Ka ci gaba da karatu

Bakayi rajistan shiga ba
Kayi rajista yanzu a cikin dandalin Taa domin ka fara karatu da kuma bibiyan ci gabanka tare da tara maki domin samun damar shiga gasa bayan yin rajistan

Ɓangaren yanzu model

Darasi Sunnonin fiɗira

Allah Mai girma da ɗaukaka Ya halicci mutum akan wasu siffofin kamala waɗanda zasu sanya shi ya zamto mafifici idan har yayi amfani dasu. A cikin wannan darasin zaka san sunnonin fiɗira da hukunce-hukuncen ta

  • Sanin sunnonin fiɗira. 
  • Sanin hukunce-hukuncen sunnonin fiɗira

Sunnonin fiɗira

Su ne kyawawan halayen da Allah Ya halicci mutum akan su waɗanda zasu mayar da mutum ya zamto cikakke idan ya aikata su, sai ya kasance a bisa mafi kyawun siffofi da mafificin yanayi, domin lalle shi musulmi yana lura da ɓangaren kyau da kamala ga musulmi, saboda ya kasance a bisa inganci na fili da na ɓoye.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Fiɗira guda biyar ne: Kaciya, aske gashin mara, rage gashin baki, yanke farce, tuge gashin hammata" (Bukhari, 5891, Muslim: 257). Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Ababe goma suna daga cikin fiɗira: Rage gashin baki, cika gemu, Asiwaki, sheƙa ruwa, yanke farce, wanke yatsun hannu tare da cuccuɗa su, tuge gashin hammata, da aske gashin mara da yin tsarki da ruwa" [Wanda ya rawaito hadisin yace] Na manta na goman sai dai ya kasance kuskuran baki (Muslim: 261).

Kaciya (Shayi)

Kaciya ga na miji shi ne cire fatan da ke rufe kan azzakari, kuma yawanci yana kasancewa ne a cikin ranakun farko na haihuwan yaro. Kuma yana daga cikin sunnonin fiɗira waɗanda suke wajibi a cikin haƙƙin na miji, kuma yana da fa'idodin kiwon lafiya da yawa.

Aske gashin mara

Shi ne kawar da gashin dake kan mara ta hanyar aske shi ko ta kowace hanya.

Rage gashin baki

Barin gashin baki yana daga cikin ababen da aka yarda dasu amma kuma ba mustahabbi bane, idan har musulmi ya barshi to ba aso ya tsawaita shi sosai, saidai anaso ne ya dinga rage shi tare da barin ɗan kaɗan daga gare shi.

Barin gemu da kuma cika shi

Musulunci ya kwaɗaitar a bisa barin gemu da kuma cika shi, gemu kuma shi ne gashin da yake fitowa akan bangaren fuska guda biyu da kuma haɓa. Kuma ma'anar cika shi shi ne barinshi da rashin aske shi domin koyi da sunnar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Asiwaki

Abun nufi da shi, shi ne amfani da wani ƙaramin itace wajen tsaftace haƙora, kuma yana daga cikin mustahabbai

Yanke farce

Ya kamata musulmi ya dinga yanke farcenshi domin kada su kasance matattaran dauɗa da ƙazanta

Tuge gashin hammata

Ya kamata musulmi ya dinga kawar da gashin hammata ta hanyan tuge shi ko da kowana irin abun kawarwa, domin gudun kada wari ya dinga fitowa daga gare shi.

Wanke fatan yatsu

Fatan yatsu ana nufin gaɓoɓi da kuma ramukan da suke kan yatsu, kuma wanke su mustahabbi ne.

Tsarki da ruwa, da kuskuran baki, da sheƙa ruwa:

Tsarki da ruwa shi ne Istinja'i, kuma haƙiƙa bayani ya gabata akan waɗannan ababe guda ukun a cikin darasin ladduban tsarki da na biyan buƙata, da kuma na alwala.

Haƙiƙa ka kammala wannan darasin cikin nasara


Ka fara jarrabawa