Ɓangaren yanzu model
Darasi Imani Da Mala'iku
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ma'anar imani da Mala'ika:
Mahimmancin Imani Da Mala'iku
Imani da mala'iku wajibi ne akan dukkanin musulmi, kuma duk wanda ya kafurce musu haƙiƙa ya ɓata, kuma ya zame, Allah Maɗaukaki Yace:{Kuma duk wanda ya kafurcewa Allah, da mala'ikunshi, da litattafanshi, da manzanninshi, da ranar ƙarshe, toh haƙiƙa ya ɓata ɓata mai nisa} [Annisa'i: 136] sai Allah Ya mayar da wanda yayi inkarin waɗannan rukunnan kafuri a cikin wannan ayar.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin cewa sama tayi nauyi da waɗanda suke cikinta, babu wurin sanya tafin hannu face akwai mala'ika yana tsaye, ko yana ruku'u, ko yana sujjada
Menene Imani Da Mala'ika ya ƙunsa?
Daga cikin siffofin mala'ikun da zamuyi imani da su
Allah Ya kallafawa mala'iku ayyuka masu yawa, daga cikinsu:
Da yawa zamuyi mamakin yadda mutum ya tsira daga wani hatsarin da ya kusa faruwa da shi, saidai ya wajaba akanmu kada mu manta cewa lalle kare ɗan Adam daga ababen da zasu hallaka shi da umarnin Allah yana daga cikin ayyukan mala'iku