Ɓangaren yanzu model
Darasi Imani Da Samuwar Allah
Ma'anar Imani Da Allah Mai Girma Da Ɗaukaka
Shi ne gaskata samuwan Allah Ta'ala, da tabbatar da cewa Shi ne Ubangiji kuma Shi ne abun bauta, da kuma imani da sunayenShi da siffofinShi.
Sujjada tana daga cikin mafi girman alamun ƙasƙantar da kai ga Mahalicci Mai girma da ɗaukaka.
Tabbatar da samuwar Allah Ta'ala fiɗira ce a cikin mutum wanda baya buƙatan kafa hujjoji akanshi, saboda hakane da yawa daga cikin mutane suka yarda da samumar Allah duk da banbance banbancen addininsu da kuma mazhabobinsu.
Saboda muna ji daga can cikin zukatanmu cewa akwai Allah, muna komawa zuwa gare shi yayin tsanani da buƙatu, da fiɗirarmu wacce take mumina, da kuma yanayinmu na bauta wanda Allah Ya halicci kowana mutum akanshi, duk da cewa wasu mutane sunyi ƙoƙarin kauce mishi da kuma bijire mishi.
Sai gashi muna ji kuma muna gani yadda ake amsawa masu Addu'a, da yadda ake baiwa masu roƙo, da yadda ake biyawa waɗanda suke cikin ƙunci buƙatunsu. Waɗannan ababen su zasu nuna mana cewa lalle babu shakka akwai Allah Ta'ala.
Dalilan Samuwan Allah Ta'ala a bayyane suke, sunfi ƙarfin a ƙidaya su ko a ambato su, daga cikinsu akwai:
Yana daga cikin abunda kowana mutum ya sani cewa lalle fararren abu (Shi ne abunda aka samar da shi bayan bai kasance ba) saboda haka dole ne a samu wanda ya samar da shi, kuma dukkanin waɗannan halittun wanda muke kallonsu a kowana lokaci dole ace suna da mahalicci wanda ya samar dasu, kuma wannan shi ne Allah Mai girma da ɗaukaka, domin babu yadda za ayi a samu halittu ba tare da mahaliccin da ya halicce su ba, kamar yadda kuma babu yadda za ace su suka halicci kansu; domin babu wani abunda zai iya halittan kanshi. Kamar yadda Allah Yace: {Shin an halicce su ne ba tare da wani abu ba, kodai su ne mahalittan} [Aɗɗur: 35]. Ma'anar wannan ayar: Ba a halicce su ba tare da mahalicci ba kuma ba su ne suka halicci kansu ba, saboda haka dole ne kawai mahaliccinsu wanda shi ne Allah.
Lalle yadda aka tsara wannan duniyar da samanta da ƙasanta, da kogunanta da watanninta da taurarunta, da ababen dake kewaye da ita, da ƙoramanta da duwatsunta da bishiyoyinta, da dukkanin ababen da suke cikinta na daga halittu ƙirƙirarru, babu shakka hakan yana nuni a zahiri cewa wannan duniyar tana da mahalicci guda ɗaya, kuma wannan mahaliccin shi ne Allah Mai girma da ɗaukaka: (Ƙirƙirar Allah Wanda Ya kyautata kowana abu)[Al-Naml: 88].
Saboda haka waɗannan taurarin -misali- suna tafiya ne akan wani tabbataccen tsarin da baya lalacewa, kuma kowana tauraro yana tafiya ne a cikin wani tazaran da bazai wuce shi ba kuma ba zai ƙetare shi ba. Allah Ta'ala Yace: {Baya kamata ga rana da ta riski wata, kuma dare baya tserewa yini, kuma dukkaninsu a cikin sarari guda suke iyo) [Yasin: 40].