Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Ababen da suke lalata Azumi

Akwai ababe da dama waɗanda idan suka faru da mai Azumi na miji ko ta mace sun lalata musu azuminsu. A cikin wannan darasin zaka san waɗannan ababen.

Sanin nau'in ababen da suke karya Azumi

Ababen da suke karya Azumi

Su ne ababen da ya wajaba akan mai azumi da ya kame daga gare su domin lalle zasu lalata mishi azumi

1. Ci da Sha

Allah Ta'ala Yace: (Kuma ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana daga baƙin zare na daga alfijir a gare ku, sa'annan sai ku cika azumi zuwa dare) (Albakara: 187).

Duk wanda ya ci ko ya sha a bisa mantuwa, to azuminshi ingantacce ne babu laifi akanshi, Kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ya manta cewa yana azumi sai ya ci ko ya sha to ya cika azuminshi domin lalle Allah ne Ya ciyar da shi Ya kuma sahayar dashi" (Bukhari: 1933, Muslim: 1155).

2. Abunda yake matsayin ci ko sha

١
Kaman Allurar abinci wacce take isa zuwa jiki domin ta sama mishi abunda ya rasa na daga gishiri da abinci, domin lalle shi yana matsayin abinci da abun sha ne, daga nan sai a bashi hukuncinsu.
٢
Allurar jini ga mara lafiya; Domin jini shi ke ciyar da jiki, saboda haka wannan alluran ma zai ɗauki hukuncin abinci.
٣
Hayaƙi (Shaye-shaye) da dukkanin nau'ukanshi, lalle yana karya azumi; domin yana isa zuwa cikin mutum tamkar abinci da abun sha.

3. Jima'i da shigar da kan azzakari a cikin farjin mace, sawa'an Maniyyi ya fita ko bai fita ba.

4. Fitar da maniyyi da gangan; da shafan mace ko da wasa da Al'aura, da makamancin haka.

Amma kuma mafarkin da yake kasancewa a cikin bacci baya lalata azumi, kuma ya halatta ga mutum da ya sumbanci matarsa idan har zai iya kame kanshi daga abka mata, amma kuma idan har ba zai iya kame kanshi ba to hakan bai halatta a gare shi ba domin tsoron kada ya lalata azuminshi.

5. Janyo Amai da gangan

Amma kuma wanda yayi Amai ba da gangan ba to babu laifi a gare shi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda Amai ya fito mishi ba tare da zaɓinshi ba alhalin kuma yana azumi, to babu komai akanshi, amma idan shi ya janyo Aman ɗin to ya biya wannan azumin" (Attirmizi: 720, Abu Dawood: 2380).

6. Fitan Jinin Haila Da Na Biki

A duk lokacin da aka samu jinin haila ko na biki, a wani ɓangare na rana to azumin mace ya lalace, idan kuma ta kasance mai haila ce sai ta tsarkaka bayan ketowan alfijir, to azuminta na wannan ranan ba zai inganta ba, saboda faɗin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Shin bakuga cewa idan tayi haila bata sallah kuma bata azumi ba?" (Bukhari: 1951).

Amma kuma jinin da yake fita daga mace sakamakon rashin lafiya, kuma shi ne wanda ba hailan da ta saba na wasu kwanaki a cikin wata ba kuma ba jinin biki wanda yake fitowa bayan haihuwa ba, to wannan jini ba ya hana azumi.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa