Ɓangaren yanzu model
Darasi Alwala
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Falalan Alwala
Ta yaya zanyi alwala domin kawar da ƙaramin kari?
Anniyyah
Anaso ya wanke tafin hannunshi har sau uku
Zai kuskura ruwa a cikin bakinshi, ma'ana ya sanya ruwa a cikin bakinshi ya mommotsa shi daga ciki sa'annan sai ya fitar da shi, kuma anso mishi da ya aikata hakan har sau uku, amma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya.
Zai shaƙa ruwa: Ma'ana zai ja ruwa da hancinshi, sai ya face: ma'ana ya turo ruwan zuwa waje tare da iskan da yake fitowa daga hanci, kuma anso da ya kai maƙura wajen aikata hakan sai dai idan yaji tsoron cutarwa, ko ya kasance yana azumi, kuma anso ya maimaita hakan har sau uku, amma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya.
Zai wanke fuskarshi, kuma shi ne daga saman goshi wurin matsiran gashi har zuwa ƙarƙashin haɓa, kuma daga kunne har zuwa kunne, amma kuma kunnuwa basa daga cikin fuska, kuma anso da ya maimaita hakan har sau uku, amma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya.
Zai wanke hannayen shi biyu daga kan yatsu har zuwa gwiwar hannu, kuma gwiwan hannu shi ne abunda yake haɗe tsakanin zira'i da cinyar hannu, kuma gwiwan hannu yana daga cikin abunda za a wanke, kuma anso mishi da ya fara da hannun dama, ya kuma maimaita wankewa har sau uku, amma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya
Zai shafi kanshi, ya jiƙa hannunshi da ruwa sa'annan sai ya shafi kanshi daga farkon kan har zuwa ƙarshen shi wato sama da wuya ta baya, kuma anso da ya dawo da hannunshi yana mai shafa kanshi zuwa inda ya fara, kuma ba a so ya maimaita hakan har sau uku kamar yadda yayi a sauran gaɓoɓin jiki, sai dai zai shafa kai ne sau ɗaya kawai.
Zai shafi kunnuwan shi ta yadda zai sanya wani ɓangaren yatsunshi biyu a cikin kunnenshi sai ya shafi zahirin kunnuwan da su.
Zai wanke sawayenshi biyu tare da idon sawu, idon sawu su ne ƙashushuwan da suka tsiro a gefen sahu a daidai wurin da ƙafa da diga-digai suke haɗuwa, zai fara ne da dama, kuma anso da ya maimaita wankewa har sau uku, amma kuma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya, idan kuma ya kasance yana sanye da safa ne to ya halatta da yayi shafa akansu tare da wasu sharruɗa.