Ɓangaren yanzu model
Darasi Azumin watan Ramadan
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Allah Ya farlantawa musulmai azumin wata guda a cikin shekara, kuma wannan watar ita ce watan Ramadan mai albarkah, kuma Ya sanya shi rukuni na huɗu ne daga cikin rukunnan musulunci da kuma ginshiƙun shi masu girma, Allah Ta'ala Yace: (Ya ku waɗanda sukayi imani an farlanta muku azumi kaman yadda aka farlantawa Waɗanda suka rigaye ku domin kuji tsoron Allah) (Albakara: 183).
Ma'anar azumi a musulunci shi ne bautatawa Allah da kamewa da kuma barin ci da sha da jima'i da dukkanin sauran ababen da suke lalata azumi daga ketowan alfijir ɗin gaskiya -kuma shi ne lokacin shigan sallar asubahi - har zuwa faɗuwan rana, kuma shi ne lokacin shigan sallar Magariba.
Falalar watan Ramadan
Allah Ta'ala Yace: (Watan Ramadan shi ne wanda aka sauƙar da Alkur'ani a cikinshi domin ya zamto shiriya ga mutane da kuma bayyana ababen shiriya da rarrabewa, saboda haka, duk wanda ya riski watan Ramadan a cikinku to ya azumce shi) (Albakara: 185).
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Idan watan Ramadan ya shiga sai a buɗe ƙofofin Aljannah, a kuma kulle ƙofofin Jahannama, kuma a ɗaure shaidanu" (Bukhari: 3277,Muslim: 1079). Haƙiƙa Allah Ya shiryawa bayinShi fiskantar wannan wata da aikata kyawawan ayyuka da kuma barin munanan ayyuka.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ya sallaci watan Ramadan yana mai imani da kuma neman lada, an gafarta mishi abunda ya gabatar na daga zunubanshi" (Bukhari: 2009,Muslim: 759).
Kuma shi ne daren da Allah Ya bada labari a cikin littafinShi cewa lalle aikin alheri a cikinshi yafi aiki a cikin watanni dubu. Allah Ta'ala Yace: Daren lailatul ƙadari yafi alheri fiye da watanni dubu) (Alkadar: 3), Kuma shi dare ne wanda ba a ayyana shi ba sai dai yana daga cikin goman ƙarshe na daga watan Ramadan, duk wanda ya sallace shi yana mai imani da kuma neman lada an gafarta mishi abunda ya gabatar na daga zunubanshi.
Falalar Azumi
1. Gafarta Zunubbai
Kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mai azumi yana da farin ciki guda biyu: Farin ciki yayin buɗa bakinshi, da kuma farin ciki yayin saduwa da Ubangijinshi" (Bukhari: 1904,Muslim: 1151).
3. A cikin Aljannah Akwai wata ƙofar da ake cewa da ita Ar-Rayyan babu wanda zai shiga ta cikinta sai masu azumi.
4. Lalle Allah Ya danganta sakamakon azumi da ladanshi zuwa gare Shi
Hikimar dake cikin Azumi
Domin azumi ibada ne wanda bawa yake samun kusanci zuwa ga Allah dashi, ta hanyan barin ababen da yakeso, da daƙile sha'awarshi wacce take halal, domin bin umarnin Ubangijinshi da kuma gujewa saɓa miShi.
Domin ƙauracewa ababen da suke halal da mai azumi yayi domin bin umarnin Allah Ta'ala zai taimaka mishi wajen danne sha'awarshi ga barin aikin zunubi.
Domin lalle a cikin azumi akwai yanayin tunawa da marasa hali da kuma jin yunwa, wanda hakan zai sa a tuna da talakawa waɗanda suke fama da talauci a rayuwarsu, sai bawa ya tuna da ƴan uwanshi talakawa da yadda suka kasance suna wahala daga yunwa da kuwa ƙishirwa, sai yayi ƙoƙari wajen taimaka musu da kuma agaza musu.