Ɓangaren yanzu model
Darasi Dukiyoyin da zakkah suka wajaba a cikinsu
Su waɗanne dukiyoyin ne zakkah ta wajaba a cikinsu?
Allah Ya wajabta zakkah a cikin wasu nau'i na dukiya waɗanda suke da yanayin ƙaruwa, kuma su ne:
Kuma Zakkah bata wajaba akansu har sai sun kai nisabin shari'a, kuma sun kai shekara cikakkiya, wato tsawon kwanaki 354.
Nisabin Zakkah a cikin zinari da azurfa shi ne kaman haka:
Idan musulmi ya kasance ya mallaki wannan adadin -ko fiye da haka- na daga zinari ko azurfa, sa'annan suka kai shekara a wajenshi, to babu shakka zai cire musu zakkan da ya kai kimanin 2.5% daga kimarsu.
Dukiya ta haɗa da takardun kuɗaɗe daban-daban koda ace suna hannunshi ne ko ya ajiye su a banki
Musulmi zai lissafa nisabin dukiyarshi da kuɗaɗenshi ne da abunda zai kasance dai-dai da kimansu na daga zinari, idan ya kasance yana da dukiyar da takai nisabin zinari, wato kaman kimanin giram 85, ko fiye da hakan a lokacin da zakkah ta wajaba, kuma wannan dukiyar ta zauna a wajenshi har na tsawon shekara guda, to zai cire 2.5% na daga kimarta.
Misali akan nisabin zakkan dukiya:
Abun nufi da hakan shi ne: Duk wasu ababen da aka tanade su don kasuwanci kaman filaye da gine-gine, da shaguna da gidaje, ko kuma ababen abincin da ake amfani dasu yau da kullum
Yadda ake fitar da zakkan ababen kasuwanci
Allah Maɗaukaki Yace: (Ya ku waɗanda sukayi imani ku fitar daga ababe kyawawan da kuka samu da kuma ababen da Muka fitar muku da su daga cikin ƙasa) (Albakara: 267).
Zakkah tana wajaba a cikin wasu nau'uka na musamman na daga amfanin gona, ba wai a cikin dukaninsu bane, kuma su ma dole ne sai sun kai wani nisabin da shari'a ta tanada.
Kuma ana bambanta tsakanin wanda aka shayar da shi da ruwan sama da wanda aka shayar da shi da ƙoramai da kuma wanda aka shayar dashi da wahala da biyan kuɗaɗe wajen nisabin da ya wajaba a fitarwa zakkah domin la'akari da yanayin mutane.
Sharruɗan wajabcin zakkan hatsi da ƴaƴan itatuwa
1. Sai abunda aka samu ya kai nisabi
2. Kuma abunda aka shukan sai ya kasance cikin nau'ukan da zakkah ta wajaba a kansu
3. Ya zamto an kammala girbe shi
Abun nufi da dukiyar dabbobi shi ne ababen da mutum yake amfani dasu na daga dabbobi, musamman ma: Raƙuma, Shanaye, tumakai.
Kuma hakika Allah Yayiwa bayinShi ni'ima da halittan wadannan dabbobin domin su ci daga namansu, kuma su sanya fatunsu, kuma su dinga ɗaukansu da kayakin nauyinsu yayin tafiya da balaguro, Allah Ta'ala Yace:(Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci * Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã * Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai)(Alnahl: 5 -7).