Ɓangaren yanzu model
Darasi Imani Da Annabi Muhammadu Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata A Gare Shi
Akwai ababe da dama waɗanda suka wajaba akanmu dangane da Annabinmu Muhammadu (S. A. W), daga cikinsu:
1- Zamuyi imani da cewa lalle Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bawan Allah ne kuma Manzonshi ne, kuma lalle shi ne shugaban mutanen farko da na ƙarshe, kuma shi ne cikamakin Annabawa babu wani annabin da zai zo a bayanshi, kuma haƙiƙa ya isar da aike, ya cika amana, yayiwa Al-ummah nasiha, kuma yayi matiƙar ƙoƙari a addinin Allah
2- Kuma mu gaskata shi cikin abunda ya bada labari, muyi mishi biyayya cikin abunda yayi umarni, mu nisanci abunda ya hana ya kuma tsawata, kuma mu bautawa Allah a bisa sunnarshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, muyi koyi dashi shi kaɗai, Allah Ta'ala Yace: {Lalle abun koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatar rahamar Allah da ranar lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa} [Al-Ahzab: 21].
3- Kuma ya wajaba a garemu da mu gabatar da soyayyar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi akan soyayyar mahaifi, da ɗa, da dukkanin mutane, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yace: "Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai na kasance mafi soyuwa a gare shi fiye da mahaifin shi, da ɗanshi da kuma mutane baki ɗaya" (Bukhari: 15, Muslim: 44). kuma haƙiƙanin son shi yana kasancewa ne da bin sunnarshi, da bibiyan shiriyarshi. kuma ba a samun asalin jin daɗi da haƙiƙanin shiriya sai dai da yi mishi biyayya, kaman yadda Allah Yace: {Kuma idan kukayi mishi biyayya zaku shiryu, kuma babu abunda yake kan Manzo face isarwa bayyananne} [Alnur: 54].
4- Ya wajaba a gare mu da mu karɓi abunda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yazo mana dashi, kuma mu bibiyi sunnarshi, kuma mu girmama shiriyarshi mu kuma karrama ta, kamar yadda Allah Maɗaukaki Yace:{Na rantse da ubanginka ba za za suyi imani har sai sun sanya ka mai hukunci a cikin abunda ya wakana a tsakaninsu, sa'annan ba zasu samu wata damuwa a cikin rayukansu dangane da hukuncin da ka yanke ba, kuma su miƙa wuya miƙawa} [Annisa'i: 65].
5- Ya kamata mu nisanci saɓawa umarninshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin saɓawa umarninshi sababi ne na fitina da ɓata da azaba mai raɗaɗi, Allah Maɗaukaki Yace:{Ton wadanda suke saɓawa umarninshi su kiyaye domin kada fitina ta same su ko azaba mai raɗaɗi} [Alnur: 63].
Manzancin Annabi Muhammadu ya banbanta da saƙonnin da suka rigaye shi da ababe masu yawa, daga cikinsu.
1. Manzancin Annabi Muhammadu shi ne cikamakin dukkanin manzancin da suka gabata, Allah Maɗaukaki Yace:{Muhammadu bai kasance mahaifin wani daga cikinku ba, sai dai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa} [Al-Ahzab: 40].
2- Manzancin Annabi Muhammadu ya shafe dukkanin shari'un da suka gabata, saboda haka Allah ba zai karɓi addini daga wani ba bayan aiko shi sai dai idan ya bi shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma babu wanda zai isa zuwa ni'imar Aljannah sai ta hanyar shi, saboda haka shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mafi darajan Annabawa, Al-ummarshi kuma ita ce mafi alherin Al-ummu, shari'arshi kuma ita ce mafi cikan shari'a, Allah Maɗaukaki Yace:{Duk wanda ya riƙi wani abu koma bayan musulunci a matsayin addini, toh ba za a karɓa daga gare shi kuma lalle shi a lahira yana daga cikin asararru} [Ali Imran: 85]. Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Na rantse da wanda rai na yake hannunshi, babu wani wanda zaiji labarina a cikin wannan Al-ummar, bayahude ne ko banasare, sa'annan ya mutu ba tare da yayi imani da ni ba face ya kasance daga cikin ƴan wuta" (Muslim: 153, Ahmad: 8609)
3- Annabi Muhammadu an aiko shi ne zuwa ga dukkanin mutane da aljanu, Allah Maɗaukaki Yace Yana mai hakaito zancen Aljanu:{Ya ku Al-ummar mu ku amsawa mai ƙira zuwa ga Allah} (Al-Ahƙaf: 31). Kuma Allah Maɗaukaki Yace:{Bamu aiko ka ba face ga dukkanin mutane, kana mai bishara kuma kana mai gargaɗi}[Saba'i: 28]. Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "an fifita ni a bisa sauran Annabawa da ababe guda shida: An ba ni suratul fatiha, an bani nasara yayin firgici, kuma an halasta mini ganima, kuma an sanya mini ƙasa ta zamto masallaci mai tsarki, kuma an aiko ni zuwa ga dukkanin mutane, kuma ni ne cikamakin Annabawa" (Bukhari: 2977, Muslim: 523).
Allah bai aiko wani Annabi ba face sahabbanshi da mataimakanshi sun kasance sune mafi alherin mabiyanshi, kuma ƙarninsu zai kasance mafi darajan ƙarnin Al-ummarshi. Allah Maɗaukaki Ya zaɓawa Annabinshi mafi alherin mutanen bayan Annabawa da Manzanni da su zamto sahabbanshi, domin su ɗauki wannan addinin kuma su isar dashi zuwa ga mutane yana tsarkakakke kuma tsabtatacce, kaman yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Mafi alherin Al-ummata su ne ƙarnin da aka aiko ni a cikinsu, sa'annan sai waɗanda suka biyo su» (Muslim: 2534).
Ma'anan Sahabi
Sahabi: Shi ne wanda ya haɗu da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana musulmi kuma ya mutu a bisa haka, ba tare da kasancewa yayi ridda bayan rasuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba.
Yabo ya zowa sahabban Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, hakama an bayyana siffofinsu da falalansu a wurare da yawa a cikin littafin Allah da kuma sunnar manzonshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga cikin hakan:
Abunda Yake Wajibi Akanmu Dangane Da Sahabbai
Akwai ababe da yawa waɗanda suka wajaba akanmu dangane da sahabbai, daga cikinsu:
1- Son su da girmama su da kuma yi musu Addu'a:
Hakiki Allah Ya yabawa Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyarsu a Makkah sukayi hijirah zuwa Madinah domin kuɓuta da addininsu, da kuma neman yardan Allah, haka kuma Allah Ya yabawa Ansar Mutanen Madinah waɗanda suka taimakawa ƴan uwansu, kuma sukayi tarayya dasu cikin abunda ke hannunsu na daga dukiya da kayan duniya, harma suka gabatar da ƴan uwansun a bisa kawunansu, sa'annan sai Allah Ya yabawa waɗanda zasu zo a bayansu har zuwa ranan alkiyama daga cikin waɗanda zasu san falalan sahabbai da matsayinsu su kuma so su, suyi musu Addu'a, kuma ba zasu ƙuntacesu a cikin zuciyarsu ba.
Allah Madaukaki Yace: {(Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da ManzonSa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya. Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu, sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo. Kuma waɗanda suka zõ daga bãyansu, sunã cẽwa, «Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai.}[Al-Hashri- 8-10].
2- Nemawa dukkanin sahabbai yardan Allah:
Ya kamaci musulmi idan ya ambaci ɗaya daga cikin sahabbai da yace:(Allah Ya kara mishi yarda), haƙiƙa Allah Ya bada labarin cewa lalle Ya yarda dasu kuma Ya karɓi kyawawan ayyukansu, kuma su ma sun yarda da shi da abunda Ya basu na daga ni'imar duniya da na addini, Allah Ta'ala Yace:{Kuma da magabatan farko na daga muhajirai (Mutanen Makkah) da Ansar (Mutanen Madinah), da kuma waɗanda suka biyo su da kyautatawa, Allah Ya yarda dasu su ma sun yarda da shi, kuma ya tanada musu Aljannah wacce ƙoramai suke gudanawa a ƙarƙashinta, suna masu tabbata a cikinta har abada, wannan shi ne babban rabo} [Attaubah: 100].
Matsayin Sahabbai:
1- Sahabban Manzon Allah dukkanin su ma'abota falala da kyautatawa ne, amma kuma mafi falala daga cikinsu su ne Khalifofi shiryayyu guda huɗu, su ne a jere: Abubakar As-siddik, Umar Binul Khaɗɗab, Usman Bin Affan, Aliyu Bin Abi ɗalib Allah Ya kara musu yadda baki ɗaya.
2- Sahabban Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi mutane ne ba ma'asumai ba ne kuma suna iya faɗawa cikin kuskure, amma kuma kusakuran su ba zai ka irin na wasunsu ba, kuma daidai ɗinsu yafi na waninsu yawa, domin haƙiƙa Allah Ya zaɓawa Annabinshi mafi alherin mutane domin ɗaukan wannan addinin: «Mafi alherin Al-ummata su ne wadanda aka aiko ni a cikinsu sai waɗanda suka biyo su» (Muslim: 2534).
3- Mu shaida cewa dukkanin sahabbai Adilai ne kuma masu kyautatawa ne, mu dinga ambaton kyawawan ayyukansu kuma kada mu kutsa cikin mutuncinsu da kuma ababen da sukayi na kura-kurai ko ijtihadin da ya saɓawa daidai. Domin suna da ƙarfin imani, da kyawawan ayyuka da kuma biyayyan da zai hana wani kuskure da gangan ya zo daga gare su, kaman yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Kada ku zagi sahabbai na, da ace ɗayanku zai ciyar da misalin uhud na zinari ba zai kai mudu ɗayansu ko kwatanshi ba" (Bukhari: 3673).
Mutanen gidan Annabi su ne matanshi da yaranshi da kuma makusantanshi na daga ƴaƴan baffaninshi: Ãli Ali, da Ãli Aƙil, da Ãli Ja'afar, da Ãlil Abbas da kuma zurriyansu.
Kuma mafifici daga cikinsu shi ne wanda ya riski Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kamar Aliyu Binu Abi Ɗalib, da Faɗimatu Ƴar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma ƴaƴansu biyu: Alhasan da Alhusaini shuwagabannin matasan gidan Aljannah, da kuma matan Manzon Allah uwayen muminai; kaman Khadijah, da Aisha As-siddiƙah Allah Ya kara musu yadda gaba ɗaya.
Kuma haƙiƙa Allah Maɗaukaki Yace dangane da matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bayan fiskantar daau zuwa mafifitan ladduba da kyawawan hakaye:(Lalle Allah Yana so ya gusar muku da ƙazanta ne yaku mutanen gidan Annabi Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa) (Al-Ahzab:
Son Mutanen Gidan Annabi
yana daga cikin son Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Annabi (S. A. W) yace yana mai wasiyya da kulawa da mutanen gidanshi da kuma kyautata halaye tare dasu: "Ina tunatar daku da Allah game da mutanen gida na, Ina tunatar daku da Allah game da mutanen gida na" (Muslim: 2408). Kamar yadda mahaifin da yake tausayawa yaranshi zai ce: Na haɗaku da Allah akan haƙƙin yarana.
Kuma ya kamata musulmi ya barranta kanshi da mutane Nau'i biyu:
Iyalan Annabi Ba Ma'asumai Bane:
Iyalan Annabi tamkar wasunsu na daga mutane suke, a cikinsu akwai musulmi da kafuri, da na gari da mai saɓo, saboda haka zamu so na kirki daga cikinsu kuma muyi mishi fatan alheri, kuma zamu guji mai saɓo daga cikinsu muyi mishi fatan shiriya. kuma falalan Ãlul baiti baya nufin fifita su a cikin kowana yanayi, ko fifita su a bisa dukkanin mutane, domin ana fifita mutane ne ta hanyan la'akari da ababe da dama, saboda haka za a iyan samun wanda ya fisu falala ba daga cikinsu ba.