Ɓangaren yanzu model
Darasi Sanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
Sunan Annabinmu (S. A. W)
Muhammadu Ɗan Abdullahi Ɗan Abdul Muɗɗalib Ɗan Hashim Baƙuraishe, kuma shi ne mafificin larabawa dangi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Allah ya aiki Annabinmu Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zuwa ga mutane baki ɗaya da dukkanin jinsinsu da ƙabilunsu, kuma ya wajabta yin imani da shi da yi mishi biyayya akan dukkanin mutane. Allah Ta'ala yace: {Kace ya ku mutane lalle ni Manzon Allah zuwa gare ku baki ɗaya} [Al-A'araf: 58].
Allah Ya sauƙarwa Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare mafi girman littafinShi, Alkur'ani wanda mummunan abu baya zuwa mishi ta gabanshi ko daga bayanshi
Allah Ya aiko Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a matsayin cikamakin Annabi, saboda haka babu wani annabin da zai zo a bayanshi, Allah Maɗaukaki Yace: {Saidai shi Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa} [Al-Ahzab: 40].
1- Haihuwar Shi (S. A. W)
An haife shi a Makkah shekarar Giwa (571 A.D) Marayan mahaifi, kuma ya rasa mahaifiyarsa da wuri sai ya rayu a cikin kulawar kakanshi Abdulmuɗɗalib, sa'annan a bayanshi ya rayu a ƙarƙashin kulawar baffanshi Abu Ɗalib wanda ya kula da shi ya kuma kare shi.
Ya rayu a cikin ƙabilan Ƙuraishawa na tsawon shekara Arba'in gabanin Annabta (571 - 611 A.D), Ya kasance a cikin waɗannan shekarun mai kyawawan halaye ne abun buga misali wajen daidaituwa da tantancewa, kuma ya shahara a cikinsu da laƙabin mai gaskiya da amana, ya kasance yana kiwo daga baya kuma sai yayi kasuwanci. Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance gabanin musulunci yana kan tafarki madaidaici, yana bautawa Allah a bisa tafarkin Annabi Ibrahim kuma yana ƙyamatan bautawa gumaka da kuma dukkanin ayyukan bautan gunkin.
Bayan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya cika shekaru arba'in na daga rayuwarshi, kuma a yayin da ya kasance yana ta'ammuli kuma yana bauta a kogon hira wanda yake jabalun Nur, sai wahayi daga Allah yazo mi shi, Alkur'ani ya fara sauƙa, kuma ya kasance farkon abunda ya sauƙa a gare shi na daga Alkur'ani mai girma shi ne faɗin Allah Ta'ala: (Kayi karatu da sunan ubangijinka wanda Yayi halitta} [Al-Alak: 1]; domin sanar da cewa wannan aiken tun daga farkonshi wani zamani ne na daban wanda zai cika da ilimi da karatu da haske da kuma shiriya ga mutane, sa'annan sai Alkur'ani yaci gaba da sauƙa a gare shi har na tsawon shekara ashirin da uku.
4- Farkon Da'awarshi (S. A. W)
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare yayi ƙira zuwa ga addinin Allah na tsawon shekaru uku a ɓoye, sa'annan sai ya bayyana da'awar yayi ƙira a bayyane na tsawon wasu shekaru goma, Manzon Allah da sahabbanshi sun fiskanci mafi tsananin tozarci ta zalumci daga ƙabilarshi ƙuraishawa a cikin waɗannan shekarun, sai ya fara bijirar da musulunci ga ƙabilun da suke zuwa aikin hajji, sai mutanen Madinah suka karɓi musuluncin, sai musulmai suka fara ƙaura zuwa gareta kaɗan-kaɗan.
5- Hijirarshi (S. A. W)
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi hijirah zuwa Madinah Al-Munawwarah wacce ake ƙiranta Yasriba a wancan lokacin a shekara ta (622A.D), kuma a lokacin ya kasance yana shekara ta hamsin da uku na daga rayuwarshi, bayan shuwagabannin ƙuraishawa sunyi mishi taron dangi akan tsayuwa a hanyar da'awarshi da kuma kashe shi; sai ya rayu a cikinta na shekaru goma yana mai ƙira zuwa ga addinin musulunci, kuma yayi umarni da sallah, da zakkah da kuma sauran ayyukan shari'ar musulunci.
Manzon Allah (S. A. W) ya kafa ginshiƙan daular musulunci a cikin Madinah Al-Munawwarah bayan hijirah (622A.D) kuma ya samar da tushen zamantakewar musulunci, sai ya jefar da ƙabilanci irin na jahiliyya, kuma ya yaɗa ilimi, ya tabbatar da adalci da daidaito, da ƴan uwantaka, da taimakekkeniya akan biyayya ga Allah da tsoronShi. wasu ƙabilu sunyi yunƙurin turmushe musulunci, sai wasu yaƙoƙa da dama suka faru, sai Allah kuma ya baiwa addininShi da addinin Manzonshi nasara, sa'annan sai aka dinga shiga musulunci, sai Makkah ta shiga musulunci tare da mafi yawan garuruwa da ƙabilu na cikin yankin larabawa suna masu yarda da kuma zaɓan wannan addini mai girma.
A cikin watan Safar shekara ta 11 bayan hijirar Annabi kuma bayan Manzon Allah ya kammala isar da saƙo, kuma ya cika amana, kuma Allah ya gama cika ni'ima a bisa mutane da cika addini, sai zazzaɓi ya kama Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai rashin lafiya yayi tsanani akanshi har zuwa lokacin da ya rasu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin yinin ranar litinin, sha biyu daga watan rabi'ul Auwal a shekara ta 11 bayan hijirah wanda ya dace da (6/8/632) Miladiyyah. A lokacin kuma ya cika shekara sittin da uku, kuma aka binne shi a ɗakin Aisha Allah Ya kara mata yarda a gefen masallacin Annabi.