Ɓangaren yanzu model
Darasi Su Waye Allah Yayiwa Rangwamen Shan Azumi?
Su waye Allah Ya yiwa rangwamen shan azumi?
Toh ya halatta a gare shi da ya sha azumin, sai ya biya kwanakin da ya sha bayan watan Ramadan idan har ya kasance cikin waɗanda ake tsammanin warakansu.
Saboda tsufa ko rashin lafiyan da ba a masa tsammanin warkewa, to ya halatta a gare shi da ya sha azumin sai ya ciyar da miskini guda a kowace rana, zai bashi abunda ya kai kimanin kilo da rabi na daga abincin mutanen garin.
Azumi ya haramta akansu, kuma baya inganta daga gare su, zasu biya wanda suka sha ne bayan watan Ramadan.
Idan mai ciki ko mai shayarwa ta jiwa kanta tsoro ko ta jiwa yaronta tsoro, to zata sha sai ta biya daga baya. Daga Anas Allah Ya kara mishi yarda lalle Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ka zauna na baka labari akan azumi, lalle Allah Mai girma da ɗaukaka Ya sauƙewa matafiyi wani ɓangare na sallah, kuma Ya sauƙewa matafiyi da mace mai ciki da mai shayarwa azumi» (Ibnu: Majah: 1667).
Yayin tafiyarshi da kuma yayin zamanshi na ɗan ƙaramin lokaci wanda bai wuce kwanaki huɗu ba, to ya halatta a gare shi da ya sha azumi sai ya biya waɗannan kwanakin bayan Ramadan.
Allah Ta'ala Yace: (Duk wanda ya kasance mara lafiya a cikinku ko akan tafiya to ya biya a wasu kwanaki na daban, Allah Yana nufin sauƙi ne a gare ku, kuma baya nufin wahala) (Albakara: 185).