Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Shaidawa lalle Annabi Muhammadu Manzon Allah ne

Shaidawa lalle Annabi Muhammadu Manzon Allah ne shi ne ɓangare na biyu na daga shahada biyu (Shahadataini), a wannan darasin zaka san ma'anarta da kuma ababen da take buƙata.

Sanin ma'anar shaidawa lalle Annabi Muhammadu Manzon Allah ne 

Ma'anar shaidawa lalle Annabi Muhammadu Manzokn Allah ne

Shi ne gaskanta labaranshi da bin umarninshi da nisanta haninshi, kuma mu bautawa Allah kamar yadda Manzon Allah (S. A. W) ya shar'anta ya kuma koya mana. Kuma hakan ya ƙunshi ababe masu zuwa:

1- Gaskata labaran da ya labarta a cikin dukkanin ɓangarori, daga cikinsu akwai:

١
Al'amuran gaibu da na ranan lahira, da Aljannah da ni'imarta, da wuta da azabarta.
٢
Ababen da zasu faru a ranan alkiyama da alamominta, da kuma ababen da zasu faru a ƙarshen zamani.
٣
Labaran mutanen farko da na magabata, da kuma ababen da suka faru a tsakanin Annabawa alaihimus Salam da mutanensu.

2 - Bin umarninshi da nisanta haninshi, kuma hakan ya haɗa da:

١
Aikata abunda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare ya umarce mu da shi na daga ibadah, da kyawawan ayyuka, da kuma ɗabi'u na gari,
٢
Nisantara ababen da ya hana na haramun, na daga munanan halaye, da ɗabi'u masu cutarwa, da kuma yin imani da cewa lalle hanamu waɗannan ababe da yayi akwai hikiman da Allah Yake nufi a cikinshi, kuma domin maslaharmu ne, duk da cewa ba lalle mu gane wannan hikimar ba a wasu lokutan.
٣
Sakankancewar mu da cewa baya faɗin son zuciyarsa saidai wahayi daga Allah Mai girma da ɗaukaka, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: {Duk wanda yayiwa Manzon Allah biyayya toh haƙiƙa yayiwa Allah biyayya} [Anisa'i: 80].
٤
Imaninmu da cewa duk wanda ya saɓawa umarnin Annabi (S. A. W) lalle ya cancanci azaba mai raɗaɗi, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: {To waɗanda suke saɓawa umarninshi su kiyaye, domin fitina zata iya samunsu ko azaba mai raɗaɗi} [Alnur: 63].

3- Ba zamu bautawa Allah ba sai da abunda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shar'anta mana, kuma hakan ya ƙunshi ababe da yawa waɗanda ya wajaba a tabbatar da su:

Koikoyonshi (S. A. W)

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne abun koyin mu, kuma mutum zai samu kusanci da Allah kuma darajarshi zata ƙaru a duk lokacin da ya kasance yana bin shiriyarshi da kuma sunnarshi; da dukkanin ababan dake cikinta na zantuka, da ayyuka, da yarda, da tabbatarwa. Allah Ta'ala Yace: {Kace idan har kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah Ya soku, ya kuma gafarta muku zunubanku, kuma Allah Mai yawan gafara ne Mai jin ƙai} [Ali Imran: 31].

Cikakkiyar Shari'a

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya isar da addini da kuma shari'a a cike ba tare da wata tawaya ba, saboda haka baya halatta ga wani da ya ƙago wata ibadar da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai shar'anta mana ita ba.

Shari'ar Allah Daidai Take Da kowace Zamani Da Kuma Lokaci

Hukunce-hukuncen addini da na shari'a waɗanda sukazo a cikin littafin Allah da sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun dace da kowana zamani da lokaci, saboda babu wanda yafi sanin abunda zai amfanar da mutane fiye da wanda ya halicce su ya kuma samar da su daga babu.

Dacewa Da Sunnah

Daga cikin sharruɗan karɓan ibadah akwai tsarkake su ga Allah Shi kaɗai, kuma ibadar ta kasance tamkar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya shar'anta mana, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: {kuma duk wanda yake burin saduwa da ubangijinshi to ya aikata aiki na ƙwarai kuma kada yayi shirka a cikin bautar ubangijinshi da kowa) [Alkahfi: 110]. Ma'anar (Na ƙwarai) shi ne daidai wanda kuma ya dace da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Haramcin Ƙago Ibadah

Duk wanda ya ƙirƙiro wata ibadar da bata cikin sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma yana nufin bautawa Allah da ita, kaman wanda zai ƙirƙiri wata sallah ba ta hanyar da shari'a ta koyar ba; to babu shakka ya saɓawa umarnin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yayi zunubi da wannan aikin, kuma an mayar mishi da aikinshi. Allah Ta'ala Yace: {To waɗanda suke saɓawa umarninshi su kiyaye, domin fitina zata iya samunsu ko azaba mai raɗaɗi} [Alnur: 63], kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Duk wanda ya ƙirƙiri wani abu a cikin wannan lamarin namu wanda baya daga cikinshi to an mayar mishi" [Bukhari: 2697, Muslim: 1718]

Soyayyarshi (S. A. W)

Daga cikin ababen da suke wajibi a cikin imani da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne cewa lalle Allah da manzonshi su kasance sunfi soyuwa zuwa ga mumini fiye da komai, kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai na kasance nafi soyuwa a gare shi fiye da mahaifinshi, da ɗanshi da kuma dukkanin mutane" [Bukhari: 15, Muslim: 44].

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa