Ɓangaren yanzu model
Darasi Imani da cewa Allah Shi ne Ubangiji:
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ma'anar Tauhidin rububiyyah:
Lalle Allah shi kaɗai ne mahaliccin dukkanin ababen da suke cikin kauni, kuma babu wani mahalicci koma bayanShi, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: {Allah Shi ne mahaliccin dukkan komai}[Azzumar: 62]. Amma kuma halittan da mutum ya keyi ba komai bane face juya abu daga wata siffa zuwa wata siffan, ko kuma tarawa da jerawa, ko wani abu makamancin hakan, amma ba halitta bane na gaske, kuma ba samarwa daga babu bane, kuma ba rayarwa bayan mutuwa bane.
Kuma lalle Allah shi ne mai azurta dukkanin halittu, babu wani mai azurtawa sai Shi, kamar yadda Allah Yace: {Kuma babu wata dabba da take doron ƙasa face arzikinta yana ga Allah} [Hud: 6]
Kuma cewa lalle Shi ne mamallakin dukkan komai, kuma babu wani mamallaki na haƙiƙa koma bayanShi. Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: {Mulkin sammai da ƙasa da ababen da suke cikinsu na Allah ne} [Alma'idah: 120].
Kuma Shi ne mai gudanar da dukkan komai, babu wani mai gudanarwa sai Shi, kaman yadda Allah Ta'ala Yace: {Shi yake gudanar da al'amura daga sama zuwa ƙasa} [Alsajadah: 5].
Gudanarwar Allah Da Gudanarwan Mutum
Mushirkan Larabawa na zamanin Manzon Allah sun tabbatar da rububiyyar Allah:
Ta yaya hankali zai kama cewa mutum ya tabbatar da cewa lalle Allah Shi ne Mahaliccin komai kuma Shi ne Mai gudanar da kauni, Mai rayawa Mai kashewa, sa'annan ya gudanar da wani nau'i na ibadah ga waninShi?! wannan shi ne mafi munin zalumci da mafi girman zunubi, saboda hakane Luƙuman yace wa ɗanshi yayin da yake yi mishi nasiha kuma yake shiryar da shi: {Ya ɗa na kada kayi shirka da Allah, domin lalle shirka zunubi ne mai girman gaske} [luƙuman: 13].
Kuma yayin da aka tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: Wana zunubi ne yafi girma a wajen Allah? sai yace: "Shi ne ka sanyawa Allah kishiya bayan shi ya halicce ka" [Bukhari: 4477, Muslim: 86].
Idan bawa ya samu tabbacin cewa babu wani daga cikin halittu wanda ya isa ya fita daga cikin ƙaddarar Allah Maɗaukaki; domin lalle Allah Maɗaukaki Shi ne Mahaliccin su gaba ɗaya, babu wani mahalicci sai shi, kuma domin Shi ne Mamallakin su Yana sarrafa su yadda yake so daidai da hikimarShi, kuma idan yasan cewa lalle dukkanin umarni yana hannun Allah Maɗaukaki, babu wani mai gudanar da kauni sai Allah Shi kaɗai, kuma ƙwayan zarra bata isa ta motsa ba sai da izininShi, kuma ba zata natsu ba sai da umarninShi, kuma idan ya tabbatar da cewa lalle babu mai azurtawa sai Allah. Hakan zai gadar mishi da natsuwa a zuciyarshi, kuma zai ƙara mishi son Allah Shi kaɗai, kuma zai roƙe Shi Shi kaɗai, kuma zai nemi biyan buƙata daga gare Shi, kuma zai dogara akanShi Shi kaɗai a cikin dukkanin al'amuran rayuwarshi.