Ɓangaren yanzu model
Darasi Hukunce-hukunce da kuma ladduban karanta Alkur'ani
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ladduban Karatun Alkur'ani Mai Girma
Hukuncin Haddace Alkur'ani
Daga Aisha Allah Ya kara mata yarda, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Misalin wanda yake karanta Alkur'ani alhali ya gwanance a cikinshi yana tare da manyan mala'iku» [Bukhari: 4937].
Hukuncin Tilawar Alkur'ani Mai Girma
Hukuncin Sauraro Da kuma Natsuwa Yayin Karatun Alkur'ani
Wajibi ne akan kowa da yayi imani da Alkur'ani mai girma, kuma yayi aiki da hukunce-hukuncen shi, ya halalta halalinshi, ya haramta haram ɗinshi, ya tsaya a wurin haninshi, kuma ya aikata ababen da yayi umarni da su.
Ya kamata akan kowana musulmi da ya nace akan karatun Alkur'ani, kuma bai kamata ace wata rana ta wuce ba tare da ya karanta wani ɓangare na Alkur'ani ba, domin kada ya manta shi ko kuma ya ƙaurace mishi, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma Manzon yace ya ubangiji haƙiƙa mutane na sun ɗauki wannan Alkur'anin abun ƙauracewa} [Alfurƙan: 30].
Daga Abu Musa Allah Ya kara mishi yarda, daga Annabi (S. A. W) yace: Kuyi riƙo da wannan Alkur'anin, domin na rantse da wanda rai na yake hannunshi yafi rakumi a akalanshi saurin kuɓucewa» [Bukhari: 5033].