Ɓangaren yanzu model
Darasi Ladduban tsarki da na biyan buƙata
Ladduban biyan buƙata
Wajibi ne akan musulmi da ya ɓoye tsaraicinsa daga ganin mutane yayin da yake biyan buƙatarshi.
Kuma haramun ne a gare shi biyan buƙatarshi a wurin da zai cutar da mutane
Ya haramta a gare shi da ya biya buƙatarshi a cikin wani rami a yayin da yake cikin daji, domin akwai yiwuwa ya kasance akwai dabbar da zai iya cutar da ita ko ta cutar da shi a cikin wannan ramin
Ya wajaba a gare shi da ya kiyaye kada najasa ya shafi tufafinshi ko jikinshi, kuma idan har wani najasa ya taɓa shi toh ya wajaba a gare shi da ya wanke shi.
kuma idan ya gama biyan buƙatarshi, toh ɗaya daga cikin ababe biyu ya wajaba a gare shi
Al-istinja'u: Shi ne mutum ya tsarkake wurin fitar fitsari da kuma kashi daga jikinshi da ruwa
Al-istijmaru: Shi ne mutum ya tsarkake wurin fitar fitsari da kuma kashi daga jikinshi da wasu yanki guda uku, ko duwatsu guda uku ko wani abu makamancinsu wanda zai iya tsarkake jiki ya kuma tsaftace shi daga najasa.
Hadasi (Kari)
Kari yana gushewa daga mutum ne idan yayi alwala ko yayi wanka da ruwa mai tsarki, kuma ruwa mai tsarki shi ne: Ruwan da Najasa bata cakuɗu da shi ba bare tayi tasiri a cikin launinshi, ko ɗanɗanonshi, ko warinshi
Kari ya kasu zuwa kashi biyu
Ƙaramin kari da kuma alwala daga gare shi
3. Cin naman raƙumi, kuma lalle an tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: shin za ayi alwala idan akaci namar raƙum? sai yace "Na'am" (Muslim: 360).
4- Gushewar hankali da bacci ko hauka ko suma ko maye.