Ɓangaren yanzu model
Darasi Ma'anar Sallah da falalarta
Ababen da darasin ya ƙunsa
manufofi
Count Wani dalibiku kammala wannan darasin
Ma'anar Sallah
Sallah ita ce mafi girman ibadar gangan jiki da kuma mafi darajansu, kuma ita ibadah ce wacce ta ƙunshi zuciya da hankali da kuma harce, mahimmancin sallah yana bayyana a cikin ababe masu yawa, daga cikinsu:
2- Ita ce take bambanta tsakanin musulmai da kafurai, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Lalle abunda ke tsakanin mutum da shirka da kuma kafurci shi ne barin sallah" (Muslim: 82). Kuma yace: "Alƙawarin dake tsakanin mu da su shi ne sallah; kuma duk wanda ya barta haƙiƙa ya kafurta" (Attirmizi: 2621, Annasa'i: 463).
3. Allah Yayi umarni da a kiyaye ta a cikin dukkanin yanayi, a cikin tafiya da yayin da ake zaune, a cikin tashin hankali da kwanciyar hankali, a yanayin lafiya da rashin lafiya, kuma ana gudanar da ita ne gwargwadon iko, Allah Ta'ala Yace: (Ku kiyaye Salloli da kuma sallar tsakiya) (Albakara: 238), kuma Ya wasafta bayinShi muminai da faɗinShi:(Waɗanda suke kiyaye sallolinsu) (Muminun: 9).
Falalar Sallah
1- Tana kankare zunubi, kamar yadda Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: "Salloli lokuta biyar, da jumma'a zuwa jumma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, ana kankare zunuban da suke tsakaninsu idan aka nisanci manyan zunubai" (Muslim: 233, Attirmizi: 214).
2- Lalle ita haske ne mai haskakawa ga musulmi a cikin rayuwarshi baki ɗaya zatana karkatar da shi zuwa aikata alheri, ta kuma nisantar dashi daga sharri, Allah Ta'ala Yace: (Lalle Sallah tana hanawa daga alfasha da kuma abun ƙi) (Al-Ankabut: 45), Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace "Sallah haske ne" (Muslim: 223).
Lokacin Sallah shi ne lokaci mafi daɗi a wurin mumini domin a wannan lokacin ne yake ganawa da Ubangijin shi, sai ya samu kwanciyan hankali da natsuwa, da jin daɗin kasancewan shi tare da Allah Maɗaukakin Sarki.
Kuma ita ce mafificin abunda Annabi yake samun natsuwa da ita kaman yadda yace: "Kuma an sanya sanyin idanu na a cikin Sallah" (Annisa'i: 3940).
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana gayawa ladaninshi cewa: "Ya bilal ka tayar da Sallah, ka hutar damu da ita" (Abu Dawood: 4985).
Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan wani abu ya shigar da shi cikin baƙin ciki ko ya shagaltar da shi, sai yayi gaggawa zuwa Sallah (Abu Dawood: 1319).