Ɓangaren yanzu model
Darasi Siffar Sallah
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
1- Anniyyah
Mai sallah zai tsaya yayin fara sallah sai yace: Allahu Akbar (Allah Shi ne mafi girma) sai ya ɗaga tafin hannayenshi zuwa kafaɗunshi ko kuma zuwa daura da kunnuwanshi, yana mai miƙe yatsunshi mai sanya tafin hannunshi suna fiskantar alkiblah.
Ma'anar kabbara
3- Bayan kabbara sai ya sanya hannunshi na dama akan na hagu a bisa ƙirjinshi, kuma zai aikata hakan a koda yaushe yayin da yake tsaye.
Ya wajaba akan kowana musulmi da ya haddace suratul Fatiha; domin karanta ta rukuni ne a cikin sallah ga wanda yake sallah shi kaɗai ko ya kasance mamu a cikin sallar da liman baya bayyana karatu a cikinta.
Ya wajaba akan kowana musulmi da ya haddace suratul Fatiha; domin karanta ta rukuni ne a cikin sallah ga wanda yake sallah shi kaɗai ko ya kasance mamu a cikin sallar da liman baya bayyana karatu a cikinta.
Suratul Fatiha
10- Sa'annan yayi kabbara domin tafiya zuwa ruku'u yana mai ɗaga hannayenshi zuwa kafaɗunshi ko sama da su, yana mai sanya cikin tafukan hannunshi suna fiskantar alkiblah kamar yadda yayi a kabbarar farko.
11- Sai yayi ruku'u; Da sunkuyar da bayanshi ta bangaren alkiblah kuma sai ya daidaita bayanshi da kanshi, yana mai sanya tafukan hannunshi akan gwiwowinshi, kuma ya rarraba tsakanin yatsunshi, sai kuma yace: (Subhana rabbiyal Azim) kuma anso da ya maimaita wannan tasbihin har sau uku, amma kuma abunda yake wajibi shi ne sau ɗaya kawai, kuma ruku'u wajen girmama Allah ne da kuma jinjina miShi.
Ma'anar (Subhana rabbiyal azim) shi ne: Ina tsarkake Allah Mai girma kuma ina mai kore miShi dukkanin tawaya. Mai sallah zai faɗeta ne alhali yana cikin ruku'u.
12- Zai ɗago daga ruku'u zuwa yanayin tsayuwa yana mai ɗaga hannayenshi zuwa kafaɗunshi, cikin tafukan hannunshi kuma suna fiskantar alkiblah kamar yadda ya gabata, yana mai cewa: (Sami'allahu liman hamidahu) - Idan ya kasance shi ne liman ko yana sallah shi kaɗai- sai jama'a kuma suce: (Rabbana wa lakal hamdu).
Kuma anso da yayi ƙari sai yace bayanta: (Hamdan kasiran ɗayyiban mubarakan fihi, mil'as sama'i wa mil'al ardi, wa mil'a ma shi'ita min shai'in ba'adu).
13. Daga nan sai ya zube a ƙasa yana mai kabbara kuma mai sujjada a bisa gaɓɓanshi guda bakwai, kuma su ne: Goshi tare da hanci, da hannaye biyu, da gwiwowi biyu, da diga-digai biyu, kuma anso da ya nisantar da hannayenshi daga jikinshi, kuma ya nisantar da cikinshi daga cinyoyinshi, kuma ya nisantar da cinyoyinshi daga ƙafafunshi a cikin sujjadarshi, kuma ya raba zira'inshi da kasa.
Sujjada tana daga cikin mafi girman wurin addu'a ga Allah Mai girma da ɗaukaka, sai musulmi ya roƙi Allah abunda yake so na alherin duniya da lahira a cikinta bayan yin zikirin da yake wajibi, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Mafi kusancin wurin da bawa yake kasancewa ga Allah shi ne a lokacin da yake sujjada, saboda haka ku yawaita Addu'a a cikinta" (Muslim: 482).
15. Sa'annan sai yace: (Allahu Akbar), sai ya zauna a tsakanin sujjada biyu, kuma anso mishi da ya zauna akan ƙafarshi ta hagu ya kuma tayar da ta dama, sai ya sanya hannayenshi a bisa farkon cinyoyinshi sama da gwiwowinshi.
Siffar zama a cikin sallah
16. Zai ce yayin da yake zaune a tsakanin sujjada biyu: (Rabbigfir li) kuma anso da ya maimaita ta har sau uku.
17. Sa'annan sai yayi wata sujjada tamkar ta farkon.
18. Sa'annan sai ya taso daga sujjada ta biyu zuwa yanayin tsayuwa yana mai cewa: (Allahu Akbar).
19. Sai ya sallaci raka'ah ta biyu tamkar ta farko, ba wani banbanci
20. Bayan sujjadarshi ta biyu a cikin raka'a ta biyu zai zauna irin zaman tsakanin sujjada biyu domin karatun tahiyyah, kuma zaiyi nuni da manuniyarshi ta hannun dama zuwa ɓangaren alkiblah sai yace: (Attahiyatu lillahi wassalawatu waɗɗayyibat, Assalamu alaika ayyuhan nabiyyu wa rahmatullahi wa barkatuhu, Assalamu alaina wa ala ibadil Lahis Salahina, Ash hadu an la'ilaha illal lahu, Wa ash hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluhu).
22. Sa'annan a cikin raka'a ta ƙarshe bayan sujjada ta biyu zai zauna domin karatun tahiyyar ƙarshe, kuma siffar zaman shi ne ya zauna akan ɗuwawunshi na hagu yana mai kafa ƙafarshi ta dama sai ya fitar da ƙafarshi ta hagu daga ƙarƙashinta, sai ya faɗi abunda ya faɗa a cikin tahiyar farko, sa'annan sai ya karanta salatul Ibrahimiyyah wanda shi ne: «Allahumma salli ala muhammad, wa ala ali muhammad, kama sallaita ala Ibrahima wa ala ali Ibrahim innaka Hamidun Majid, wa barik ala muhammad wa ala ali muhammad kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim innaka Hamidun Majid».
23. Sa'annan sai ya juya zuwa ɓangaren dama yana mai cewa: (Assalamu alaikum wa rahmatullah), sai ya sake juyawa zuwa ɓangaren hagu ya faɗi kwatankwacin abunda ya faɗa a ɓangaren dama, kuma da sallama ne musulmi zai kasance ya kammala sallarshi kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Shiganta shi ne kabbara kuma fita daga gare ta shi ne sallama" (Abu Dawood: 618, Attirmizi: 3) Ma'ana: Lalle Sallah ana shiganta ne da kabbarar farko ana kuma fita daga gareta ne da salama.
24. Anaso bayan sallama daga sallar farillah da mutum yace:
Ya wajaba a gare shi da ya ƙoƙarta matiƙar ƙoƙari wajen ganin cewa ya haddace suratul Fatiha da yaren larabci domin lalle sallah bata inganta sai da ita, kuma ya wajaba a gare shi da yayi matiƙar ƙoƙari wajen haddace ambaton Allan da suke wajibi a cikin sallah, kuma su ne: Fatiha, da kabbara, da Subhana rabbiyal Azim, da sami'al Lahu liman hamidahu Rabbana lakal hamdu, da Subhana rabbiyal A'ala, da Rabbigfirli, da tahiyah, da salati a bisa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da kuma Assalamu Alaikum wa rahmatullah.
Kuma har zuwa lokacin da zai haddace toh ya wajaba akanshi da ya dinga maimaita abunda ya sani na daga tasbihi da kabbara da hamdala yayin sallah, ko kuma yata karanta ayar da ya haddace ta yayin tsayuwa domin faɗin Allah Ta'ala: (Kuji tsoron Allah gwargwadon ikonku) (Attagabun: 16).
Ya kamata ya zamto mai matiƙan kwaɗayi -gwargwadon iko -akan sallah cikin jama'a domin ya inganta sallolinshi, kuma domin lalle liman zan ɗauki wani ɓangare daga cikin tawayewan mamu.