Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Imani Da Sunayen Allah Da Kuma SiffofinShi

Sanin Allah Mai girma da ɗaukaka da sunayenShi kyawawa da siffofinShi maɗaukaka, da kuma bauta wa Allah da ababen da suke nuni zuwa gare su, yana daga cikin manya-manyan ababen da suke ƙara imani. A cikin wannan darasin zaka san wasu daga cikinsu.

  • Sanin Tauhidin sunaye da siffofi
  • Sanin Aƙidar Ahlus Sunnah wal jama'a dangane da sunayen Allah da siffofinShi 
  • Sanin ma'anan wasu daga cikin sunayen Allah Mai girma da ɗaukaka 

Imani da sunayen Allah da kuma siffofinShi

Alkur'ani yayi matiƙan ƙarfafa alaƙar dake tsakanin bayi da Allah Ubangijinsu kuma Mahaliccinsu, kuma ya maimaita hakan a cikin ayoyi da dama; domin babu makawa dole ne sai bawa yasan waye ubangijinshi da kyawawan sunayenShi da kyawawan siffofinShi maɗaukaka waɗanda ya siffantu da su, domin ya bauta wa Allah a bisa basirah kuma yayi amfani da ma'anonin waɗannan sunayen da siffofin da kuma tasirin da suke da shi, a cikin rayuwarshi da kuma ibadarshi.

Saboda hakane musulmi zaiyi imani da abunda Allah ya tabbatarwa kanShi a cikin littafinShi ko a cikin sunnar ManzonShi (S. A. W) na daga sunaye da siffofi a bisa fiskar da ta dace da Allah Maɗaukakin Sarki.

Kuma Allah subhanahu wa ta'ala Yana da kyawawan sunaye da cikakkun siffofi, kuma bai da kwatankwaci a cikin sunayenShi da siffofinShi. Allah Ta'ala Yace {Wani abu bai zamto tamkar shi ba, kuma shi mai ji ne mai gani} [Alshura: 11]. Saboda haka Allah Maɗaukaki ya tsarkaka daga kama da wani daga cikin halittunshi a cikin dukkanin sunayenShi da siffofinShi.

(Kace ku ƙira Allah ko ku ƙira Arrahman (Mai rahama), duk wanda kuka ƙira daga cikinsu to shi Yana da kyawawan sunaye) [Al-Isra'i: 110]

Anan ne zamu bijiro da wasu daga cikin sunayen Allah Maɗaukakin Sarki

Arrahmanu Arrahimu (Mai rahama, Mai jin ƙai)

Waɗannan sunaye guda biyu da su ne Allah Ya buɗe fatihar littafinShi, kuma da su ne Allah Ya fara sanarwa bayinShi kanShi, kuma da su ne aka buɗe dukkanin surorin Alkur'ani mai girma a cikin faɗinShi: (Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai), banda suratut Taubah.

Kuma haƙiƙa ubangijinmu mai falala ne a yayin da Ya rubuta wa kanShi rahama, kuma Shi rahamarShi ta yalwaci komai da kowa, har ma rahamar dake tsakanin halittu sashinsu a bisa sashi, da rahamar da mahaifiya take da shi a bisa ɗanta, da kuma sauƙaƙewa halittu hanyar cin abinci, wannan ba komai bane face wani ɗan ƙaramin ɓangare daga cikin rahamar Allah akan halittunShi, kaman yadda Allah Yace: {Ka duba alamomin rahamar Allah yadda yake raya ƙasa bayan mutuwarta} [Rum: 50].

An karɓo daga Umar Ɗan Khaɗɗabi Allah Ya kara mishi yarda: «An kawowa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bayi, sai ga wata mata a cikinsu tana tatsan nononta tana shayarwa, idan taga wani jariri a cikin bayin sai ta ɗauke shi ta manna shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace mana: shin kuna ganin cewa wannan matar zata iya jefa ɗan cikinta a wuta? sai mu kace: A'a, alhalin kuma zata iya barinshi, sai yace: Na rantse Allah Yafi jin tausayin bayinShi fiye da wannan matar ga yaronta» [Bukhari: 5999, Muslim: 2754].

Saboda haka rahamar Allah Mai girma da ɗaukaka abu ne mai girman gaske, kuma ya wuce tunanin mutum ko kimantawarshi, da ace bayin Allah sun san kimanin rahamar Allah mai girma da ɗaukaka da babu wanda zai ɗebe tsammani daga rahamarSa.

Kuma rahamar Allah Maɗaukaki nau'i biyu ne:

١
Rahamarsa ga dukkanin halittu Aljan da mutane da dabbobi da ma ababen da basa motsi, dukkansu za a sauƙaƙa musu a cikin gidan duniya, kaman yadda Allah Ta'ala YaceYana mai ba da labarin addu'ar Mala'ikunshi: (Ya ubangijinmu lalle rahamarKa da iliminKa sun yalwaci komai da kowa) [Gafir: 7].
٢
Keɓantacciyar rahama ga bayinShi muminai, sai ya datar dasu zuwa ga miShi biyayya, ya kuma sauƙaƙa musu aikin alheri, ya kuma tabbatar dasu akan haka da rahamarsSi, kuma ya cika musu rahamarShi da yafiya da kuma gafara, ya shigar da su Aljannah ya kuma kare su daga shiga wuta, kaman yadda Allah Ta'ala yace:{Kuma ya kasance mai rahama ne ga muminai * Gaisauwarsu a ranar da zasu sadu da shi ita ce aminci, kuma ya tanada musu sakamako mai karamci} [Al-Ahzab: 43 - 44].

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Babu wanda zai shiga Aljannah da ayyukanshi" sai sukace: Har kai ma ya Manzon Allah?! sai yace: Har ni ma sai dai idan Allah ya nitsar dani a cikin rahamarSa" [Bukhari: 6467, Muslim: 2818].

Kuma bawa a duk lokacin da biyayyarshi ta yawaita kuma kusancinshi ga Allah ya ƙaru, rabonshi na daga cancantan wannan rahamar ma sai ya ƙaru, kaman yadda Allah Ta'ala Yace: {Lalle rahamar Allah tana kusa da masu kyautatawa} [Al-A'arafi: 56].

Mai Yawan Ji Mai Yawan Gani:

Allah Mai girma da ɗaukaka yana jin dukkanin sautuka a bisa saɓanin yaruka da kuma banbancin buƙatu, koda ace an bayyana zance ne ko kuwa an ɓoye shi, a yayin da wasu jahilai sukayi tsammanin cewa lalle Allah baya jin sirrukansu da kuma zantukansu na ɓoye, sai faɗin Allah Mai girma da ɗaukaka ya sauƙa yana mai tsawata musu: {Ko suna tsammanin cewa ba Ma jin sirrukansu da kuma gulmace-gulmacensu ne, ba haka bane Manzanninmu suna nan a tattare dasu kuma suna rubutawa} [Azzukhruf: 80].

Kuma Allah subhanahu wa ta'ala yana ganin dukkanin komai koda ace ɗan mitsitsi ne, babu wani abunda yake ɓoyuwa a gare shi, kuma haƙiƙa Annabi Ibrahim alaihis salam ya yiwa mahaifinshi inkarin bautar gunkin da baya ji kuma baya gani, sai yace: {Ya kai baba na meye yasa zaka bautatawa abunda baya ji baya gani kuma bazai iya amfanar da kai da komai ba} [Maryam: 42].

To idan bawa yasan da cewa lalle Allah Mai yawan ji ne Mai yawan gani ne, babu wani abunda yake ɓoyuwa a gare shi ko da ƙwayan zarra ne a cikin sammai da ƙassai, kuma lalle cewa shi Allah Ya san sirri da ma abunda yafi sirrin ɓoyuwa, to hakan zai gadar masa da sanin cewa Allah Yana ganinshi a duk inda yake, daga nan zai kare harcenshi daga faɗawa cikin ƙarya da munanan zantuka, kuma zai kiyaye gaɓɓansa, zai kuma kiyaye zuciyarsa daga fiskantar duk wani abunda zai fusata Allah Mai girma, kuma zaiyi amfani da waɗannan ni'imomin cikin ababen da Allah Yake so ya kuma yarda dasu; domin lalle shi yana ganin sirrinshi da zahirinshi da kuma baɗininshi, saboda hakane Manzon Allah (S. A. W) yace: "Kyautatawa shi ne ka bautawa Allah tamkar kana ganinShi, domin idan kai ka kasance baka ganinShi to Shi yana ganinka" [Bukhari: 4777, Muslim: 9].

Rayayye Wanda Ya Tsaya Da KanShi:

Allah subhanahu wa ta'ala yana da cikakkiyar rayuwa wacce rashi bai rigaye ta ba kuma bazata taɓa gushewa ko ƙarewa ba har abada, kuma babu wani naƙasu ko wani aibi a tattare da ita, domin ubangijinmu Ya girma kuma ya ɗaukaka daga hakan, rayuwa ce wacce take lizimtar cikakkun siffofinshi na daga sani da ji da gani da iko da iradah da sauransu na daga siffofinshi Mai girma da ɗaukaka, kuma duk wanda ya kasance wannan shi ne sha'aninsa, to babu shakka ya cancanci a bauta mishi, ayi mishi ruku'u, kuma a dogara akanshi, kaman yadda Allah Ta'ala Yace: {Kuma ka dogara akan rayayye wanda baya mutuwa} [Alfurƙan: 58].

Kuma ma'anar sunan Allah Mai tsayuwa da kanShi tana nuni zuwa ga ababe biyu:

١
Allah ta'ala cikakken Mawadaci ne, saboda haka Shi ya dogara ne a bisa kanShi Ya kuma wadata ga barin bayinshi, kaman yadda Allah Yace: {Ya ku mutane lalle ku ne mabuƙata zuwa ga Allah, amma kuma Allah Shi Mawadaci ne abun godiya} [Faɗir: 15]. Shi Allah Mai girma ya wadata ga barin bayinShi ta kowace fiska, saboda haka biyayyar mai biyayya ba zata amfanar da shi ba, kuma saɓon mai saɓo ba zai cutar da shi ba, kamar yadda Allah ta'ala Yace: {Duk wanda yayi ƙoƙari to haƙiƙa ya yiwa kanshi ne ƙokƙarin, domin lalle Shi Allah Mawadaci ne ga barin talikai} [Al-Ankabut: 6], Kuma Allah Yace a bisa harcen Annabi Musa alaihis salam: (Idan zaku kafurce ku da dukkanin waɗanda suke doron ƙasa, to lalle Allah Mawadaci ne Abun godiya} [Ibrahim: 8].
٢
Allah Mai cikakken iko ne wajen sarrafa halittunShi, Allah Shi ne yake tsayawa halittunShi da ƙudurarShi, kuma dukkanin halittu matsiyata ne mabuƙata zuwa gare shi, ba za su taɓa wadata ga barin Allah daidai da kiftawar ido ba, kuma abunda muke gani na yadda aka tsara wannan kaunin, da yadda rayuwa take gudana ba komai bane face alamomin tsayuwarshi da kanshi subhanahu wa ta'ala, kamar yadda Allah Yace Yana Mai inkari ga masu mishi tarayya da wani: {Shin ba shi ne wanda yake tsaye akan kowana rai game da abunda ta aikata ba?}[Arra'ad: 33]. Kuma Allah Ta'ala Yace: {Lalle Allah Yana riƙe da sammai da ƙasa domin kada su gushe kuma idan suka gushe babu wanda zai iya riƙe su a bayanshi} [Fadir: 41].

Shiyasa haɗuwan waɗannan manyan sunayen guda biyu a waje ɗaya yana da tasiri na musamman wajen addu'a da kuma ƙasƙantar da kai zuwa ga Allah, kuma ya kasance daga cikin Addu'arshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: "Ya Hayyu ya Ƙayyum bi rahmatika astagisu" (Ya Kai rayayya wanda yake tsaye da kanshi, ina neman agaji da rahamarka) [Attirmizi: 3524].

Sakamakon Imani Da Sunayen Allah Da Kuma Siffofinshi

١
Sanin Allah Maɗaukakin sarki, duk wanda yayi imani da Allah da sunayen shi da kuma siffofinshi, toh zai ƙara sanin Allah Maɗaukaki, sai imaninshi da Allah ya ƙaru, kuma kaɗaita Allanshi zai ƙarfafa, kuma duk wanda yasan sunayen Allah da siffofinshi ya cancanta zuciyarshi ta cika da girmama Allah, da soyayyarshi, da kuma ƙasƙantar da kai zuwa gare shi Mai girma da ɗaukaka.
٢
Jinjina wa Allah da kyawawan sunayen shi, kuma wannan yana daga cikin mafificin nau'in ambaton Allah, Allah Ta'ala yace: {Ya ku waɗanda sukayi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa} [Al-Ahzab: 41].
٣
Roƙon Allah da yin Addu'a a gare shi da sunayen shi da kuma siffofinshi, kaman yadda Allah Yace: {Kuma Allah yana da kyawawan sunaye saboda haka ku roƙe shi dasu} [Al-A'arafi: 180], Kuma misalin haka shi ne mutum yace: Ya mai azurtawa ka azurtani, ya mai karɓan tuba ka karɓa tuba na, ya mai rahama ka rahamce ni.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa