Ɓangaren yanzu model
Darasi Tadabburin Alkur'ani mai girma da fassara shi
Fassara Alkur'ani Mai Girma Da Tadabburin Shi
Ya kamaci kowana musulmi da ya kwaɗaitu a bisa karanta Alkur'ani mai girma karatu mai kyau, da tadabburin shi da kuma tuntuntuni a cikin ma'anoninshi, da umarninshi, da haninshi, da koyon fassara shi tare da sanin hukunce-hukuncen shi, sa'annan aiki dashi, domin ya rabauta a duniya da lahira.
Ma'anar Tadabburi
Tadabburi: Shi ne tsayuwa akan ma'anonin ayoyi da tuntuntuni a cikinsu, da amsa musu; domin amfanuwa da su da kuma aikata su.
Kuma ya wajaba akan mai tadabburin Alkur'ani mai girma da yasan dunƙulallen ma'anar ayoyi, domin tadabburin shi da fahimtarshi su zamto masu inganci.
Matsayin tadabburin Alkur'ani mai girma
Ya wajaba akan kowana musulmi da yayi tadabburin wannan Alkur'ani mai girman, kuma ya nemi fahimtar ayoyinshi da ma'anoninshi, ya kuma rayu da shi. Allah Maɗaukaki Yace: {Wannan littafi ne mai albarkah wanda muka sauƙar dashi zuwa gareka, domin suyi tadabburin ayoyinshi kuma domin masu hankali su hankalta} [Sad: 29], kuma Allah Mai girma da ɗaukaka Yace: {Shin ba zasuyi tadabburin Alkur'ani bane, kodai akwai makullai a zukatansu ne} [Muhammad: 24].
Tafsiri: Shi ne bayanin ma'anonin Alkur'ani mai girma.
Mahimmancin tafsiri da kuma buƙatuwa zuwa gare shi
Ilimin tafsiri yana daga cikin ilimi masu yawan amfani kuma masu darajah; domin yanada alaƙa ne kai tsaye da littafin Allah Maɗaukaki, kuma yana taimakawa wajen fahimtar maganan Allah Mai girma da ɗaukaka; da kuma sanin muradanShi, kuma ta hanyar ilimin tafsiri ne ake sanin ma'anonin Alkur'ani mai girma wanda hakan zai taimaka wajen shiryar da musulmi ga aiki na gari, da kuma samun yardar Allah Maɗaukaki da rabauta da AljannarShi, kuma hakan zai samu ne da aikata ababen da yayi umarni da su a cikin littafin Shi mai girma, da nisantar haninshi, da kuma ɗaukan izina daga ƙissoshin shi, da gaskata labaranshi, kuma da ilimin tafsiri ne mutum zai bambance tsakanin gaskiya da ƙarya ya kuma gusar da kowace shubuha wajen isa zuwa ma'anar ayoyi da kuma haƙiƙanin ababen da suke nuni zuwa gare su.
Himmatuwan sahabbai a bisa sanin ma'anonin Alkur'ani mai girma da fassaranshi daga wurin Annabi (S. A. W)
Sahabbai masu darajah Allah Ya kara musu yarda sun kasance suna tambayar Annabi (S. A. W) akan duk wani abunda basu fahimce shi ba na daga cikin Alkur'ani, an karɓo daga Abdullahi Bin Mas'ud Allah Ya kara mishi yarda yace: A yayin da wannan ayar ta sauƙa: {Waɗanda sukayi imani kuma basu jirkita imaninsu da zalumci ba} [Al-An'am: 82] hakan yayi nauyi akan sahabban Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, sai sukace: Toh waye ne daga cikinmu bai zalumci kanshi ba?! sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: «Abun ba kaman yadda kuke zato bane, yadda zancen yake shi ne kamar yadda Luƙuman yacewa ɗanshi: {Ya kai ɗa na kada kayi shirka ga Allah, domin lalle shi shirka zalumci ne mai girman gaske} [Luƙuman: 13] [Bukhari: 6937, da Muslim: 124].
A Wajen fassara Alkur'ani mai girma da kuma sanin ma'anoninshi, ana komawa ne zuwa hanyoyi masu zuwa:
Na Farko: Fassaran Alkur'ani da Alkur'ani
Domin Allah Maɗaukaki Shi ne ya sauƙar da shi, kuma Shi Yafi kowa sanin manufofinShi.
Misalin faɗin Allah Ta'ala: {Ku saurara lalle waliyan Allah babu tsoro a gare su kuma basa baƙin ciki * Waɗanda sukayi imani kuma sukayi taƙawa} [Yunus: 62- 63] haƙiƙa a cikin wannan ayar Ya fassara waliyyan Allah da faɗinShi: (Waɗanda sukayi imani kuma sukayi taƙawa).
Na Biyu: Fassaran Alkur'ani Da Sunnah
Domin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi shi ne mai isarwa daga Allah Maɗaukaki, saboda haka yafi kowa sanin manufar Allah Ta'ala daga zantukanShi.
Daga cikin misalin irin wannan tafsirin, fassarar da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayiwa ƙarfi da jifa, an karɓo daga Ukubata Bin Ãmir Allah Ya kara mishi yarda yace: Naji Manzon Allah (S. A. W) alhalin yana kan Mimbari yana cewa: {Kuma kuyi musu tanadi na daga ƙarfi gwargwadon ikonku} [Al-Anfal: 60], ku saurara kuji, lalle abunda ake nufi da ƙarfi anan shi ne jifa, ku saurara kuji, lalle abunda ake nufi da ƙarfi anan shi ne jifa» [Muslim: 1917].
Na Uku: Fassaran Sahabbai Allah Ya kara musu yarda
Domin lalle su sunfi sanin hakan: saboda sunga wasu ababe da kuma yanayin da ake sauke Alkur'ani a cikinshi, kuma sun kasance masu cikakken fahimta mai inganci da kuma ayyuka na gari.
Daga cikin misalin haka: Faɗin Allah Ta'ala: {Kuma idan kuka kasance marasa lafiya ko kuna kan tafiya ko kuma ɗayanku yazo daga bahaya ko kuma kuka shafi mata} [Annisa: 43], haƙiƙa ya inganta daga Ibnu Abbas Allah Ya kara musu yarda: cewa lalle shi ya fassara shafan mata anan da jima'i"] Tafsirin Ɗabari: 8/389].
Na Huɗu: Fassaran Tabi'ai
Su ne waɗanda suka himmatu da ɗaukan tafsiri daga wurin sahabbai Allah Ya kara musu yarda, domin tabi'ai su ne mafi alherin mutane bayan sahabbai, kuma sunfi kuɓuta daga soye-soyen zuciya akan waɗanda suka zo a bayansu. Kuma a zamanin su yaren larabci bai kasance ya tagayyara sosai ba, sai suka kasance sunfi kusa da daidai wajen fahimtar Alku'ani akan waɗanda suka zo a bayansu.
Abunda yake wajibi akan musulmi yayin fassara Alkur'ani
Ya kamata akan musulmi idan wani abu ya shige masa duhu wajen fahimtar Alkur'ani da sanin ma'anoninshi da ya koma zuwa ga litattafan tafsiri, da zantukan ma'abota ilimi masu tafsiri waɗanda aka aminta dasu wajen sharhi da kuma bayanin ma'anan ayoyi tare da fassara su.
Tafsirin Alkur'ani mai girma ba na kowana musulmi bane; saidai shi na ma'abota ilimin tafsiri ne, saboda haka ya kamata marasa ilimi daga cikin musulmai su kame daga tafsiri ba tare da ilimi ba; saboda mai tafsiri yana yin fassara ne daga Allah Ta'ala, yana mai shaida a gare Shi da manufofin maganganun Shi, saboda haka ya kamata ya girmama wannan shahadar yana mai tsoron kada ya faɗi wani abu akan Allah ba tare da ilimi ba, sai ya faɗa cikin abunda Allah Ya haramta, daga nan kuma sai ya taɓe a ranan alkiyama, Allah Ta'ala yace: {Kace lalle ubangijina Ya haramta Alfasha, wanda ya bayyana daga gareta da kuma wanda yake a ɓoye, da aikin zunubi, da ta'addanci ba tare da haƙƙi ba, da kuyiwa Allah shirka da abunda bai saukar da hujjah akanshi ba, da kuma ku faɗi abunda baku sani ba akan Allah} [Al-A'araf: 33].
Litattafan da aka wallafa su na tafsirin Alkur'ani mai girma sunada yawa, amma kuma dukkaninsu matsayinsu bai zamto guda ba ta wajen samun karɓuwa, abunda ya zamto wajibi akan musulmi shi ne dogara akan ingantattun litattafan tafsiri waɗanda masu shi sun lizimci ƙa'idojin tafsiri. kuma daga cikin irin waɗannan tafsiran akwai masu zuwa: