Ɓangaren yanzu model
Darasi Shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah
Musulunci ya sanya wa kalmar tauhidi la'ilaha illallahu matsayi mai girman gaske kuma mai darajah
Matsayin La ilaha illal lahu
Saboda haka, lalle Shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi ne mafi girman abunda ke wajibi kuma mafi mahimmancin su.
Ma'anar La ilaha illal lahu:
Kuma abun nufi da abun bauta: Shi ne abun bautan da zukata suke ƙasƙantuwa a gare shi sai su girmama shi, su roƙe shi, suji tsoronshi, su kuma tsammace shi, duk wanda ya ƙasƙantar da kanshi ga wani, ya rusuna a gare shi, ya so shi, ya tsammace shi; toh haƙiƙa ya riƙe shi ubangiji abun bauta, kuma dukkanin waɗannan ababen da ake bautatawa ba ababen bauta bane saidai abun bauta ɗaya, kuma Shi ne Ubangiji, Mahalicci, Mai girma da ɗaukaka
Domin Allah Maɗaukaki Shi ne wanda ya cancanci bauta ba tare da waninshi ba, kuma shi ne wanda zukata suke bauta mishi domin soyayya, da girmamawa, da karramawa, suna masu tsoronshi, masu ƙasƙantuwa zuwa gare shi, masu dogaro akanshi, kuma masu roƙonshi, saboda haka ba a fiskantar wani da Addu'a saidai Allah, kuma ba a neman agaji sai a wurinShi, kuma ba a dogara sai dai akanShi, kuma ba a yiwa wani sallah sai dai Shi, kuma ba a yanka domin neman kusanci sai dai gare Shi, saboda haka ya wajaba a tsarkake bauta ga Allah Ta'ala, kamar yadda Allah Maɗaukaki yace: (Kuma ba a umarce su da komai ba face su bautatawa Allah, suna masu tsarkake mishi addini) [Albayyinah: 4].
Kuma duk wanda ya bautatawa Allah Ta'ala yana mai tsarkake mishi addini, mai tabbatar da ma'anar la ila illal lahu, toh zai samu rayuwa mai daɗi da buɗuwan zuciya, da murna, da farin ciki, saboda zukata ba sa samun natsuwa, kuma ba sa kasancewa cikin tsanaki sai da kaɗaita Allah Ta'ala da Ibadah, kamar yadda Allah Maɗaukaki Yace: {Duk wanda ya aikata aiki na gari na miji ko ta mace, to lalle zamu raya shi rayuwa mai daɗi} [Annahli: 97).