Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Tarihin rayuwar Annabi Muhammadu (S. A. W) (1)

Sanin tarihin rayuwar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana daga cikin addini. Kuma a cikin wannan darasi zaka san da yawa daga cikin tarihin rayuwanshi (S. A. W) gabanin manzanci.

Sanin cikakken bayanin rayuwar Annabi tun daga haihuwarshi har zuwa kusa da aikoshi

Tarihin Rayuwar Annabi

Ya wajaba akan musulmi da yasan cikakken tarihin rayuwar Annabi (S. A. W) domin ya samu damar koyi da shi a cikin dukkanin lammuranshi na rayuwa, domin tarihin rayuwanshi ya kasance aiwatar da hukunce-hukuncen musulunci ne da kuma shari'o'inshi, Allah Maɗaukaki Yace: {Haƙiƙa a cikin rayuwar manzon Allah akwai kyakkyawan abun koyi a gare ku, ga wanda ya kasance yana tsammanin saduwa da Allah da kuma ranar lahira} [Al-Ahzab: 21].

1. Dangantakanshi (S. A. W)

Dangantakan Annabi (S. A. W) shi ne mafi alherin dangantaka da kuma mafificinta. Shi ne Muhammadu Ɗan Abdullahi Ɗan Abdulmutallib Ɗan Hashim Ɗan Abdu Manafi Ɗan Ƙusayyu Ɗan Kilabi Ɗan Murrata Ɗan Ka'abu Ɗan Lu'ayyu Dan Galib Dan Fihir Dan Malik Ɗan Nadar Ɗan Kinanah Ɗan Khuzaimah Ɗan Mudrikata Ɗan Ilyasu Ɗan Mudar Ɗan Nazari Ɗan Mu'iddi Ɗan Adnan, kuma Adnan Ɗan yaron Isma'il ne amincin Allah ya tabbata a gare shi.

2. Mahaifanshi (S. A. W)

Mahaifinshi shi ne: Abdullahi Ɗan Abdulmutallib Ɗan Hashim, ya rasu alhalin yana cikin mahaifiyarshi. Mahaifiyarsa kuma ita ce: Aminatu Yar' Wahab Ɗan Abdu Manafi Ɗan Zuhrata.

3. Haihuwarshi (S. A. W)

An haife shi ranar litinin a cikin watan Rabi'ul Auwal, shekarar Giwa, wacce ta dace da shekara ta 571 Miladiyya.

4. Shayar Da shi (S. A. W)

Suwaiba kuyangar Abu Lahab ta shayar da shi na wasu kwanaki, Sa'annan sai aka shayar da shi a ƙabilar Bani Sa'ad, sai Halimatus Sadiyya ta shayar da shi, kuma ya zauna a wurinta a cikin ƙabilar Bani Sa'ad na kimanin shekaru huɗu. kuma a can ne a ka tsaga zuciyarsa, aka cire rabon son zuciya da na Shaiɗan daga gare ta, bayan nan sai Halima ta komar da shi zuwa mahaifiyarshi.

5. Rayuwarshi Da Samartakanshi (S. A. W)

١
Bayan Annabi (S. A. W) ya dawo daga wurin ƙabilar Bani Sa'ad zuwa ga mahaifiyarshi Amina a garin Makkah, ya rayu a wurinta na wani lokaci, sa'annan sai mahaifiyar tashi ta rasu a Abwa'i yayin da take dawowa daga Madinah zuwa Makkah, a lokacin kuma ya kasance yana da shekaru shida, da hakan ne ya zamto cikakken maraya wanda ya rasa mahaifi da mahaifiya.
٢
Sai Kakanshi Abdulmutallib ya dawo dashi zuwa Makkah, yana rainon shi kuma yana kula da shi, a lokacin da ya kai shekara takwas da wata biyu da kwanaki goma (S. A. W), sai Kakanshi Abdulmutallib ya rasu a garin Makkah.
٣
Bayan rasuwar kakanshi, sai baffanshi abu Ɗalibi ya ɗauki nauyin rainon shi da kuma kula da shi, sai ya haɗa shi da yaranshi ya kuma fifita shi akansu, kuma ya keɓance shi da falalan girmamawa da karramawa, kuma bai gushe ba yana kula da shi har sai da ya haura shekara arba'in

Aikinshi (S. A. W) Gabanin Manzanci

١
A ƙuruciyarshi ya kasance yana kiwon dabbobi a garin Makkah na mutanenta a bisa lada.
٢
A shekara ta sha biyu na daga rayuwarshi, ya fita tare da baffanshi Abu Ɗalibi domin kasuwanci zuwa garin Sham, kuma a shekara ta ashirin da biyar na daga rayuwarshi sai Khadijatu Ƴar Khuwailid ta buƙace shi -kuma ta kasance Bakuraishiya ce ƴar kasuwa ma'abociya ɗaukaka da dukiya- da ya fita da dukiyarta zuwa Sham domin kasuwanci, kuma zata ba shi fiye da abin da ta kasance tana baiwa waninshi na daga attajirai, domin taji labarin gaskiyan zancen shi, da girman amanarshi, da kuma kyawawan halayenshi (S. A. W), sai Manzon Allah ya yarda da hakan, ya kuma fita da dukiyarta tare da yaronta Maisara

Rayuwarshi (S. A. W) Gabanin Manzanci

Rayuwar Manzon Allah (S.A.W) gabanin manzanci ta kasance rayuwa ce mai falala da ɗaukaka, ba a taɓa sanin shi da wani shirme ba, kuma bai taɓa aikata wani laifi a cikinta ba, haƙiƙa Manzon Allah (S. A. W) ya taso a cikin kulawar Allah Maɗaukaki, kuma Allah Ya kare shi daga dauɗar jahiliyya, har saida ya kasance yafi kowa mutunci a cikin mutanenshi, kuma ya fisu kyawawan halaye, kuma ya fisu asali, kuma ya fisu kyautata maƙobta, kuma ya fisu haƙuri, kuma ya fisu gaskiya, kuma ya fisu Amana, kuma ya fisu nisantar alfasha da halayen banza, har saida ya shahara a cikinsu da "Mai gaskiya mai amana" (S. A. W).

6. Matayen Annabi (S. A. W)

Ya auri khadijah Allah Ya kara mata yarda yana da shekaru ashirin da biyar, a yayin da ya fita zuwa Sham domin yi mata kasuwanci tare da yaronta Maisara, sai Maisara yaga abunda ya bashi mamaki na daga lamarinsa, da kuma kyawawan siffofin da yake da su na gaskiya da kuma amana, to a yayin da ya dawo sai ya baiwa khadijah labarin abunda ya gani, sai ta bijirar mishi kanta da ya aure ta, kuma ita ce farkon matar da Manzon Allah (S. A. W) ya aura a rayuwarshi, kuma bai auri wata mata akanta ba har ta rasu, kuma ita ce uwar dukkanin yaranshi, sai dai Ibrahim, kuma Khadijah Allah Ya kara mata yarda ta rasu ne gabanin hijirah da shekaru uku.

Sunayen Matan Annabi (S. A. W)

١
Khadijah Allah Ya kara mata yarda
٢
A yayin da Khadijah Allah Ya kara mata yarda ta rasu, sai ya auri Saudatu Ƴar Zam'atu Allah Ya kara mata yarda
٣
Sa'annan sai ya auri Aishatu Ƴar Abubakar As-Siddik Allah Ya kara mata yarda
٤
Sa'annan sai ya auri Hafsat Ƴar Umar Binul Khaddabi Allah Ya kara Musu yarda
٥
Sa'annan sai ya auri Zainab Ƴar Khuzaimah Ɗan Haris Allah Ya kara musu yarda
٦
Sa'annan sai ya auri Ummu Salamata kuma asalin sunanta shi ne Hindu Bintu Umayyah Allah Ya kara mata yarda
٧
Sai kuma ya auri Zainab Ƴar Jahash Allah Ya kara mata yarda
٨
Sa'annan kuma sai Manzon Allah ya auri Juwairiyya Ƴar Haris Allah Ya kara mata yarda
٩
Sa'annan kuma sai ya auri Ummu Habiba Allah Ya kara mata yarda, kuma asalin sunanta shi ne Ramlatu a wani faɗin kuma akace Hindu Ƴar Abi Sufyan
١٠
Bayan buɗe Khaibar kuma sai ya auri Safiyyah Ƴar Huyay Ɗan Akhdab Allah Ya kara mata yarda
١١
Sa'annan sai ya auri Maimunah Ƴar Haris Allah Ya kara mata yarda, kuma ita ce mata ta karshe wacce Manzon Allah (S. A. W) ya aura.

7. Yaran Annabi (S. A. W)

Ƴaƴan Annabi (S. A. W) a bisa zance mafi inganci guda bakwai ne: (Uku Maza, huɗu Mata).

Ƴaƴanshi Maza guda uku ne: Al-Kasim, da shi ne ake mishi alkunya, kuma ya rayu ne na wasu ƴan kwanaki, da Abdullahi, kuma ana mishi laƙabi da Aɗɗahir da Aɗɗayyib, sai kuma na ukun su Ibrahim.

Ƴaƴa matanshi guda huɗu ne: Zainab kuma ita ce babbar ƴarshi, da Ruƙayya, da Ummu Kulthum, da Fadimah. Saboda haka dukkanin yaran Annabi (S. A. W) Mazansu da Matansu uwar muminai Khadijah Allah Ya kara mata yarda ce ta haife su, sai dai Ibrahim domin shi mahaifiyarshi kuyangar Annabi ce mai suna Mariyatul Ƙibɗiyyah wacce Al-Muƙauƙis ya ba shi kyautarta.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa