, saboda haka zamuyi imani da shi ba tare ta shishshigin sanin yadda yake ba, domin lalle ƙwaƙwalwa ba za ta iya sanin yadda yake da kuma haƙiƙaninshi ba, domin kasancewan shi abune wanda yake duniyar gaibu kaman Aljannah da wuta, kuma ƙwaƙwalwa zata iya kimanta abunda tasan kwatankwacin shi ne a cikin duniya kawai.

Kaman yadda abunda zai faru a cikin kabari yana daga cikin al'amuran gaibu wadanda mutum ba zai iya gane haƙiƙaninsu ba, da za a iya gane hakan, da an rasa fa'idar imani da gaibu, da kuma hikiman kallafawa ta kau, kuma da ba a binne mutane ba, kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ba don ji muku tsoron kada ku bar binne mutane ba da na roƙi Allah da ya jiyar daku wani ɓangaren azabar kabari" (Muslim: 2868, Annasa'i: 2058). Amma kuma a yayin da wannar hikima ta azabar kabari ta zamto korarriya a haƙƙin dabbobi, sai suka kasance suna jin abunda yake faruwa a cikin kabari, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: (Lalle ana azabtar dasu da azabar da dabbobi suna ji) (Bukhari: 6366: Muslim 586).

Daga Cikin Dalilan Alkur'ani Na Tabbbatar Da Tada Mutane:

Dalilai da dama a cikin Alkur'ani mai girma sun tabbatar da cewa lalle za a tayar da mutane bayan sun mutu, daga cikin waɗannan dalilan:

Lalle Allah Ta'ala shi ne wanda ya ƙirƙiri halittan mutane, kuma wanda yake da ikon ƙirƙiran mutane to sake dawo da su ba zai gagare shi ba, Allah Maɗaukaki Yace: (Kuma shi. ne wanda ya ƙirƙiri halitta sa'anna yake dawo da su) (Alrum: 27). Kuma Allah Maɗaukaki Yace yana mai ba da umarnin yin raddi ga wanda yayi inkarin raya ƙashushuwa bayan sun rigirgije: (Kace wanda ya raya su a karon farko shi ne zai sake raya su, kuma shi masanin kowace halitta ne) (Yasin: 79).

Lalle ƙasa takan kasancewa matacciya babu korayen bishiyoyi akanta, sai ruwan sama ya sauƙo a kanta, sai ta rayu ta zamto koriya akanta akwai kowana irin nau'in tsirrai masu ƙyawatarwa, Wanda yake da ikon rayata bayan mutuwarta lalle babu shakka zai iya tayar da matattu, Allah Maɗaukaki Yace:{Kuma Muka sauƙar da ruwa mai albarkah daga sama sai Muka tsirar da itatunan lambuna da shi da kuma ƙwaya abun girbewa * Da itatuwan dabino dogaye masu ƴaƴa ninki-ninki * Domin su kasance arziki ga mutane, kuma Muka raya matacciyar ƙasa da shi, to kaman hakane fitowa daga kabari ma yake) (Ƙaf: 9- 11).

Duk wani mai hankali yasan cewa lalle duk wanda yake da iko akan gudanar da wani aiki mai girman gaske to wanda bai kai shi girma ba zaifi sauƙi a gare shi, kuma Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya ƙirƙiri halittan sammai da ƙasa, da taurari duk da girman da suke da shi da faɗinsu, da kuma ababen mamakin dake cikinsu, saboda haka lalle shi Mai iko ne a bisa rayar da ƙashushuwa bayan sun rududduge, Allah Maɗaukaki Yace: (Shin Wanda ya halicci sammai da ƙasa ba mai iko bane a bisa halittan kwatankwacin su, hakane lalle shi ne mai yawan halitta mai yawan sani)(Yasin 81).

Amfanin Imani Da Ranar Ƙarshe:

1- Imani da ranar ƙarshe yanada tasiri sosai wajen nitsar na musulmi, da kintsa shi da kuma fiskantar da shi zuwa ga ayyuka na gari da tsoron Allah Mai girma, kuma zai taimaka mishi wajen nisantar munanan halaye da siffofi, saboda hakane imani da ranar ƙarshe yake da alaƙa ta kusa da kyawawan ayyuka a cikin lokuta da yawa, kaman faɗin Allah Ta'ala: (Lalle masu raya masallatan Allah su ne waɗanda sukayi imani da Allah da ranar ƙarshe) (Attaubah: 18). Da kuma faɗinshi: (Kuma waɗanda sukayi imani da lahira masu imani ne da shi, kuma lalle akan sallolinsu su masu kiyayewa ne) (Al-An'am: 92).

2- Ankarar da rafkanannu waɗanda suka shagaltu da al'amuran duniya da jin daɗinta suka bar tsere zuwa biyayya ga Allah da ribatan lokaci wajen samun kusanci ga Allah zuwa fahimtar haƙiƙanin rayuwar duniya da gajartanta, da kuma cewa lalle lahira ita ce matabbata da wurin dawwama. kuma a yayin da Allah Ya yabawa Manzanni a cikin Alkur'ani mai girma Ya kuma ambaci ayyukansu, sai ya jinjina musu da sababin da yake kaisu zuwa aikata waɗannan ayyukan, Allah Ta'ala Yace: Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsatstsarkar aba: Hukunce- hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira) (Sad: 46). Ma'ana lalle sababin waɗancan ayyukan masu falalan shi ne kasancewansu sun keɓanta da yawan tuna gidan lahira.

Kuma a lokacin da wasu musulmai suka samu rauni wajen bin umarnin Allah da na Manzonshi, sai Allah Ta'ala Yace Yana mai ankarar dasu: (Shin kun yarda da rayuwar duniya ce akan ta lahira, toh jin daɗin rayuwar duniya a lahira ɗan kaɗan ne) (Attaubah: 38). Saboda haka, a duk lokacin da mutum yayi imani da ranar lahira, to babu shakka zai tabbatar da cewa lalle ni'imar lahira ba a ƙiyastata da ta duniya, kuma ba zai kai nitso ɗaya cikin azabar Allah ba, kuma dukkanin azabar duniya -A tafarkin Allah- ba zai taɓa kai azabar lahira ba, kuma ba zai kai tsomi guda cikin rahamar Allah ba.

3- Samun natsuwar cewa lalle haƙƙin mutum ba zai taɓa lalacewa ba; saboda haka duk wani wanda aka karɓan mar wani abu koda kaman ƙwayan zarra ne ba tare da haƙƙi ba, toh lalle babu shakka zai same shi a ranar alkiyama, kuma a lokacin ne yake matiƙar buƙatuwa zuwa gare shi, to ta yaya wanda yasan cewa lalle haƙƙinshi zai same shi babu makawa a lokacin da yake matiƙar buƙatanshi zai samu damuwa? kuma ta yaya wanda yasan cewa lalle wanda zaiyi hukunci a tsakaninshi da abokin faɗanshi shi ne wanda yafi kowa iya hukunce zaiyi baƙin ciki?

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa