Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Imani Da Manzanni

Imani da manzanni ɗaya ne daga cikin rukunnan imani guda shida. A cikin wannan darasin zaka san ma'anan imani da manzanni da mahimmancin shi, kuma zaka san siffofinsu, da wasu daga cikin mu'ujizozinsu.

  • Sanin ma'anan imani da manzanni 
  • Sanin siffofin Annabawa da na Manzanni
  • Sanin wasu daga cikin mu'ujizozinsu 
  • Sanin amfanin imani dasu

Ma'anan imani da Manzanni

Shi ne tabbatar da cewa lalle Allah ya aiko Manzo zuwa kowace Al-ummah daga cikinsu, domin ya kirasu zuwa ga Allah Ta'ala shi kaɗai bashi da abokin tarayya, kaman yadda Allah Maɗaukaki Yace:{Kuma lalle Mun aiko da Manzo a cikkn kowace Al-ummah da cewa ku bautawa Allah kuma ku nisanci Ɗagutu} [Alnahl: 36].

Zamuyi imani da cewa dukkanin Manzanni masu gaskiya ne kuma abun gaskatawa ne, masu taƙawa ne amintattu ne, shiryayyu ne masu shiryarwa ne, kuma cewa lalle sun isar da dukkanin abunda Allah ya aiko su dashi, basu ɓoye ba kuma basu canza ba, kuma basu ƙara wani abu akanshi daga wurinsu ba koda harafi ne kuma basu rage shi ba, kamar yadda Allah Maɗaukaki Yace: {Wadanda suke isar da sakon Allah kuma suna tsoronshi, kuma basa tsoron kowa sai Allah,kuma ubangiji ya isa shaida} [Al-Ahzab: 39].

Buƙatuwan Mutane Zuwa Ga Saƙon Allah:

Mutane ba zasu iya rayuwa ba tare da saƙon Allah wanda zai dinga bayyana musu shari'o'inshi ba, ya kuma shiryar dasu zuwa daidai da gaskiya, kuma saƙon Allah shi ne ruhin duniya da haskenshi da kuma rayuwarshi, toh ta yaya duniya zata rayu idan ta rasa ruhi da rayuwa da kuma haske?!

Saboda hakane Allah ya ambaci saƙonshi da ruhi, kuma idan aka rasa ruhi toh babu rayuwa, Allah Maɗaukaki Yace: Kuma kaman hakane muka sauƙar maka da ruhi daga lamarinmu, baka kasance kasan menene littafi ko imani ba, saidai mun sanya shi haske ne wanda muke shiryar da wanda mukeso dashi daga cikin bayinmu}[Alshura: 52]. duk da cewa hankali yakan iya banbanta tsakanin alheri da sharri gaba daya saidai cewa bazai iya gane haƙiƙaninsu da kuma ababen da suka ƙunsa ba. Kuma ba a sanin yadda ake gudanar da ibadu sai ta hanyar wahayi da kuma saƙon Allah.

Saboda haka, babu wata hanya zuwa ga tsira da rabauta a cikin duniya da lahira sai ta hannun Manzanni, kuma babu yadda za a tantance tsakanin mai kyau da mara kyau yadda ya kamata sai dai ta hanyarsu, kuma duk wanda ya kau da kai ga barin saƙon Allah, babu shakka zai ruɗe, zai kasance a cikin baƙin ciki, kuma zai taɓe gorgodon kau da kanshi da juyawanahi. Allah Maɗaukaki Yace:{Sai mukace ku sauƙa gaba ɗayanku daga cikinta, lalle da sannu shiriya zata zo muku daga gare ni, duk wanda yabi shiriya ta, toh babu tsoro a gare su kuma ba zasuyi bakin ciki ba * Kuma waɗanda suka kafurta kuma suka ƙaryata ayoyinmu waɗannan su ne ma'abota wuta zasu tabbata a cikinta} [Albakara: 38- 39].

Ɗaya Daga Cikin Rukunnan Imani:

Imani da Manzanni ɗaya ne daga cikin rukunnan imani guda shida, Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: {Manzon yayi imani da abunda aka sauƙar mishi daga wurin ubangijinshi da muminai, kowa yayi imani da Allah, da mala'ikunshi, da litattafanshi, da Manzanninshi, ba zamu banbanta tsakanin ɗaya daga Manzanninshi ba} [Albaƙara: 285]. Sai wannan ayar tayi nuni a bisa wajabcin imani da dukkanin Manzanni Alaihimus Salam ba tare da rarrabe tsakaninsu ba, saboda haka ba zamuyi imani da shashin Manzanni kuma mu kafurcewa shashi ba kamar yadda yahudu da nasara sukayi.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace dangane da imani: "Shj ne kayi imani da Allah, da mala'ikunshi, da litattafanshi, da Manzanninshi, da ranar ƙarshe, kuma kayi imani da ƙaddara alherinshi da sharrinshi" (Muslim: 8)

Ayoyin Manzanni Da Mu'ujizozinsu

Allah Maɗaukaki ya ƙarfafa Manzannin shi alaihimus salamu da hujjoji masu yawa da kuma ƙarinoni daban-daban waɗanda suke nuni i zuwa ga gaskiyarsu da Annabtansu, daga cikin hakan akwai taimaka musu da mu'ujizozi da kuma ayoyi bayyanannu waɗanda wani mutum ba zai iya aikata su ba; domin tabbatar da gaskiyarsu da tabbatar da Annabtansu. Kuma abun nufi da Mu'ujiza shi ne faruwan abunda ya saɓawa Al'ada wanda Allah zai bayyana shi a bisa hannun Annabawanshi da manzanninshi ta yadda wasu mutane ba zasu iya aikata irinshi ba.

Daga Cikin Mu'ujizozin Annabawa Alaihimus Salam

١
Juya sandan Annabi Musa alaihis salam zuwa macijiya.
٢
Annabi Isa alaihis salam yana baiwa mutanenshi labarin abin da suka ci da abunda suka tanada a gidajensu.
٣
Tsagewar wata ga Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Menene imani da Manzanni ya ƙunsa?

1- Imani da cewa lalle saƙon da suka zo dashi daga Allah ne kuma gaskiya ne, kuma dukkanin saƙonnin sunyi ittifaƙi wajen ƙira zuwa ga bautar Allah shi kaɗai bashi da abokin tarayya

Allah Maɗaukakin Sarki Yace:{Kuma lalle Mun aiko da Manzo cikin kowana Al-ummah da cewa ku bautawa Allah kuma ku nisanci Ɗagutu} [Alnahl: 36

Kuma shari'o'in Annabawa zasu iya bambanta a cikin rassa na daga halal da haram da abunda ya dace da kowace Al-umma, kamar yadda Allah Ta'ala Yace: {Ga kowanne daga cikinku mun sanya mishi shari'a da kuma tafarki}[Alma'idah: 48].

2- Imani da dukkanin Annabawa da Manzanni

Wajibi ne muyi imani da waɗanda Allah Ya amabata daga cikin Annabawa, kaman: Muhammad, da Ibrahim, da Musa, da Isa, da Nuhu, da Yakubu, da Yusuf, Da Yunus da wasunsu Amincin Allah ya tabbata a gare su baki ɗaya, amma kuma waɗanda bamu san sunayensu ba daga cikinsu, sai muyi imani dasu a dunƙule, kuma duk wanda ya kafurcewa manzancin ɗaya daga cikinsu toh lalle ya kafurce musu gaba ɗaya.

3- Gaskata abunda ya inganta na daga labarunsu da Mu'ujizozinsu

Sai mu gaskata abunda ya inganta na daga labaran Manzanni da mu'ujizozinsu na cikin Alkur'ani da Sunnah, kaman labarin darewan kogi ga Annabi Musa alaihis salam.

4- Aiki da shari'ar Manzon da aka aiko shi zuwa gare mu, kuma shi ne mafificinsu kuma cikamakinsu: Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Daga Cikin Siffofin Manzanni:

1- Lalle su mutane ne

Kuma bambancin dake tsakaninsu da wasunsu shi ne lalle su Allah ya keɓance su da wahayi da kuma saƙo. Allah Ta'ala Yace:{kuma bamu..} [Al-Anbiya: 7], Kuma Allah Ta'ala Yace:{Kace lalle ni mutum ne tamkar ku, ana mini wahayin cewa lalle abun bautanku guda ɗaya ne} [Alkahfi: 110]. Saboda haka basu da wata sifffa ta rububiyyah ko ta Uluhiyyah, saidai su mutane ne waɗanda suka kai maƙura wajen cikan zahirin halitta kamar yadda suka kai maƙura wajen cikan kyawawan halaye. Kuma lalle su ne mafi alherin mutane wajen dangi, kuma suna da kaifin hankali, da harshe mai bayani wanda hakanne ya basu damar isar da saƙon Allah da kuma jurewa wahalhalun Annabta, kuma abunda yasa Allah ya sanya Manzanni daga cikin mutane, domin ya kasance waɗanda zasuyi koikoyo dasu daga jinsinsu suke, domin hakan zai taimakawa mutane wajen bin manzannin da kuma koyi dasu.

2- Allah Ya Keɓance Su Da Manzanci

Allah Mai girma da ɗaukaka ya Keɓance su da wahayi koma bayan sauran mutane, kamar yadda Allah Ta'ala Yace:{Allah yana zaɓan Manzanni daga mala'iku hakama daga cikin mutane, lalle Allah Mai yawan ji ne Mai yawan gani} [Hajj 75]. Saboda haka Annabta da Manzanci ba ababe ne da ake samunsu sakamakon tsarkakan rai, ko kaifin hankali ko iya magana ba, saidai su zaɓen Allah ne, haƙiƙa Allah ya zaɓi Manzanni daga cikin sauran mutane, kaman yadda Allah Ta'ala Yace:{Allah Shi ya san wurin da yake sanya saƙonshi} [Al-An'am: 124].

3- Lalle Su Kararru Ne Cikin Ababen Da Suke Isarwa Daga Allah

Sakamakon haka, basa kuskure wajen isar da saƙon Allah, kuma basa kuskure wajen zantar da abunda Allah Yayi musu wahayinshi.

4- Gaskiya

Dukkanin Annabawa masu gaskiya ne a cikin zantukansu da ayyukansu. Allah Ta'ala Yace: {Wannan shi ne abunda Allah Mai rahama Yayi alƙawari, kuma manzanni sunyi gaskiya}[Yasin: 52]

5- Haƙuri

Hakƙiƙa sunyi ƙira zuwa ga addinin Allah Maɗaukaki suna masu bishara masu gargaɗi, kuma a sakamakon haka nau'i daban daban na cutarwa da wahalhalu sun same su, sai sukayi haƙuri suka kuma jure domin ɗaukaka kalmar Allah, Allah Ta'ala Yace:{Kayi hakƙuri kaman yadda ma'abota girma na daga Manzanni sukayi haƙuri} [Al-Ahƙaf: 35].

Imani Da Manzanni Yanada Amfanu Masu Yawa, Daga Cikinsu:

١
Sanin rahamar Allah Maɗaukaki da kuma kulawar shi ga bayinshi, ta yadda ya tura musu Manzanni domin su shiryar dasu zuwa tafarki ingantacce, kuma su bayyana musu yadda zasu bautawa Allah; domin ƙwaƙwalwar mutum ba zata iya nuna mishi hakan ba, Allah Ta'ala Yace dangane da Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: {Kuma bamu aiko ka ba face ka zamto rahama ga dukkanin talikai} [Al-Anbiya: 107].
٢
Godewa Allah Maɗaukakin Sarki a bisa wannar ni'imar mai girman gaske.
٣
Son Annabawa alaihimus salamu, da girmama su, da kuma jinjina musu da abunda ya dace dasu; domin lalle su sun bautawa Allah kuma sun tashi da isar da saƙonshi tare da yiwa bayinshi nasiha.
٤
Bin saƙon da Manzanni suka zo dashi daga wurin Allah, kuma wannan saƙo shi ne bautawa Allah shi kaɗai ba tare da abokin tarayya ba, da kuma aiki dashi, kuma da aikata hakanne muminai zasu samu alheri da shiriya da jin daɗi a cikin duniya da lahira.

Allah Maɗaukaki Yace:{Kuma duk wanda yabi shiriya ta, toh ba zai ɓata ba kuma ba zai tozarta ba * Kuma wanda ya kau da kai ga barin ambatona toh lalle zai rayu rayuwa mai ƙunci}[Ɗaha: 123- 124].

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa