Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Imani Da litattafai

Imani da litattafan da aka sauƙar daga wurin Allah rukuni ne daga cikin rukunnan imani. A cikin wannan darasin zaka san ma'anan imani da litattafai da mahimmancin su, da sunan wasunsu, da kuma matsayarmu akan waɗanda suke nan daga cikinsu a yau.

  • Sanin ma'anar imani da litattafai da mahimmancin shi. 
  • Sanin matsayar musulmi dangane da litattafan da suke nan a yau
  • Sanin abunda yake wajibi akan musulmi dangane da Alkur'ani mai girma

Ma'anar Imani Da Litattafai

Gaskata cewa lalle Allah Maɗaukaki yanada litattafai waɗanda ya sauƙarwa manzanninshi domin su isarwa bayinshi, kuma cewa lalle waɗannan litattafan maganar Allah Ta'ala ne, haƙiƙa yayi furuci dasu ta yadda ya dace da shi subhanahu wa ta'ala, kuma lalle waɗannan litattafan a cikinsu akwai shiriya da haske da rabauta ga mutane a cikin duniya da lahira.

Mahimmancin Imani Da Litattafai

Imani da litattafai ɗaya ne daga cikin rukunnan imani, Allah Maɗaukaki Yace:{Ya ku waɗanda sukayi imani kuyi imani da Allah da manzanninshi da littafin da ya sauƙarwa manzanninshi da kuma littafin da ya sauƙar a baya} [Annisa'i: 136]. Sai Allah Maɗaukaki yayi umarni da imani da shi, da manzanninshi, da litattafan da aka sauƙarwa Manzonshi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi kuma shi ne Alkur'ani, kaman yadda yayi umarni da ayi imani da litattafan da aka sauƙar dasu gabanin Alkur'ani.

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace dangane da imani: "Kayi imani da Allah, da mala'ikunshi, da litattafanshi, da manzanninshi, da ranar ƙarshe, kuma kayi imani da ƙaddara alherinshi da sharrinshi" (Muslim: 8)

Menene imani da litattafai ya ƙunsa?

١
Imani da cewa sauƙo dasu daga wurin Allah gaskiya ne
٢
Imani da cewa lalle su maganan Allah Maɗaukaki.
٣
Imani da wanda Allah ya ambata daga cikin litattafan shi, kaman Alkur'ani mai girma wanda aka sauƙarwa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Attaurah wanda aka sauƙarwa Annabi Musa alaihis salam, da Injila wanda aka sauƙarwa Annabi Isa alaihis salam.
٤
Daga cikin labaran litattafan da suka gabata zamu gaskata wanda Alkur'ani mai girma ko sunnar Annabi suka gaskata, kuma mu ƙaryara wanda Alkur'ani da sunnah suka ƙaryata, kuma muyi shiru akan sauran labaran, ba za mu gaskata su ba kuma ba zamu ƙaryata su ba.

Menene matsayarmu dangane da litattafan da suka gabata?

Mumini zaiyi imani da cewa Attauran da aka sauƙarwa Annabi Musa alaihis salam, da Injilan da aka sauƙarwa Annabi Isa alaihis salam, gaskiya ne daga wurin Allah Ta'ala, kuma haƙiƙa sun ƙunshi hukunce-hukunce da wa'azozi da labarai waɗanda a cikinsu akwai shiriya da haske ga mutane a cikin rayuwar su, da duniyarsu da kuma lahirarsu. amma kuma Allah Maɗaukaki ya bamu labari a cikin Alkur'ani mai girma cewa lalle Ahlul kitabi na daga Yahudu da Nasara sun jirkita litattafan su, sunyi ƙari a cikinsu, kuma sun rage daga garesu, saboda haka ba kamar yadda Allah ya sauƙar dasu suke ba.

Saboda haka, attauran da muke gani a yau ba ita ce Attaurar da aka sauƙarwa Annabi Musa alaihis salam ba, domin yahudawa sun jirkita ta sun kuma canza ta, kuma sunyi wasa da dayawa daga cikin hukunce-hukuncen ta. Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma lalle daga cikinsu akwai wata ƙungiya suna karkata harsunansu da littafi, domin kuyi zaton cewa daga littafin yake, alhali ba daga littafin yake ba, kuma suna cewa shi daga wajen Allah yake, alhalin ba daga wurin Allah yake ba, kuma suna faɗan ƙarya ga Allah, alhali suna sane} [Ali Imran: 78].

Hakama Injilar da muke ganinta a yau ba ita ce Injilar da aka sauƙarwa Annabi Isa alaihis salam ba, domin haƙiƙa Nasara sun jirkita ta sun canza ta, kuma sunyi wasa da dayawa daga cikin hukunce-hukuncen ta. Allah Ta'ala Yace game da Nasara: (Daga cikin waɗanda sukace lalle mu ne nasara mun riƙi alƙawarinsu, sai suka manta da wani yanki na abunda aka tunatar dasu dashi, sai muka gudanar da adawa da ƙeta a tsakaninsu har zuwa ranar alƙiyama, kuma da sannu Allah zai basu labarin abunda suka kasance suna aikatawa} [Ma'ida: 14].

Shiyasa a yau mukaga littafin da ake ƙiranshi da littafi mai tsarki wanda yake hannun Nasara da kuma da yawa daga cikin abunda ke cikin Attaurah da Injila sun ƙunshi da yawa daga munanan aƙidu, da labaran ƙarya, da kuma ƙirƙirarrun hikayoyi.

Duk da cewa munyi imani da cewa lalle Attaurah da Injilan da muke ganinsu a yau an jirkita su an kuma sauya su kaman yadda Alkur'ani ya bamu labari, saidai musulmi zai girmama su kada ya wulaƙanta su kuma kada ya tozarta su, domin ba abun mamaki bane su ƙunshi wani ɓangare na daga maganan Allah wanda ba a jirkita shi ba.

Menene Yake Wajibi Akanmu Dangane Da Alkur'ani Mai Girma?

١
Ya wajaba akanmu da muso Alkur'ani mai girma, mu girmama shi mu kuma mutunta shi, domin lalle shi maganan mahaliccinmu ne Mai girma da ɗaukaka, saboda haka, shi ne mafi gaskiyan zance da kuma mafificinshi.
٢
Ya wajaba akanmu da muna karanta shi kuma muna tilawarshi, tare da tuntuntuni akan ayoyinshi da surorinshi, sai mu dinga tunani akan wa'azin Alkur'ani, da labaranshi, da ƙissoshinshi, kuma sai muna bijirar da rayuwanmu akansu domin mu banbance gaskiya da ƙarya.
٣
Kuma ya wajaba akanmu aiki dashi, da bin hukunce-hukuncen shi, da aikata umarninshi, da gujewa haninshi, da ladabtuwa da laddubanshi, da kuma sanyashi shi ne tafarkin rayuwarmu.

A yayin da aka tambayi Aisha Allah Ya kara mata yarda dangane da halayen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai tace: "Ya kasance halayenshi su ne Alkur'ani" (Ahmad: 24601)

Ma'anar hadisin: Lalle Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance a cikin rayuwar shi, da ayyukanshi, da zantukanshi yana zantar da hukunce-hukuncen Alkur'ani da shari'o'inshi ne a aikace, haƙiƙa Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tabbatar da cikakken bin shiriyar Alkur'ani, kuma kyakkyawar abun koyi ne ga kowana ɗaya daga cikinmu, kaman yadda Allah Maɗaukaki Yace: {Haƙiƙa abun koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasance yana fatar rahamar Allah da ranar lahira, kuma ya ambaci Allah mai yawa} [Al-Ahzab: 21].

Sauƙaƙa haddan Alkur'ani da tilawarshi a sassan duniya daban-daban tare da bambance-bambancen yarukan mahaddatan, da yanayinsu; yana daga cikin mafi girman dalilin kiyaye wannan Alkur'ani daga Allah.

Ababen Na Musamman Da Alkur'ani Ya Keɓanta Dasu:

Lalle Alkur'ani mai girma maganan Allah Ta'ala ne wanda ya sauƙarwa Annabinmu abin koikoyonmu Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga nan ne, ya wajaba akan mumini da ya girmama wannan littafin, kuma yayi riƙo da hukunce-hukuncen shi, ya dinga karanta shi kuma yana tuntuntuni akan ayoyinshi. kuma ya ishe mu kasancewan wannan Alkur'anin shi ne mai shiryar damu a duniya, da kuma sababin tsirarmu a lahira. Kuma Alkur'ani mai girma yanada wasu ababe na musamman masu yawa waɗanda ya keɓanta dasu daga sauran litattafan da aka sauƙar daga sama waɗanda suka rigaya, daga cikinsu:

1- Lalle Alkur'ani mai girma ya ƙunshi dukkanin hukunce-hukuncen Allah a taƙaice

Kuma yazo ne domin ƙarfafa da kuma gaskata litattafan da suka zo gabaninshi na daga umarni da bautawa Allah shi kaɗai. Allah Maɗaukaki Yace:(Kuma mun sauƙar maka da littafi da gaskiya, yana gaskata ababen da suka rigaye shi na daga littafi kuma yana mai bada shaida akanshi} [Al-Ma'idah: 48]. Kuma ma'anar {Yana mai gaskata abunda ya rigaye shi na daga littafi} shi ne yana dacewa da ababen da sukazo a cikin labaran litattafan da suka gabata, da ababen da sukazo a ciki na aƙidah, kuma ma'anan {Mai bada shaida akanshi} shi ne yana amintar da shi kuma yana bada shaida akan litattafan da suka zo kafin shi.

2- Lalle ya wajaba akan dukkanin mutane tare da bambance-bambancen yarukansu da ƙabilunsu da suyi imani da shi.

Kuma za ayi amfani dashi a kowana zamani koda ace wannan zamanin ya nisanci zamanin da aka sauƙar dashi, koma bayan sauran litattafan da suka rigaya, domin lalle su ana sauƙarwa wasu mutane ne na musamman a wani zamani na musamman, Allah Maɗaukaki Yace: {Kuma anyi mini wahayin wannan Alkur'ani domin na gargaɗe ku da shi da kuma duk wanda labari ya kai gare shi} [Al-An'am: 19].

3- Lalle Allah Maɗaukaki Ya ɗauki nauyin kare Alkur'ani mai girma

Saboda haka ne ba a taɓa jirkita shi ba kuma ba za a jirkita shi ba har abada kamar yadda Allah Ta'ala Yace:{Lalle Mu ne muka sauƙar da ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne} [Alhijir: 9]. Saboda hakane dukkanin labaran da suka zo a cikinshi ingantattu ne kuma wajibi ne a gaskata su.

Imani da litattafai yanada amfani, daga cikinsu:

١
Sanin yadda Allah Maɗaukaki yake kula da bayinshi, da sanin cikakkiyar rahamarshi ta yadda ya aikowa kowana mutane littafin da zai shiryar dasu, ya kuma sama musu jin daɗin rayuwa a cikin duniya da lahira.
٢
Sanin hikimar Allah Ta'ala a cikin shari'arshi, ta yadda ya shar'antawa kowana mutane abunda zai dace da yanayinsu kuma ya saje da halittansu, kamar yadda Allah Madaukaki Yace: {Kuma kowanne daga cikinku mun sanya musu shari'a da kuma hanyar da ta dace} [Ma'idah: 48].
٣
Godewa ni'imar Allah a bisa sauƙar da waɗancan litattafan, domin waɗannan litattafan shiriya ne da kuma haske a rayuwar duniya da lahira, saboda hakane ya kamata a godewa Allah a bisa wannan ni'ima mai girman gaske.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa