Ɓangaren yanzu model
Darasi Wasu yanayi na musamman a cikin tsarki
Shafa akan huffi da kuma safa
An shar'anta shafa akan huffi ko safa yayin alwala ne idan har musulmi ya kasance ya sanya su a bisa tsarki na daga kari biyu babba da ƙarami.
Tsawon lokacin shafa akan huffi da safa
Shafa akan huffi ya inganta yayin alwala, amma kuma a yayin wanka daga janaba ya wajaba a wanke diga-digai biyu cikin kowana hali.
Ana fara ƙirga lokacin shafa akan huffi da safa ne daga farkon lokacin shafa bayan kari
Bendeji shi ne abunda ake sanyawa akan wata gaɓa yayin da taji rauni ta hanyar karaya ko kujewa domin ya taimaka mata wajen saurin warkewa da kuma sauƙaƙa zafi.
Shafa akan wannan bendijin da jiƙaƙƙen hannu ya wadatar yayin buƙatan hakan, sawa'an a cikin alwala ne ko kuma yayin wankan janaba.
Zai wanke ɓangaren wannan gaɓan wanda ba a kulle da bendejin ba, wurin dake kulle na bendejin kuma zai shafa shi da jiƙaƙƙen hannu.
Tsawon lokacin shafa akan Bendeji
Taimama
Siffar Taimama
Mutum zai bugi ƙasa da tafin hannayenshi biyu bugu guda.
Zai shafi zahiran tafin hannunshi na dama da cikin hannunshi na hagu da kuma akasin haka.
Zai shafi fuskarshi da abunda ya maƙale a tafin hannunshi na daga turɓayan.